Sashe 308
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da haka sukaja hannuna zuwa cikin gidan wanda kamshi da sanyine suka bugi fuskokin mu lokaci guda su anty amarya sai masha Allah nake jin suna fada. Ke kan sahiba kin gama da duniya saidai ki nemi lahiran ki kuma kai wanan daulan duniya haka kamar kana kasan masar azziki ya nuna kamshi wurin nan gaskiya. Nasan da biyu take wanan maganan a lokacin sister ce ta iso da sauri tana waya tare da fadin ehh tagane take fadin ku shigo ga dakin amarya daga nan . Subahanallah Walhamdullilah Allahu Akbar shine abinda yarbawan ke kira kamar da waka a bakin su wasu na amsa masu cikin yan uwana da nasa da sukai muna rakiya dayan kanwarshi duk tana vedioting komai da akeyi lokacin. Nan dai suka kaini dakin daya bugawa soster waya cewa shine nawa dakin ya hadu komai na cikin gidan ga baki daya na wajene don haka tsayawa bayani bata lokacine gaskiya gida dai tubarkallah masha Allah. Daga nan suka fara fita kallon yanayin gida sai aka barni da su faiza da saura a dakin sai lokacin na bude idona ina bin ko ina nagidan da kallo,. Tirkashi yayi da uwargidana hjy Falmata ke can wancan gidan nasa suna ta buki da mutanen ta ana kisa yadda komai zai wakana idan mun iso . Sai kuma labari yazo masu a nazata cewa ai amarya ta tare a ko da sauri hjy Falmata dake waya lakacin da yaranta tace mene kike fada ta tambayi wace kebada labarin tarewan a lokacin. Tace ta tare a gidan ta mana tun karfe hudu da rabi suka kaita dakinta tana can gaba daya dakin yayi shiru na lokaci guda kowa da irin abinda yake tunane a zuciyar shi. Mikewa tayi daga zaune sai wanan yatta din hafsat tace ina zaki koma ki zauna yanzu idon kowa yana kanki aga yaya zakiyi. Zama tayi ba dan taso ba lokaci guda sukaci gaba da fadin shi kuma haka yaiwa mutane dama bai fadi inda amaryan nasa zata tare bane. Kubar wanan zancen yar nasu ta kara fada don a bar maganan a bainan jamma,a saidai falmata din ta kasa controling din kanta a lokacin don jin zancen take kamar a mafalki. A cikin hasala take tambaya wani gidan nasa ya kaita ke nan sai mai bada labarin take fadin naji ance kusa da gidan sarki nan dai unguwar nakune mana ba niss naji suna fada. Katseta yarta da take biwa ga haihuwa tayi da fadin waike a ina kika samu wanan labarin ne ina nan daine yake nan kuma za a kawota wancan dayan part din ko ? Ya canza shawarane dai wata daga cikin bakin kawayen ta ta fada ta bude baki da kyar tace ya canza ne kan don ko jiyan nan saida yan uwansa sukazo aka kara gyara part din ai. Gyara ko na sosai don har mun leka ai komai a kwai ciki eh wanan makircin suka shirya yasa suka hana ta tare jiya din ai. Wanan bashi zaisa na fasa komai a kanta ba tunda tayi gigin shiga harkan mijina zan nuna masu ni din nice don ba irin mu ake hawa a taka ba. Falmata bakya ji a irin wanan lokacin kike wanan zancen haka haba dai ta fada a dan cikin daure fuska tana mai jin zafi da kuna a kasan zuciyarta na wanan sabon zancen da yazo mata. Lamarin na mijinta a yanzu ya fara bata mamaki don yana abubuwa kamar ba mukhatar dinta data sani a baya ba. Don a zamanta dashi sam baya boye mata duk wani lamari nasa koda kuwa yasan zata iya yin wani abinda ba daidai ba duk da tasan bawai ta kyaleshi hakana bane don ko yaushe cikin kara kammala abinta take don gudun irin haka. Ba abinda ta tsana kamar kalman kishiya sam bata taba sarai cewa zai taba mata kishiya a rayuwan su ba duba ga yanzu yadda shekarun auren su yaja zuwa yanzu. Amma sai gashi da rana tsaka yan uwa sun tasashi gaba a cewan ta har yakai ga sunyi galaba a kansu sunsashi ya kara mata wata a gida da sunan kishiya. Ita tasan ba yinshi bane don yasha fada baida ra,ayin yin mata biyu a yanzu sam haka yasa ta kara sakankancewa da bai taba mata kishiya ke nan. Ido ta runtse cikin takaici tare da fadin ina tausaya maki yar yarbawa ko yar filoce don zama gidan mukhatar saiya koma mata tankar zama cikin kabari. Tasan irin taron data shiryawa zuwan amaryan wanda manyan malaman dake mata aiki suka tabbatar mata dashi kuma ta amince da aikin su dari bisa dari don sunsha mata ai kuma ta gani ta yaba da aikin nasu don hakanema akan wanan din bata da matsalan komai a yanzu don tasan karshen yarinyar waje road zata nufa . Nan dai kowa ya shiga fadan abinda ke cikin zuciyar shi kamar yadda al,adan mata yake in iri haka ya faru suna goyon bayan bangaren da suke suna ganin ba ai masu daidai ba. Komai