← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 337

Sashe 83

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy ce ta shigo da fuska a dare muka fara gaida ita bayan ta amsa ta samu wuri ta zauna take fadawa umma duk yadda aka kwashe da Alh Nuhu da take kira da yaya Nuhu da mijin ta daddy da modibbo . Ba karamin mamakin faruwan hakan umma tayi ba don ban fada mata komai ba a ranan da muka dawo din. Tambayana umma tayi abinda ya kawo hakan sai ban boye komai ba na fada masu kamar yadda su fa,iza suka mayarwa mommy din da zancen. Ta dai fahinci ba laifina bane don ban mata wani abin bacin rai ba ra,ayin yin hakan daine tayi taso ta muzantani kuma abin bai tsaya a kaina ba sai ya koma mata. Amma duk da hakan sunyi min fada wanda nake mamakin meye laifina a cikin hakan da har akaga laifina kan wanan zancen. Tun wanan wajen nasha alwashi a raina cewa ba zan sake zuwa gidan su ba ko idan na ganta in gaida ita na kula wanan a cikin zuciyana ni kadai na barwa cikina hakan. A fannin daddy da Alh Nuhu kuma shi Alh Nuhu yasan ko waye daddy din don sun sha buga irin wanan wasa a tsakanin shi Nuhun nakaiwa daddy hari baiyi nasara ba. Don daddy tsohon jami,in tsarone yasan kansa son bai zauna kamar mace ba don yasan halinsu fulani da bakin rai ga riko kan dan abu kadan sai a salwantar da mutum ba komai bane a wurin su. Lokacin da yan uwa suka watse daga gidan kanin mahaifin su sai duk hankalin su ya tashi da kakaman da Alh Nuhu din yayiwa dan uwan nasu mai taimakon su don sanin halin Alh Nuhu din da kowa yayi. Domin bai fadin zance da wasa shi idan ya fada har cikin ranshi yake nufin hakan don hakane hankalin su bai kwanta ba musan man yan uwan haihuwan shi dcp din da shine jigo a cikin su a yanzu wurin shi suke dan samun hasafin rayuwa. Daddy dake zaune yana lazumi bayan idar da sallah asuba yaji wayan shi dake gefe ya dauki kara kirirrr kirirrr daddy bai motsa ba saida ya shafa addua ya kai hannu ya dauki wayan daya kara shigo da sabon wani kiran da sallama . Ba suna sai nomba tun kan ya dauka ya gane kiran nada wani manufa gareshi a lokacin. Hello ya sake fada bayan sallamannda yayi din a kamar kausashe don ya fahinci kowaye ke kiran nasa amma ya daure cikin muryan izza da isa yace wake magana bakin shi fam da addu,a . Bai dace na fadama sunana ba domin fadin sunana a gareka kamar na kaskantar da kainane gareka aka fada a dayan bangaren. Dan murmushi manya da kamar ya zamawa daddy dabi,an sa ya sake tare da fadin nasan dama kana kufule dani nima sin jiran ka nakeyi a ko wani lokaci. Au ashe kasan da hakan dama koda yake ni ba bakon ka bane ka sani don haka kar kaga kamar kaci bulus a wurina kaida danka ka saurareni nan da yan shekaru ka gani muddin danka yace zai wullakanta min ya wallahi sai inda karfina ya tsaya a kansu. Don a iya rayuwana bana son rainin wayau da wullakanci balle har kaida danka kunemi takani ta hanyar auren diyana ku nuna wai ku mazane a gareta. Aiko daddy yace dashi ashe kai kasan gaibu ke nan har kasan da cewa rayuwan namu zata kai nan da yan shekaru ke nan kuma. Yana fadan haka kawai ya kashe wayan don baida likacin wanan bakin jahilin da jahilci yayi mashi katutu a zuciyashi yake kuma rudin shi a duniya don baida arabi da boko. Yayi recording din komai ya nade a wayan shi ya kuma turawa danshi komai daya dauka din ya Abubakar yana gama saurare ya mike yana fadin lalai wanan mutumin dole su dauki mataki a kanshi ke nan. Ya kuma kira daddy din suka kara tatauna maganan har daddy na fadin shu,umine na gaske shiyasa na turo maka koda yaka fito muna ta hanyar baya. Duk da nasan ba zai iya min komai ba da yardan ubangiji duk da nasan cewa kafin duk ya aiwatar da wani abu mun gama tara komai da muke son samu game dashi insha Allahu sai mu rigashi yin komai yadda ya dace. Wanan sakon da mahaifin shi ya tura maine yasa ya kara kaimi wurin hada duk wasu bayanan da yake son tarawa akan surukin nasa. Yayin da syrukin nasa shi kuma a nasan bangaren yake kokarin bin hanyar da zaibi yaga ya halaka Alh Ali dcp har lahira karshe ya dan san tilon dansane zai gaji komai nasa sai yayan shi mata. Daga baya kuma ya dawo ya halaka kanawar shi hjy Addah gadon dan nasu yayi yawa a karshe sai ya juyo kan Abubakar din da yasan yarshi ce zataci gadon shi tunda uwarshi da ubanshi basu raye idan diyan mata ta kama a kawar dasu suma sai abatar dasu a huta da banza