← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 337

Sashe 144

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana zaune a falo tana jiran isowan shi koda taji tsayawan mota da hamzari ta mike ta kwashi yaran zuwa waje don su tareshi. Sai ganin su yayi a gaban shi girshi ba kunya wai tana mashi sannu da zuwa a cikin daure fuskan shi gareta ya fito daga motan ta kara gaidashi ya amsa a daure ya wuce har yaran ba tare daya taba su ba zuwa falon shi. Kamshine ya tare shi a falon zai shige yaji babban yar mai sunan mommy tana kiran shi da daddy yaja ya tsaya ya juyo yana kallon yarinyar tare da rage tsawon shi gareta yadda ya saba masu a can idan ya dawo. Ya sunbanci yarinyar a goshi tare da tambayanta yaya take tana masa gwalanci duk da ta fara mantawa dashi don watan su hudu ke nan basu tare dashi. Daga bayan shi inda Nazifa take tsaye ne yaji muryan ta tana fadin watau mu ba za ai muna wellcome ba da dawowa ba sai ita mai sunan hjy ku ko ? Bai mata magana ba sai mikewa da yayi yana karban yarshi a hannunta ya daukesu duka biyu zywa dakin shi driver daya daukoshi ya shigo mai da kayan shi ciki a lokacin Nazifa ta dauka zuwa dakin shi abinda bata saba yi ba ke nan a baya. Saida ya huta tare da yaran a dakin shi ya fito zuwa falon don kiranshi da Nazifa ta matsa dayi na ya fito yaci abincin da yasha gamin bokaye da malamai da mamanta tayi ta karbo mata shi don kawai a samun kanshi a dinga juya shi yadda ake so saboda kafiyan shi da taurin kai da yake dashi kuma yake nuna masu shidin shine fa. Saidai sun makaro don nacin ta yasa ya ankara da hakan don haka koda yana zaune sai waya yakeyi harda na iska tana zaune a cikin damuwan rashin cin abincin shi duk ta kagu taga yakai cokali a bakin shi. Can dai da taga ya gama wayan ta kirkiro murmushin kissa tana fadin wai ko fushi kake damune na abinda ya ffaru kaki cin abincin nan ? Ya kallota a lalace yana fadin fushi fushi akan me mekikai min da zanyi fushi aiku zance kuna fushi keda kuka koma gida ba tare da nasan laifin da nayi maku ba bayan mun rabu lafiya dake. Tace kayi hakkuri don Allah nagane kuskurena nayin hakan don ban dauka Abba zai canza abinda wani manufa ba haka. Ban san wani irin kiyayya ke tsakanin gidan ku da Abban mu ba har yake ikirarin shafan diyan da muka haifa dakai suma abin ya shafesu don sam Abba ya gwada min baya kaunan jinin ku ko kadan wallahi. Duk da mama ta dan fada min cewa matsala aka samu na rabon dukiyan wani dan uwansu maikudi da yarasu tun muna kanana wai kowa nason wani abu ya kasa barwa dan uwa a tsakanin su shine wai mafarin wanan fadan nasu har yanzu. A yadda naji mamana cewa har zargin duk suna da hannu a cikin mutuwan dan uwan nasu a lokacin da yake daddy na sama aka rufe zancen wai har yanzu kuma ba, a san inda iyalin dan uwan nasu suke ba gashi su sun raba dukiyan nasa a tsakanin su suda su baffah gyade da sauran su. Gaskiya abinda su Abba keyi baida kyau saidai kuma ai dukiyan dan uwan sune shine kawai amma aibai kamata ace har ya zama matsala a tsakanin su ba haka. Tayi shiru tana dago kai ta kalloshi don dama tana duke tana sharewa yarta dake shan nono bakine saita dago kai jin yayi shiru yana sauraren ta. Irin kallon da yake mata a lokacin shiyasa tasha jinin jikin ta ta fara zargin irin baran baraman da tayi ko katobara a gaban shi duk a wautanta nason su shirya dashi ya sake jiki da ita saboda kewan shi da sharenta da taga yanayi. Amma cikin labarin abu biyu yafi tsaya mai a rai na farko shine