Sashe 276
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
da wuyan shi tau zaka iya tafiya don na zata fushi kayi dama zaka fita. Ya mike tare da kallon su yana fadin to ni zan tafi Allah ya bamu alheri sai yadda aka shirya din inji yasa kai ya fita suka bishi da kallo lokaci guda. Kafin tsohon ya kada kai yana fadin kai hamza watau dai wanan halin nasa sai abinda ya karu dashi yanzu kuma . A toh ya kara karfi yanzu dakuma matsayi tsohon dan bokone fa haukan boko na dukan shine ai daddy da sai yanzu ya samu daman yin magana yace tsohon mahaukaci dai ko anje kotun da yace din meye zasu iya wai ? Mikewa modibbo da bai iya jin karasan zancen na mahaifin shi yayi yana fadin ni zan tafi tunda ba wani abu zakuyi ba a yanzu din. Baffah Abdullahi yace tsaya sai ka saukemu a gida dama da aikin da nakeyi a can nafito shima ya mike yabi bayan dan nasu modibbo. Nan aka barsu da sauran suna kulla yadda abin zai kasance don yasan basu danacewa ga duk yadda ya tsara masu don dole subi shi don yana da karfin fada a cikin su. Dukan kofan da akeyine ina kitchen ina hadawa Ammar abin karyawa kada ya fita bai karya ba zuwa school yasa nake fitowa tunda safe idan na idar da sallah saina dora abinda zan hada mashi din. Tsam na wanke hannuna na fito zuwa kofan ina fadin who is on the door kafin na bude din nake tambaya daga ciki don ban yarda na bude kofan haka kai tsaye ba. Yace shine sakone daga mukhatar usman ya aikoshi jin hakan yasa na bude kofan wani mutum na gani a waje gajerene baida haske sosai yana rike da wasu takardu a hannun shi. Good morning yace dani you're welcome nace ya kara maimaita abinda ya fada da farko cewa an aikoshi wurin mrs Sambo da danta da za ai masu passport na visa. Ko zai iya ganin ta ya fada yana dan leka bayana daga ciki ashe umma ce ta fito yake kallonta zanyi magana naji tace talloni da yarbacin nan ya juye harshe yana fada mata sakon da aka aikoshi tace aitace danta kuma Ammar yana cikin dakin. Umma wai baki ganewane yanzu fa duniya ya canza umma kada ki saurin yarda haka da mutane lokaci guda ina fadin hakan saina juya na koma kitchen inda nake aiki ban san ya suka kwashe dashi ba dai a nan don aikina na ba hinma na gama na koma dakina a lokacin Ammar yazo ya sallameni bayan ya gama shirin shi na bashi kudin breakfast din ya tafi. Barci ne ya fara fisgana lokacin da wayana ya dauki kara don dole na tashi ina mika hannu na dauko wayan ina dubawa wanan sabon layine kamar na share sai na dauka oga sha,aban ne a lokacin na kara a kunne na. Yan mata barka da warhakan ya fada kai tsaye a cikin hausa wayan dana kara a kunnena na dan daga ina kallon layin da aka kirani dashi kafin na mayar ina fadin who is on the line please ? It,s me mukhatar usman your new boss now ya kuke ya hjy na turo yarona ya kawo takardan da zasu cika kin hanna hjy cikawa. Idanuwana na dan runtse muryan shi na dukan dodon kunnena sautin yana kayar min da gaba numfashina yana wani irin sauka da sauri sauri a lokacin. Hello din da ya sake fada yasa na tattaro natsuwa nasaka a zuciyana lokaci guda ina fadin no ka barshi already na riga dana biya mata makka zata tafi this year don haka mun gode. Masha Allah ya fada a bangaren shi tare da fadin da alama kina son kwaso halin mahaifin ki wurin kyautatawa sosai naji dadin jin hakan a gareki Allah yasa a fi hakan. Ba zan kuma so na hanaki samun lada a wurin Allah ba a yanzu saidai don haka zaku je umarah kuje makka daga baya no ita kadai dai zata tafi don haka yanzu no need taje umurah a yanzu. No Saidai shi umurah ba zuwa makka bane ai don haka zamu tafi a yanzu muyiwa mahaifin ku addua kamar yadda na saba zuwa ina masa lokaci lokaci zanso wanan lokacin muje tare daku da mahaifiya da iyalina muyi addua a tare insha Allahu . I hope ban takura maku ga hakan ba in a kwai wasu da kuke son muje tare dasu zaku iya bamu list din su a cikin lokaci mata biyar maza biyar bayan ku saidai ki tabbatar da masu imanine da mutunci a cikin family din . Don haka zan barki ki huta sai naji daga gareki shawaran da kuka yanke din zuwa anjima. Wayan nabi da kallo ina mamaki da al,ajabi ni kadai a dakin yau ina Alaja mai son nisanta danta damu yau ga wani na rokon a zaba mashi mutane masu kirki da zasu kai ziyara kasa mai tsarki don yin addua. Ni yanzu me zancewa umma kan wanan maganan ta dauka sai yadda nace a yanzu ina kokarin juyata yadda nake so ko me ? Da haka na mike zuwa wurin ta shago don naji fitanta daga gidan kafin barci ya fara daukana nasan zancen nan ne ya hana tayi min sallama.