Sashe 21
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Yanzu ya kike so ayi don ban fahinci inda zancen ki ya dosa ba ya dago yana fadi tare da kallon inda hjy karima take tsaye.
Eh akan zancen Abubakar daine nace kai masa magana idan zai bamu kyauta ya rika bayarwa ta hannun ka sai taja tayi shiru.
Ya dan dago ya kalleta yace uhumm ina jinki cigaba mana tace a, a shine dama nace zan ma magana don ka kafa wanan dokan .
Eh lalai karima tunda gani dattijon banza ko don kawai in farauta maki rai sai inyi bakin jini ga iyalina saboda ke kece ko ?
Wai karima ina tunanen ki yake zuwa kwanan nan ne ko dai wani abu na faruwa dakene ba a farga ba ta jefo mai wani irin kallo tare da fadin .
Watau na haukace ke nan ba a sani ba ake zaune tare dani hakan kalaman ka ke nufi yanzu Alh don kawai na fadi gaskiya shine laifi ?
Hakan nake nufi kin taba jin inda akaiwa uwa da danta shamki don kawai wani ko wata yaji dadi a rayuwan
Yau ko cewa Addah tayi ya daina baki kudin shi ga baki daya ai ban tambayan ta dalili don datane ita ta haifi abinta.
Balle ya bada sakon har abaki kike ganin kamar Addah ta rage ko bata son a baki din ko wani abu don haka zaki zo wurun dattijon banza ki izani in saba masu ko ?
Ai dama nasani nasan haka zaka fada Alh haka dinne ai har kin sani kuma kika fada min yanzu ?
Ta wani mikewa tana fasin ni in ma kyautan ya zama magana daga yau a bari don Allah ai ba rasa kudi nayi ba a hannu na.
Ina da aikina ko yanzu naga daman komawa sai in koma yace badai gidana ba keda aiki sai idan baki gidan nan.
Don Allah yaga halinki na boye da kika boye min da farko ya kareni daga fita aikin ki tun farko kyautan kuma abarshi zan fadawa modibbo din.
A daina sai me zaka wani lauyeni kace nace matar kana ragewa ko wani abu can don hadin fada ta fita daga dakin.
Tafita tana dan kunkumi don dabaranta ba soici ba gashi kuma zata kulawa kanta tsiya a gidan kan hakan.
Dama shawaran kawace data bata tace ta gwada duk ranan da maigida ya kwana da ita har ya nuna jin dadin shi gareta to ita kuma ta gwada sa,anta a wurin miji ga abinda take bukata .
Acewar kawar a take miji ke biyawa mutum bukatan shi a wanan lokacin don kawai jin dadin kasamcewan su a tare da suka raya dare suna sunna.
Shine tayi kokarin gwadawa gashi kuma ita batayi sa, a ba abin yana neman kwabewa da ita ga baki daya a yanzu.
Dakin ta nufa kai tsaye wurin wayan ta taje ta kira kawar ta nan take labarta mata komai daya faru tsakanin ta da Alh.
Wani irin tsukin takaici taja tana fadin Allah karima ke banza ce waya fada maki da safen nan ya dace kiyi wanan maganan dashi ?
Ai tun jiyan ya kamata a daidai lokacin da abin bai gama fita masa kai ba ke kuma saiki sako zancenki ki gani.
Sallaman da taji daga kofa yasa ta katse wayan tana amsawa tare da fadin waye hjy nice Talatu dama wai nazo na fada maki Alh karami zai tafi.
To sai akace me to hjy babba ce dai tace nazo na sanar maki Allah kai lafiya mana ko ta fada adan hasale.
Talatun ta amsa mata da amin ta juya ta tafi yana zaune kannen shi sun dan mane suna rokon shi kudin anko yana ja masu hankali da hakan talatu ta dawo.
Yanayin fuskanta kawai hjy Adda ta kalla tasan da akwai bacin rai a lokacin saidai bata nuna hakan ba don cewa da tayi Allah saukeka lafiya zata shiga wankane yana jin hakan ya mike tare da fadin .
To mommy ni zan tafi ke nan sai kuma Allah ya sake hadamu da alherin sa uwar ta mike da sauri a cikin yanayin rashin jin dadi da tafiyan da dan nata zaiyi a lokaci.
Modibbo Allah ya tsare ya kare muna ku a duk inda kuka shiga ya dawo muna da kowa lafiya shi da kannen sa suka amsa da Amin.
Sai lokacin ya kalli kannen sa yana fadin to ni zan tafi ko sukace aaaa yaya gaskiya ka ganmu kafin ka tafi.
Wani gani kuma zan maku bayan wanan gaskiya mudai ka ganmu yana dariya ya saka hannu ya ciro kudi masu yawa mika masu suka hau murna da Allah ya tsare Allah ya kiyayye a cikin murna .
Nabila ya kalla yace nasan su Amira ba barci yanzu basu tashi ba idan sun tashi sai ku basu wanan suma su sayi alawa suka ari bakin yaran suna mashi godiya.
Haka ya karasa inda daddy ke tsaye yana magana dasu malam mudi ya dan kai rusunne yana fadin daddy zan tafi ke nan .
Dafa kafadan shi mahaifin nasa yayi ya mikar dashi yana fadin ka gama da yan rikicin can ke nan yace wallahi daddy .
Na dai sallamesu ai mun rabu lafiya yanzu yau su Amira basu fito ba ke nan eh daddy naba Amira nasu ta basu idan sun tashi.
Dan murmushi mahaifin ya sake kafin yace ka kyauta dan ko yanzu nasan akwai rikici idan sun tashi sukaji ka tafi ai .
Cikin dabara ya fara tafiya da dan nasa don su bar wurin dasu malam mudi suke tsaye ma,ana zaiyi maganan siri dashi ke nan.
Ganin hakan suma suka ja suka dan tsaya daga nisa dasu kadan sai da suka danyi kamar tako biyar suka tsaya har lokacin hjy da yaran ta na tsaye daga kofa suna kallon su.
Don jira suke suga tashin shi su koma cikin gidan haka ka,idan rakiyan su yake idan maigidan na gida iya kofa suke tsayawa.
Yanzun lagos din kuma zaka koma ya dan murmusa kadan yana fadin can zamu koma daddy don yau akai min waya sun gano mai wanan sunan.
Allah ya bada sa, a ya amsa da amin ya kara fadin ka kula da kanka don Allah irin wanan aikin nasan hatsatin dake cikin sa sai anbi a hankali.
Daga yayi mai fatan nasara ya juya ya dagawa mahaifiyar shi hannu tare kannen shi ya nufi motar da za a kaishi airport dashi.