← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 303 OF 337

Sashe 303

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mun samu yan maidugurin sun iso wai yan daukan amarya bayan wa yanda suka kwana a nan mazansu da mata nagodewa Allah na kuma godewa yan uwa da suka taru suka fitar dani kunya suka nuna nidin yar dangice gaba da baya. Don yan uwan umma ma da dangin mu na kauye ba,a barsu a baya ba duk sunzo daga kauye din don an aika masu suma kuma sunzo. A yadda suka buga anko wai duk sabodani din ya kara sana fashe da kuka ga ko ina ya cika makil da dan mutum anci ansha sai sam barka ga kowa lokacin. Yan kai amarya mutum ashiri aka bukata saura yan uwan ango ne da abokai wai ashe shima mukhatar din yana kaduna a ranan. Jin cewa tafiyan na jirgine yasa su gwaggo hari da tawaganta dama wasu da ban zata ba duk suka shirya yimin rakiya don su karas da komai yadda suke jin labari. Mommy ce akace su zauna su sallami baki a gida daga baya zasuzo tare da ummana da wasu sauran yan uwa ganin daki wanan alkawarine da akai masu. Haka gwaggo Amina ta fito rike da hannuna zuwa falon daddy dake cike da yan uwa da abokan arziki kan inyi sallama dasu lokacin. A tsakiyan falon aka zaunar dani bayan wasu daga cikin iyayyen mu mata sun rikoni zuwa falon nidai sai binsu nakeyi don ban taba sanin al,adan hausa fulani haka yake da akidu masu tarbiya ba idan bawa yabisu daki daki. Daddy ne ya soma magana bayan budan taro da addua ya fara min nasiha saidai ince ya dora inda aka tsaya don nasiha kan nasha a wurin yan uwa dama. Har yakai akaba baffah hamza dama shida wa yanda suke yan sa,oi kusan baffah hamza din shine ba karshe a lokacin. To Sahiba Alhamdullahi mun godewa Allah daya bamu iko tare da lokacin sauke wanan nauyi da dan uwan mu yabar muna. Alhamdullah don zan iya cewa kinyi dace da miji wanda yasan darajan ki tare da kimar ki kuma da tausayin ki a matsayin kina marainiya a yanzu. Don Allah sahiba kije ki zauna tsakani da Allah a dakin mijinki kada ki yarda wani abin asha ya fito daga gareki ko wani hali da baida kyau damu bamu sanki dashi ba. Kirike Allah da mairaicin ki Allah yai maki jagora da haske ga almarin ki ya baki zuria masu albarka yasa ku gama lafiya ki kara hakkuri shine maganata ta karshe dake. Haka suka fito dani ga yan uwa nan kan sunzo bila,adadin gaskiya nidai kodan me sukazo naji dadin ganin hakan daga garesu. Bayan mun shiga motoci airport aka nufa har yan rakiya sai a nan ne naji ana fadin aiga angon can ashe harshi sukazo suna gaisawa da mutanen mu. Ba,a tsaya jiran komai ba aka fara kidaya masu zuwa dama sun fito da shirin su na tafiya har wa yanda ba,a kidaya zuwan dasu ba. Nidai ina biye da gwaggo har zuwa cikin jirgin ba,a dade ba jirgin ya tashi wanan karon tare da anty Amarya hjy karima nake zaune. Tun zaman take kara lurar dani abubuwa wanda hakan yakara sa kaina daukan hasken zaman kishintaka da mata keyi muna jin labari. Yan uwane da abokan arziki sukazo taron mu zuwa gidan hjyn shi inda su gwaggo suka bukaci a kaini a cewan su sai na fara kwana wurin ta taimin masauki kafin zuwa gidan da zan zauna din a ciki. Nan ma mutanene sosai muka sama anci ansha duk a gidan mahaifiyar nasa wanda ba haka ita uwargidan taso ba don hakan ya bata mata wani daga cikin tsarin ta da sukayi. Don basu da kunya har gidan hjy sukazo wai don me za a ajeni gun hjy din ace sai gobe ko wani abu can su sam ba haka tsarin al,adansu yake ba. Su gwaggo hari dasu Anty Amarya suka hayayakosu da fada suma kan cewa mu tamu al,adan fulanin mu haka muka gada sai amarya ta sauka wurin surukarta an bata girman ta kafin a kaita gidan mijinta inda zata zauna. Kiri kiri suka nuna su basu yarda da hakan ba don sun shiryawa tarona gidan don me za a bata masu tsarinsu da sukayi yanzu zakace sune iyayyen miji a yadda suke kafa doka da fadi idan kana wurin a tare damu. Nan su gwaggo hari suka nuna masu bafa su kadai suka iya iskanci ba suma da nasu a boye gwaggo harine ta fara fadin wai ku suwaye da zakuzo muna da wanan hayaniyan hakane ? Munce ga yadda al,adan mu yake kunce sai mubar al,adanmu dole mubi yadda kuke so to mu ba hakan al,adan mu yake ba dole sai ta zauna a hannun uwar miji kafin ta shiga zuwa dakin ta itama ta saka mata albarka. Ji mun mata da kafewan tsiya wata ta fada daga gefe to har in zaman lafiya kukeso a aiwatar dolene taje dakin ta a yau din nan kamar yadda kowa yasan anayi din, kuma wanan sallon uwargida kanta bata yarda dashi ba don ba