an saka a gidan babune kawai babu cikin sa hatta abinci kusan na wajene da komai na bukatan mace . Ranan ma a gidan yan uwa suka kwana amma da shirin su kan tafiya komawa kaduna Allah kadai yasan yadda nake ji a zuciyana a lokacin. Suko sai hidimar gaban su sukeyi kowana kokarin hada kayan shi wuri daya don an fada masu karfe takwas na safe jirgi zai tashi su zauna da shiri . Wani zazzabi zazzabine nakeji don haka na kwanta bayan na idar da sallah na ranan saidai ba barci nakeyi ba ina dai kwancene kawai ina kallon yadda yan uwa ke shiri amma badani da fatima ba lokacin. Anty Amaryane ta shigo dakin lokacin gani kwancen da tayine yasa ta fadin lafiya dai ko Amarya ?. Sanyi takeji Fatima ta fada kafin na samu bata amsa kallon Faiza tayi tana fadin kun samu abinda kuka bata tasha ko ? Anty kinsan halin yar nan taki fa ni wallahi tsoroma nakeji kada yazo yai mata yawa haka a jiki ta kasa komai sai kuma ta kama baki kota tuna da anty take maganane oho ? Au kema kinbi zancen gwaggonin ku ke nan ashe Faiza da suke fadin wai yau ango ya shigo ya kwana a nan duk da sun san muna nan don gulma. Wanan wai wani haline haka su gwaggo keyi ne don Allah wai haka dazun fa suka kama diban kayan kitchen wai zasu samu simple a sayo masu idan mun koma gida har saida dayan matan yarbawan nan tayi masu magana kan haka bai dace ba ai. Anty hauwa ce ke maganan a lokacin ta kara fadin ko a gida naji mommy na fada wai sin dibi kayan cikin akwatunan nan masu tsada. Don Allah ki bari hauwa anty tace wallahi ai shiyasa kikaga mommy ta dauki kayan ta mayar dasu dakin daddy. Watau dai mutanen nan sun tabbata yan son banza ke nan dai wanan wani irin haukane haka wai don sunga abin kamar banza suke yin hakane wai ? Wayana dake gefena yayi kara na kai hannu na dauka sokone daga Felix yasa na bude da sauri ina karantawa. Da farko murna yayi min tare da addua, sai na biyu da yake sheda min wai sunyi gobara a shagon su na Idi,iroko dake lagos sunyi hasara sosai a wajen. Ban bata lokaci ba na tura mai da sakon jajen kan hakan ina tayasu bakin ciki da abinda ya faru din shima ya turo min daya gode. Wanan labarin daya ban ya tsaya min a zuciya dan nasan wajen sosai wurine babba da ake aje kaya idan an shigo dasu kafin a raba zuwa garuruwan da za a kaisu. Tun jin wanan labarin na dunkele a wuri daya ba abinda nake tunawa sai irin dukiyan dake makare a wajen a gaskiya na tausaya kwarai da wanan abinda ya faru din. Ina kiran ummana da Amar dako wani lokaci yana kirana kai da kai mu dan yi hira ko ya fada min wani abu don ban bar gidaba saidana canza masu waya ga baki dayansu. Hakan yasa yanzu yana kirana sosai don suna kaduna suna jiran mutanen lagos da zasu tafi tare zuwa gida duk da Faiza ta kwarmata min cewa wai ance ai a nan kaduna su zasu zauna yanzu. Nasan umma ba zata yarda ba dan garama da ace ina gidane har yanzu mukazo idan nace zamu zauna a nan zamu zauna din tare. Waya take ta faman kira amma ta kasa samun shi don haka ta kara hasala dashi sosai a zuciyarta don saita dauki hakan ai rainin wayau ne yake mata at list ya kamata ya kira yaji lafiyan ta ai kamar yadda ya saba yi a baya. Bata samu jin labarin shiba sai baya karfe tara daya dawo gidan zuwa lokacin ta gama kuluwa dashi sosai a lokacin. Watau sai daya gama rawan kanshi ga amayarshi da yan uwanta ya dawo gida kilama ko yanzu din wani abu yazo dauka ya shigo tunda tasan dole ranam a gun amarya zai kwana tunda ta tare. Yawan mutanen dake gidan a lokacin bai hanashi shigowa part din nata ba haka ya fara gaisawa da mutanen da suka rage basu tafi ba har yakai kofan dakin nata yaja ya tsaya don muryan mutane da yakeji daga cikin dakin hakan ya tabbatar mashi da ba ita kadai bace a dakin lokacin. Kamar sun san yana tsaye wata ta bude kofan zata fito a lokacin hakan yasa ta san da yana wurin tsaya da sauri ta fara gaidashi cikin dan daga murya don naciki su sanda zuwan shi a kofan. Nan matan dama su hudune a dakin kuma suma da safe zasu tafi bakine abokanta da sukazo daga nisa sai yan uwanta mutum biyu suma. Ya dan dauki lokaci kamar yana duba wayanshi kafin yasa kai ya shiga dakin da sallama yana duban inda suke zaune. Tare da wata matar abokin shi da tazo daga Niger republic aminiyar ita hjy falmata dince sosai kuwa tun shigowan shi ta fara mai ba,a da ango ke nan Ashe amaryan zata bari mu ganka kafin tafiyan mu dan murmushi ya sake yace ai a marya bata rikeni ba kafin yai magana