Sashe 233
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
wallahi banji komai ba sai ummace nake jiyewa yadda ta saka damuwa tunda muka tunkaro wajen duk da nace da ita ta dake don Allah. Assalamu Alaikum na fada tare da daga masu hannu kafin mu karasa inda manya suke zaune a lokacin muka zube kasa muka fara gaidasu wuri ya kara kaurewa da surutu lokaci daya. Umma dake gurfane a gaban su baffa Amadu suna gaisawa a cikin mutunci muka mike tsaye tsaye kerere a a tsakiyan wurin bayan umma ina bin kowa na wajen da kallo. Suma din kallon nawa sukeyi a cikin mamaki sai magana sukeyi kasa kasa akan mu kujerun roba farare aka bamu muma mu zauna muka dago umma muka zauna a tare lokaci guda kafin tsohon ya samu wurin ya natsu ya fara magana. Sannu ku da zuwa tsohon ya kara fada tare da sake murmushi a fuskanshi haka yan uwa ke zuwa suna gaisawa da ita muna zaune hankalina ya koma a wayana da nake turawa felix sako a lokacin. Kiran Adnan ya shigo na dauka bluetooth dina na gyara na fara magana ina masa bayanin da har ya kaini ga tashi tsaye na dan gusa daga can ina magana. Eh shegiya tasan abinda ta taka wanan da ganin tama kila a turai take zaune ko irin rikkakun yan daban nan na lagos take zaune dasu. Gungun wasu samarine ke fadin haka daga gefe daya daga cikin su har da diyan su Alh Nuhu dasu Alh gyade da sauran su. Bayan tsoho ya samu wurin yayi shiru da kyat ya kallemu yacewa Umma Mairo baki kyauta muna ba da kika shige cikin duniya haka shiru baki kara waiwayan gida ba tsawon lokaci haka har muna daukan ko kun mutune mairo ? Bayan nan kwanan nan kuma mukaji bayanan ku wurin bukin yar gidan Ali dcp sai kuma mukaji shiru sai kwanan nan muka sake jin wai yarki tayi karan yan uwan mahaifinta a kotu kan wasu dalilai. Umma tana shiru sai faman goge hawayen dake zubo mata a fuskanta da takeyi Ammar yana dan lalashin ta ta hanyan dan buga mata kafada yana mika mata abin gogewa. Tambaya tsohon ya kara jefowa umma dake kurum bata bashi amsa ba sai hawayen da take sakewa . Can na dago kai na dan kalleta ina magana a harshen yarbanci nake fadin ta tashi mu tafi zaifi da wanan hawayen da take sakewa haka. Baffa hamzane ya taso daga inda yake zaune yaje wurin tsohon sukai magana kus kus dashi na dan lokaci kafin ya dago yana fadin. Mun san a yanzu gaskiya ba zata iya magana ba duba da a nan duk an hadu kuma a duba yawan shekarun da aka dauka ba a tare dole yau din nan a fama mata mutuwar mijin ta gaskiya. Don haka a barta ta huta daga baya sai a zabi wasu da zasu zauna da ita su fahinci dalilin ta da tsoho ya tambauye ta don haka ayi hakkuri har su sauko. Wanan ai ba zai yuyu ba, ba inda zata tafi tunda har taso ta wullakanta muna mahaifan mu don wani bukatan ta can na banza datazo dashi . Wani kuma daga cikin su yace wani yasata barin gidan dama da,a yanzu dawowan nasu zai jefa zukatan mutane da dama cikin tashin hankali. Kawai tunda an hadu yau din kuma tazo tayi bayani kawai kowa yaji tayi magana shine abin ji don ba zamu yarda mahaifin mu ya halaka ba saboda su. But na mike ina kallon mai maganan na nunashi da yatsa na fara fadi a cikin harshen turanci kada kayi kokarin sukan mahaifiyan mu a nan. Don mahaifiyan mu ba sa,ar yin ka bane idan kana son jin wani abu ka bari sai ranan da kotu ta bukaci zuwan mu kaji. Lokaci daya suka fara tayar da hayani wurin ana tattaresu don kaucewa fita sai shar suke faman zubawa kamar zasu zo su duke mu. Tafawa nayi na sake mikewa tsaye don naji suna fadin yau ko mu ko su a wurin ba wani