← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 337

Sashe 24

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

lokacin dana fita da ruwa. Umma na fada da sauri a cikin hausa nake fasin kamar wanda ya han kudi da nake tallan ruwa fa shine wanan mutumin. Tambayan da zan maki yanzu ke nan kika rigani ashe shi din dan sandane ke nan nifa Sahiba wanan abin yanzu ya fara bani tsoro gaskiya. Fada muka ji an rikice dashi a wajen gidan mu tsakanin yarabawan gidan da iyamurai da muke haya tare. Da sauri muka fito don hayaniyar yayi yawa duk dako darene wai wani iyamuri yace da ace yaran yarbawan gidan suka tsunci wayan nan ba zasu bayar don duk barayi ne son kudi yayi masu yawa sasai. Tofa ashe a gaban iya wale ya fada aiko nan ta saka kururuwa duk sauran yarbawan suka fito a cikin dakunan su ana fada. Saida kyat suka watse a lokacin nikan nayi barci ni da Amar sai umma dake zaune tana sallah take jin abinda suke fada a cikin fadan nasu. Washe gari kuma tunda asuba suka dasa fadan a inda aka tsaya a cikin zafi iya wale ke fadin wai e go say dat naw for yaruba becos sahiba mother na his ashawo. Inna lillahi naji umma ta fada da karfi na dago daga saka takalman da nakeyi na dan kalleta a inda take zaune din. Naji tana girgiza kai tare da fadin ni iya wale zataiwa kazafi a gidan nan kan wanan maganan yanzu kuma. We all know dat u are sleeping with her when your wife is not in d town shabi na lia i de talk ta tambayi sauran. Ai kafin umma tace me nakai waje ina fadin iya wale so ur tin don come to my mama again ? Na kalleta kallo a cikin fushi cikin turanxin su na lagos nace yau zan fadi abinda kikeyi da mazajen su a cikin dare idan suna barci basu sani. As from today u wil not tell lie for any body again in dis house no be u i see dat night with baba tunde on d floor ? An dat day again d same tin i saw u nicked baba Alaba de for ur back abi na lia i talk ? Swear if i tell lia for u naw, haba kai kace wani irin ruwan zafi na wasa matar shi yadda ta yanka ihu hankalin kowa saida ya tashi wurin. Ita ko iya wale dafe kirji tayi tare da fadin yeh Sayiba ehmi ? Yes u iya wale, na u a i saw dat day in d night with dem abi na lie i talk a wani irin maraice tace ah haba sayiba why why please ? Why u de telling dem lie sayiba ? Shabi lie no good wen u tell dem lie naw for my mama ai kafin tace zata bada amsa iya Alaba ta zo gaban ta tana girgiza tare da gyara danmaran da tayi tana fadin . Ai sai ihu ya tashi suna fadin sham sham on u iya wale , u no de feel sham sleeping wit somebody husband wuuuu. Danta wale yazo daga baya ban sani ba ya kai min duka sauran mazab gidan suka taso mai suna why , why go beat her ? Sai fadan ya koma a tsakanin su suka shiga zagin shi iya wale da yau taga masifa daga inda take ido yayi ja ta shiga surfawa wale din kuma ashar . Wanda da alama bata ma san abinda takeyi ba a lokacin don tashin hankalin data shiga a lokacin kan abinda na fada tayi. Nikan bayan na gama hada fadan na tatara na bar wirin cikin sulalewa na shige dakin mu na zata umma zatayi min fadan hakan danayi mata don tana babba sai naji shiru bata tanka min ba.
Chapter 24 · 0% Book details