haka aka san anayi ba ko ina. Au uwargida ta aura ko mijin su da mahaifiyarsa sune muka sani a jigon aure babu abinda ya damemu da damuwar uwargidan a nan mu . Kowa ya tsaya a matsayin shi don bamu kawo gareta ba mu har yanzu don haka kada ki jefo muna zancen ta a nan ki zo zaki kafa muna doka haka tsarin mu yake ga al,adan mu. Kallon gwaggo hari din matar tayi ba laifi don a tsare take da gani itama watace mai fada aji ga yanayin ta don haka ta dan daure ta sake fadin . Au naku sallan da kukazo dashi ke nan munan kujerane daidai muke da mazaunan kowa don haka zamu zuba daku ga haka. Zakuyi kunya kuya kuwa wanan karin dan yar mu na daidai da kowa ta kara binsu da wani kallon yare dayan tayi mata suka fice daga dakin a fusace kafin hjy karima tace kai nadai gode da hanza ya tsara hakan baki ga wani kallon wullakanci da suka shigo muna dashi ba da farko. Sai bin mu da kallo takeyi daga sama har kasa tana wani mere bakin ta sun shigo da niyar wullakanci sin zo gida ai kodame suke takama kuwa gwaggo harin ta sake fada. Lalai za ai zama a wanan wurin kuwa gwaggo Amina ta fada sai hjy kafima tace in dai wanan ne zasuyi daidai dan banjin komai a gun Sahiba ni. Karamci kan mun gashi karfe takwas na dare an gama shirin dinner din da aka shirya za, ayi harni din na gama duk wani shiri don nasan da hakan kada a girsheni yasa wanan custermer din nawa ta hada min kayan dinne na gani na fada tun daga dubai aka kawo min su a hade. Duk wani wanda ke wajen saida shigana ya burgeshi don zakace nidin wata yar sarkin yarbawane a yadda nayi ado da tsara jikina don ba doguwar riga bace a jikina lokacin, zanine da riga na wani lace dinkin buba irin na yayi daya sha haduwa wurin kyau. Don duk inda na juya walkiya nakeyi wal wal daurin zaninma na yarbawane nasan yadda suke komai dan haka tsarin yarbawa na tsara a komai nawa wurin. Kowa ya zuba ido zan shigo aga fuskana a lokacin don duk basu sanni ba auren ma a bazata yazowa mutanen shi da yan uwan shi. Saidai lokacin da muka shigo din fuskana yana a rufe da dan wani mayafi dayai shige da kayan sai walkiya yakeyi ba mai iya ganin fuskana lokacin. Kamshi kan shi angon sai da abin ya hau kanshi balleni da kamshin yake a jikina yana hawa min sosai ina jinshi aikin anty amarya da gwaggo hari ne wanan din. Cool music suka saka na oldscul a wurin na wani mawaki nan abokansa suka dauki tafe da shakiyanci gareshi wasu yan mata masu kaya iri daya suna gaba da bayan mu su hudu. Daga inda hjy Falmata take zaune da tawaganta tace wanan ai iskancine ashe dama haka suka shiryawa abin ban sani ba har suna fadin wai yazo a kuraren lokaci haka ? Bana fada maki naga suna shiri ba lokacin a bayana su anty hawauce faiza hamida da zainab yar wurin gwaggo Amina sune a matsayin yan matan bukina. Ba irin zagin da anty Nabila bataiwa hauwa ba da gwaggo hari tace sune za a dasu ba a yarda wani dan waje ya shigo yaci da cewan sauran yan uwanmu dake wajen bukin wai. Nan yaren kanuri ya tashi don ganin su don ba wace bata hadu ba a cikin su wurin sai nasu adon ya bambamta dana gaban mu din. Bayan mun zauna aka dan gabatar tare da bayanai nan shagali ya fara masu bayanan da sharhi suna fitowa sunayi. Gwaggo hari ta karbi abin magana ta soma magana tare da gabatar da kanta a matsayin gwaggona take nan ta fara fadin tau yan maiduguri. Ga amanan uwargijiyan ku nan Sahiba bafulatanan asali sai wurin ya dauki hayaniya kowa da abinda yake fadi tana dariya, . Tace OK duk da dai gida tazo ba wani waje ba don nan gidane gareta ango kuma uncle dintane yanzu kuma mijinta. Kiji min abinda wanan matar ke fada wata daga gefen uwargida ta fada tace haukane kawai irin nasu kafin ta gama zance taji gwaggo hari na fadin. Nace hakane don shi mukhatar kamar wani jigo yake gun yar mu koda bai aure taba ga kuma aure a tsakanin su yanzu Allah ya hada. Don haka zan kira garesu da a zauna lafiya uwargida muna mai baki hakkuri tare da kara danka amana a gareki dan nauyin bana mukhatar bane shi kadai a yanzu nan dai taci gaba da bada shawara kan zaman lafiya tare da dan barkwanci ta fita wata kawar gwaggo din darta rakota ta shigo tayi bayani itama kafi ta fara bayani . Inda ta bukaci hankalin mutane kan za ayi budan kai a lokacin daga can hjy falmata da kungiyan ta suka soma fadin wanan ai iskancin yan kadunane zasu kawo mutane a nan su nuna wayewa da iyayi kowa wasukafi wayewa suke gani oho ?. Kowa na kallo aka kawo kujeru biyu yadda ta buakata
Chapter 303 · 0% Book details