← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 296 OF 337

Sashe 296

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwance nake tun dawowan mu bawani karfi a jikina abubuwa da dama suka hadu suka sauke min rashin kuzari lokaci guda haka. Saukin abin dai shine saukan dare mukayi washegari kuma da safe su baffah suka dauki hanyar kaduna basu kwana ba sai muka koma mu kadai a gidan kuma. Idan badon tafiyan mu da Abdul bane ba wanda zaisan mun je har kuma mun dawo din yanzu saidai ganin shi da mutane sukayi yasa yan wa yanda muke hurda dasu suka san da zancen dawowan mu kasan. Daga ciki ko har da abokan aikin mu na ma,aikatan mu dama wasu makwabtan gidan mu har suke muna sanu dazuwa a lokaci. Tun bayan dawowan mu kasan wayana yana kashe ban kunna ba son banda aiki sai faman barcin gajiya da nakeyi lokacin. Da farko na dauka ai wanan matsalan nawane dana dade banyi ba saida wata makwaciyar mu ta shigone take fadin ai haka akeyi don sai lokacim da mutum ya dawo gidane yake sauke gajiyan daya kwaso a can dama. Ta wagan ma,aikatan mune sukazo don gaida mu da zuwa wanda a gaskiya badon ni suka zo ba sai don Abdul da yake ma,aikacin su a yanzu shi. Amma saboda mutunci sai wasu suka zamo suka shigo namu part din daga ciki kuwa harda Adanan da Felix sune suka shigo part din mu don mu gaisa. Umma ta shiga ta tayar dani jin sune yasa na fito daga dakin saye da wani fashion hijab dashi da babu dayane don kamar riga yake ya matseni ko ina amma a hakan wai mace ta rufe jikinta ke nan dashi a yadda sukayishi. Tunda na fito Felix ya fara min ba,a da Amarya so na your eyes be dis ? See how you look fresh you, na de enjoy wooo ? Daidai ina zama nake fadin who be amarya ? i beg de go joo, carry dis your amebo talk and go. Gaskiya kin kara wani fresh dake fa wai da gaskiyane zancen auren ki gashi kin jefa min ogana cikin tashin hankalin tun da yaji cewa wai kinyi aure bai kara daga wayan kowan mu ba kuma a nan. Na, so you hausa people de do your marrige no any cerlarbration or gathering ? Why you too de talk about that da nayi aure zaka ganni gidan mu zaune a yanzu saboda wanan matsalan muharamin na kasan saudiyane fa na fada masu hakan don kawai ya bar zancen. Ya dan bata rai tare da fadin haka mukaji ku musulmai kuna da ka,idoji masu yawa dama don a kawar da zancen nake tambayan su yaya office din su suke fadin office yana nan saidai yan canje canjen da aka samu a yanzu kawai. Nan nakejin wai yanzu Adnan da Abdul din gidan mune a matsayin aikina su biyu saidai abubuwa da dan dama sun faru bayan barikink wurin felix ke fadi har oga saida ya shigo kan matsalan barin mu da kikayi haka kuma da yan matsalolin da aka samu. Saidai yazo ya samu kunyi tafiya gaskiya baiji dadin hakan ba ashe ke matsala kuka samu da Alaja haka baki fada muna ba ? Alaja mace ce mai yawan son kanta sama ga kowa ko mu hakkuri muke da al,amarin ta har muka kai wanan lokacin a tare dasu felix din ke fadin hakan. Mikewa nayi zuwa daki ba tare dana bashi amsa ba na dauko masu tsaraban daya dace dasu irin na maza saidai da dan banbanci don na Adnan shida yake musulmi na dan banbanta masu. Har kofa na rakosu sai wanan lokacin na fito daga gidan tun bayan dawowan mu daga kasan dana shiga gida. Don hakan sai naji kawai gara na dan tsaya na sha iska a wajen kafin na juya zuwa ciki ban koma daki ba na tsaya na gyara gida don ganin yadda gidan ya dan hargitse min a idona. Bayan na gamane na shiga wanka na fito ina shafa mai wayana dana kunna da safe yana caji a power van. Na mika hannu na dauko wayan sai na samu miscall har hudu a wayan daga Faiza sai kuma shi mukhatar din da yai min kira uku ina falo banji ba yanzu kuma a kan meya kirani din na tambaya. Faiza na fara kira don jin kiran da tayi min din dukda nasan dan sabon kwana biyun da mukayi ne a zaman mu kasan saudiya ya motso mata. Aikuwa ina daukan wayan abinda nayi zato shidin ne haka kuma abinda nafi tsana shine ta fara fada min kalman amarya amarya!!! Idona na dan runtse a hankali tare da fadin Abi waireni ? Ko kin haukacene wai ? Sai naji ta kwashe da dariya tana fadin keko boyar Allah kinbi waya haka kin kashe ko samun ki ba ayi ? Ga maigidanki nason jin muryanki tare da sanin halinda jikin ki yake ciki ba a samun ki ba,a samun umma sai Abdul makwabcin ku shi kuma yace yazo garin su . Eh ya dawo jiya tare da mahaifiyarshi da bata da lafiya ayyah Allah ya bata lafiya ta fada na amsa da