kamar yadda ya shafe Sambo da iyalin shi a doron kasa har abada. Wani shu,umin murmushi ya sake don yaga plain din shi ya tafi daidai ga yadda ya tsara komai a zuciyan shi shida kanshi yayiwa kanshi kirari da Nuhu maciji baka ramin kan kan ka saidai ka kashe ka shige. Sun dauka wahalan bokon da sukayi shine sunfimu ko mai daya bayan daya zanga bayan yan iska daga su har iyalan su don ba fin kowa sukayi ba da zamu zuba ido muna kallon su a cikin daula. Daddy bai koma ba mun dawo daga school muka samu mutanen gidan tsaye a waje in ka debe umman mu dake faman boyo a cikin daki wai yuka ya yanke hjy karima zasuje asibiti . Muma da dawowan mu ke nan muka tsaya muna mata sannu a wajen har suka tafi kafin mu shiga cikin gida muna masu tausaya mata. Wanan yasa yan abokan hurdan ta ke zuwa gaida ita dama wasu daga cikin yan uwa mijin da suka samu labarin hakan. Da dare bayan magariba fatima yar ta na tsakiya ta shigo dakin tana fadin wai maman su na kirana a cikin mamaki na dan kalli umman mu kafin tayi min alama da inje nabi yarinyar zuwa part din su. Tana zaune saman dogon kujera ta tallabe hannun don zugin da yakw mata ga bande an daure hannun dashi da gani dai ciwo taji ba kadan ba a hannun nata. Nan na kara yi mata sannu na kai kasa ina fadin gani ta kalleni tana fadin na shiga wurun yaran don Allah in gyara masu shimfida . Allah ya gani ban son wuce falon su iyakana in tsaya a falo in gaidasu in fita har in shiga ya kama min dole a part din su ke nan . Saida na danyi jim kafin in iya daga kafa zuwa dakin na gyara ko ina na dakin tsaba duk da darene na wanko har bayin yaran da bai samun gyara na fito. Na samu Amira tayi barci a falon zan dauketa zuwa cikine daddy ya shigo ya samemu . Gaida shi nayi ya amsa min a cikin fara,a yana fadin mutumiyan tayi barci ke nan ashe na danyi murmushi na tafi da yarinyar fatima tana bayana ta nuna min inda Amira din ke kwanciya. Kafin in fito ita yarinyar ta rigani fitowa falon wurin iyayyen dake zaune take fadin yau mami baki ga yadda anty ta gyara muna dakin mu ba yayi kyau sosai sai gani. Ban tsaya ba nayi mata Allah ya sauwaka da saida safe na fita zuwa dakin mu ina shiga kuma umma ta aikeni nakaiwa mommy abinci. Na samesu zaune suna kallo Fa,iza ke fadin aita dauka nayi barci ne nace hjy karima ce ta kirani wai na gyarawa yaranta dakin su. A cikin hausa naji mommy tace ita suraiyya bata iya gyaran daki har yanzu ko me da sai an kiraki Nabila tace bashi bama mommy su dafa mata sata a karshe aishine ba kyau. Wanan kan idan sun dafa mata sata ashe zasuji tsiya ranan hauwa ta fadi tana gyara zama ni kuwa murmushi kawai na sake don jin abinda suke fada. Washe gari kuma still ta kara nemana wai na gyaro mata part din gaba daya sai na kira suraiyya din muyi tare har fatima diyan ta. Mun fara da falo muka gama muka koma ciki ban yarda nabawa yaran fuskan raini ba muna gab da karasa dakintane dake da uban gyara don ni ganin dakin yasa na raina da wayau anty din ashe iya tsabatan ta a waje ne kawai dan muhalinta bai kalluwa sau biyu don kazanta. Muryoyin sune ya karade falon suna fadi ina mara lafiyan take ne ko tana gun Alh ne don matar bata da dama . Anty ta mike ta fito tana fadin kudai kuka sani da safen nan haka, suka ina mukaga zama ance hannu saura kiris ya guntule ta dago masu hannun ta zauna ta fara basu labarin abinda ya faru. Muna gamawa nikan nafito gaba dayan su suka sako min ido irin anga bakon fuska din nan a inda ba a zata ba don dagani sai yar wando dogo da riga irin na exacirses din a jikina na kaina kuma da hula sai sock dake kafana da muke yawon cikin gida dashi don sanyin ties din kasan. Tsab suka kalleni ban damu da kallon su ba a yanzu don na saba da hakan tun shigowan mu arewa haka zasu zubo min ido suna kallona kamar sunga wani halitta can na daban. We na don fisnish anty na fada kafin na juya ina cewa welcome ma u na good morning wooo na sakai zan fita naji anty tace dani. Ibeg sahiba go and help dem to cook break fasat for us before u go na amsa da ok ma nabada baya naji daya na fadin wanan fa ita kuma kuka samota haka. Dayan kuma tace ke badai abuwar yar aiki kuka daukaba haka wanan tsaleliyar haka kai haba wace yar aiki kika san zan dauka sirina waje aini sam ban yardada wata yar aiki ba can a yanzu. Itace dai wace nake fada maku din nan sunzo au don Allah ki bari dai ke kice
Chapter 83 · 0% Book details