sanaya ko duban halaka a tsakani yasa na mike na fara tafawa a hankali ina zagayan su . Good, ku kawo inda nake son kuke au ashe ku har kuna da uban da kuke gani kuna jin dadi bayan mu naku uban ya mayar damu marayu ya kuma jefamu cikin duniya wullakance. Kowa wurin yayi shiru yana kallona don abindana fada din naci gaba da jefa masu kallon tsana ina tsaye kyam a tsakiyan dan filin taron Innalilllahi manyan ke fadi masu jin turanci daga cikin su, a harzuke baffa Hamza yace kunga ku bari abi abin nan yadda aka tsara shi yanzu kunji abinda ke shirin faruwa a nan kuma duk ku kuka ja. Tare guy din da yafisu zafin nama akeyi yana tun karoni nace ku barshi ya tabani daga yau ba zaiyi gigin kara taba wani ba da sunan zuciya. Muddin ka iso nan ida nake zaka kare rayuwan ka a daure gidan maza wallahi kowa yai maka tsaye a kasan nan kuwa . Wurin yayi tsit lokaci guda sai muryana da akeji in hada da turanci in hada masu da yarbanci na zamo masu yar daba ta asalin da suke jin labarin su a Getto. Unbagarborn kai idan kasan kuya har zaka iya budan baki da sunan fada yau ka kallemu bayan mahaifin ku shine yayiwa mahaifin mu yanka na rago a wuyan shi a gaban yan uwanshi bayan sun sakashi saka hannu a kan kaddarorin shi. Carb naji an rike min hannu ta baya nayi wani irin juyowa a kausashe ina shirin illanta maishi baffa hamza ne da ya Abubakar suka rike ni sai dai a lokacin har na fita hayacina ko lokaci guda. Don Ina sun makara ihun dana sake don bacin rai saida duk tsikan jikin wanda ke wurin kuma dan asalin jinin ahalinmu ya tashi kowa yace babu Aljani a duniya karyane. Ai kafin suyi haka nayi cikin taron nan na cakumo wuyan wanan dake maganan fitsaran babu wanda zaice ga yadda akayi na kai garshi a lokacin na shakoshi nayi wani irin girgizashi idanuwan shi suka firfito waje lokaci guda. Duk mazan dake wurin taron nan sunyi sunyi su bambareni daga jikin shi sun kasa da kyat umma da yaya Abubakar suka iso gareni a cikin tashin hankali. Shiya karbi wanan guy din a hannuna da kyar don kalama daya kawai daya fada a lokacin na sakeshi yanzu dai kun gani idan dabanci ko wani iskanci kuke ji tsohon ya fada rai bace. Wanan da kuke gani a gaban ku ko ubanku ya taba ta yanzu ina yake yana can cikin wahala kukuma gaku kuna son tayar muna da zaune tsaye. Daddy dake zaune yayi mutuwan wacin gadi ne ya nisa tare da mikewa zuwa inda nake sai kyarma nake ina jijiga a cikin wani irn tsuma yazo gabana yace. Sahiba ki kalleni nine daddy ki bar zancen nan har a natsu ayishi hankali kwance zaifi don mun san kinsan komai harda abinda mu bamu sani a yanzu. Kallon daddy din nayi cikin wani irin yanayi kafin na girgiza kai tare da kutawa ke da kingani kin san abin bana kai sake bane a lokacin. Ai kafin a samu yaya Abubakar su fitar dani wurin tuni wur ya rikece da surutu kowa na fadin albarkacin bakin shi kan abinda na fada a lokacin. Kamar wata gwauna suka rakani zuwa gidan gwaggo hari da umma tace can za a kaini don umma bata yarda a san inda muke ba ma,ana dasu kawai ta yarda yanzu ke nan. Ranan kan gwaggo ta sheda irin abin dake kaina sai dare sosai na samu kaina nayi barci sosai gashi koda wasa ba wanda ya sheda masu ai iskane sai suka dauka duk turjin yan iskane kawai da jigalanci irin na yam dabam lagos dana koyo. Saidai zancen cewa uban su yayiwa namu uban yanka irin na rago shi abinda ya dagawa kowa hanlali don haka yaran nasa suka shiga motan da suka ciko da sunan iskanci da turji a wurin suka koma cike da kunya da fargaban abinda sukaji din.