amin kafin tace ke gulma kecina tun jiya fa. Akan me fa na tambayeta saida taja kafin tace akan kishiyan ki fa Sahiba jiya sister ta kirani tana fada min cewa sunyi fitina sosai da mijin ki har yakaisu da batun saki saidai Allah ya gyara ba ai sakin ba . Don hakane ita kuma tace tunda a kanki komai da bai taba faruwa haka ba tsakanin su ya faru yanzu sabodake ba zaki taba tarewa a gidan shi ba da sunan aure. Faiza na katseta ina fadin ki daina irin wanan maganan ina ruwana da matalan shi da matarshi matsalan sune can tsakanin su bai shafeni ba. Ya shafeki sahiba waiko kinsan me ake nufi da kishiya mu sanma ma irin taki din nan da ta tsare ciki ta tsare waje a gidan mijin ku yanzu. Koma meye matsalan ta ni bai shafeni ba na bata amsa ta tareni da fadin keko ya shafa a yanzu sahiba don kece zaku zauna a karkashin innuwa daya da ita abinda bata taba zato ba a rayuwan ta . Sam bai fada mata zancen auren shi dake ba sahiba idan ya fadi abune daba zai yuyu ba akace dole kuma tasa hakan don hjyshi ta hana ya fada ma kowa a lokacin tunda itama iskancin matar ya isheta zuwa yanzu. Enough faiza enough please kin dameni da zancen wa yan nan mutanen kwata, kwata basu a raina balle zancen su ya dameni suje can suyi duk abinda zasuyi wanan ba matsalana bace hakan. All what i know shine idan har ta shiga gonata sam ba zataji dadin hakan ba final amma ni zancen su a yanzu ba matsalan daya shafeni da hakan understand ? Sahiba nasan da hakan amma kiyi tunane kema ki gane saboda wa take wanan haukan hakan a yanzu duk saboda kece fa ? don kawai kin auri mijinta, Shi nake son ki gane don Allah ki sa umma ta nema maki tsari a jikin ki please kafin tarewan ki tunda babu isasshen lokaci a yanzu. Katseta nayi da fadin Sahiba ni in nemi tsari bayan wanda Allah ya hore min a jikina ga kuma adduan dana sani a bakina ? Idan wanan kike jima faiza kada kiji komai a zuciyan ki ni ina tare da tsarin ubangijina komai ba zata taba yiwa yar uwarki a duniyan nan ki sani. Don zuwa yanzu na gama fahintar me faiza take ji ga hakan da taji a game dani gashi nikuma sam banji komai a zuciyata ba game da wanan labarin da take fada min din a cikin tashin hankali. Don da gani yadda take maganan hankalinta a tashe yake sosai da abinda taji amma ni sai banji wani abin tashin hankali ba a lokacin. Haka dai muka gama wayan da ita don sam bata fahinceni ba ita damuwanta shine muyi wani abu a cikin yarbawan mu da muke zaune dasu tunda ance suna da asiri muma kada wanan matar ta samu galaban illanta min rayuwana take nufi. Har muka gama wayan da ita na kashe ina mamakin maganganun faiza din sai nasawa nake a raina watau yanzu dai a kasan hausa idan zakayi aure dakai da mahaifiyar ka ko yan uwa baku da shakat a zuciya saboda irin wanan dalilin musanman ma idan mai mata zaka aure sai irin zantukan nan ya biyo baya a karshe. Ni yanzu ba shine damuwa na ba a yanzu abindake zuciyana yakuma tsaya min shine makomar mahaifiyata da inda zan bar dan uwana shine abin damuwa a gareni yanzu. Don sam ba zan iya ketare kasa ba da sunan bin wani in bar mahaifiyata da bata cikin kosasshen lafiya hakama kanina Amar ince nabi wani namiji a yanzu. Wanan dalili yana cikin abinda ya hanani kula wani namiji a bangarena bansan na boye ba don sam nikan bana kallon namiji da sunan aure a rayuwata. Hakama yasa da oga sha,aban ya fito min da zancen naga ya zubemin a idona irin yadda na daukeshi kamar dan uwa a zuciyata. Idan kana son mu zauna lafiya dakai kada ka gwada min wani tsagan soyayya a fili don yanzu ne zamu bata dakai. Ban kaiga idda tunanena ba kiran mukhutar din ya shigo layina lokaci guda wayan ya dauki kara ina kallon wayan na kasa dauka don haushin da nake ji a raina. Saida ya kusa tsunkewa na daga ina sallama naji wani irin ajiyan zuciyan daya sake yana fadin Alhamdullahi Sahiba i hope lafiya kuke haka da ba a daga wayan ki bayan sallama ya fadi hakan da yaji na amsa mai. Lafiya muke bana kusa da wayane ina falo ina aiki nabar wayan a falo na basa amsa da hakan ya kara sauke dan guntun ajiyan zuciya kafin yace. Aiki kuma ke da kanki da baki da lafiya a jikin ki aiki yanzu ba naki bane hutu ya kamata dake a yanzu kiyi barci ki huta gajiyan dawafi da zaman jirgi jinin jikinki ya dawo fresh a yanzu. Idan na kwanta sai umma tayi aikin ke nan da kanta da sauri naji yace no no no ba haka nake nufi ba amaryata ai yanzu nafi son hutun mama sama
Chapter 296 · 0% Book details