cewan da tayi mahaifin shi na cikin harkalan da akayi na kashe namu mahaifin. Sai kuma cewan da tayi mahaifinta har diyan da suka haifa baya kaunan su yana iya sabauta su don irin kiyayyen da yake nuna masu. Mikewa yayi a zabure saida gabanta ya fadi ganin yadda lokaci daya ya juye mata kamar wani zaki dashi yakai hannu ya karbi yar dake hannun ta ta rike tana kallon yanayin shi. Ina zaka da ita ya mika hannu ya fisgeta da karfin tsiya yana fadin bani yata in kaisu inda za a kulamin dasu don bazan barsu inda zasu tashi da rashin imani ba. Ganin da gaske yakeyi yana shirin fita mata da yaran yasa ta yunkura ta rigashi isa kofa ta kulle ta saka makulin a cikin jikin ta. Hakkuri ta fara bashi yana kokatin gyara yaran baida niyar bata su dabara ya fado mata ta dauki waya a cikin kuka ta kira mommy a cikin kuka take fada mata komai mommy din tace bashi wayan ta mika mai yaki karba tasaka handsfree tana fadin koma meye na fada ma kajirani gani nan zuwa yanzu gidan. Koda mommy ta iso ta samesu a cikin tashin hankali sosai don Nazifa tasha kuka har ta godewa Allah a lokacin don tashin hankali data gani a fili lokacin. Da umurnu ta fara bashi ya mika mata yar data fara kuka sosai a lokacin baiso ba ya mika mata yar ta zauna tana fadin meya kawo haka yau yau da dawowan ka ? Ina na fadama cewa komai ya wuce kada inji wani magana wani irin huci yayi da baki kafin yakai zaune yafara fadawa mahaifiyar nasa abinda ya faru tiryan tiryan. Hjy sai kada kai takeyi tana fadin Nazifa mai ya kaiki wanan katobaran haka a gaban mijin ki baki tunanen in mahaifin ki yaji wanan zancen dake da uwarki duk kun shiga cikin matsala ke nan. Nan dai mommy ta samu ta kwatar da fitinan har ya sauko kan dan bakin data bashi yace yaji amma yaran sa ba zasu taba zuwa wanan gidan ba a yanzu. Hakana ya kwana ranan yana faman tunanen wanan zancen biyu a zuciyar shi abunda ya hanashi barci ke nan a ranan. Saida na isa gida na duba abinda ya ban tunda na saka a jakka kafin in fito ban dauko na dubaba saidana gama cin abinci na dauko jakkana ina dubawa. Ba karamin kaduwa nayi ba lokacin da naga yawan kudin da yai signing a karbo gashi har ga Allah yace na zari kusan rabi muyi amfani dashi a gidan mu muma din ai marayune. Umma na kira ina fada mata abinda ya faru tayi shiru tare da mamaki cikin rike habanta can tace dani duk da hakan ki masa sadaka yadda ya kamata sai ki kwantata ki rage saura din Allah ya jikan musulmai ya gafarta masu. Na amsa da Amin zuwa la,asar na samu Abdulhamid a office na fada mai duk halin da ake ciki game da yadda mukayi da ogan mu din dashi muka fito tun a ranan muka fara bin masalataiya muna ganin limamai muna basu sadaka da abubuwan amfani a masalcin. Washe gari muka dora a inda muka tsaya don muyi yadda ya dace gaskiya mungama da masalataiya muka koma ba mabukata musulmai abinci sosai har labari yakai kunnen ogan namu. Ranan dayace din ranan mahaifiyan shi ta shigo suna falo sai ga wasu mata sunzo gaida ita da zuwa nan suke fada mata cewa sunga an saka hoton mijin nata babba ana mashi addua taji dadin hakan sosai kallon dan nata tayi don tasan aikin shine bana kowa ba. Murmushi ya sake mata taka tsantsan yakeyi da mahaifiyar nasa sosai da kanwarshi da sukazo don bai yarda wani mai aiki dan lagos ya dafa masu wani abinci ba da abinsu sukazo daga can don tsaro. Ranan da za ai taron bamu zauna ba tun safe muke faman shiye shirye da zirga zirgan komai ya kammala daidai yadda aka saba yi.
Chapter 144 · 0% Book details