← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 337

Sashe 26

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Idan wani abu ya samu Alh a yau moddibo ne silan hakan don shi ya kashe shi ina tsaye suke waya dashi ban san ko suwa ya fadawa Alh ya gani ba iya dai abinda na sani ke nan a yanzu.
Amma kuma kin san dai ba zai fada mai abinda zai halaka uban cikinsa ba da kansa don ke kanki da kike fadin haka yafiki son shi.
Ran manyan mata ya baci don haka har takai hjy tayi magana a ranan kan irin izigili da iya shegen da hjy karima kanso ta kawo masu a gidan wani lokaci.
Haka dai kikace don ko abin a zuciya yake ba a fili ba shi dai na gani don da kin san hakan ai ba zaki fadi hakan ba a yanzu ai.
Don Allah hjy wanan wani abu kuke son kawo muna a yanzu kuma mijin ku yana a cikin wanan irin hali haka.
Ku har kunga wurin fada a yanzu tsakanin ku makin ku taimaka mashi da addu zaku tsaya kuna sayar da hali haka.
Dr bari abin na karima baida armashi wallahi duk yadda ka iya hakkuri sai ta kaika kull, daga inda hjy karima take tace eh tunda ba gaskiya kike so ba ke dole ki fadi hakan ai.
Ya kara daga hannu yana fadin kunga don Allah kuyi hakkuri yanzu haka sai mun kai Alh asibiti don jinin shi ya hau sosai.
Innalillahi suke fadi bayan hjy karima dake fadin kaji ba ko yanzu na fada duk ko meye ma modibbone silar tayar da wanan zancen.
Nabila ce dake cikin shirin fita school sukaji kururuwan hjy karima tana neman agaji kan mahaifin nasu ta fice daga dakin rai bace.
Don abinda hjy karima keyiwa mahaifiyan su a yanzu abin yana matukar damun su sosai a rai.
Saidai babu yadda zasuyi ne don hjyn su ma ba zata bari suyi mata wani rashin kunya ba a cewan hjyn tasu ai kishiyar tace tana ganin a yanzu daidai suke a idon mijin su.
Gashi a cikin yan kwanakin nan wani irin tsoro da fargaban ta suke ji don ta riga data dasa masu tsoron ta a zuciyar su.
Basu Nabila kadai ba wanan abin yake damu a a yanzu ai duk wani wanda ke gidan kuma ya shaki hanyaki yai arba da ita a ranan data ai watar da sihirin shima abin ya shafe shi kamar yadda bokan ta ya fada mata tayi takuma yi din.
Ya kuma fara tasiri a jikin su a lokacin sihiri ke nan duk da ita a ganin ta bata samu yadda take son samu a garesu ba .
Don gashi duk da tana ganin tsoron ta a fuskokin su sai ya kasance kuma hjy din bata shakun ta a yadda taso ta kasance.
Alh dake kwance ne ya dago kai jin wai za a kaishi asibiti yake fadi cikin karfin hali dr a barni a gida ba sai naje asibiti ba, zan iya kula da kaina a nan ma ya fada cikin yanayin tausayi.
Ya kara da fadin idan har naji sauki ga goben nan in Allah ya kaimu nake son yin tafiya.
Tafiya kuma Alh kana cikin wanan halin ciwo haka hjy Adda ta fada yace insha Allahu zan kokarta naga na tafi don abu mai muhinmanci zai kaini inda zani din.
Duk da haka da ka bari har kaji , , , , a ikon Allah idan tafiyan baida muhunmanci a gareshi ai ba zaice zai tafi ba sai dai kawai idan ba a son ya tafi ga goben ne to amma mai abu ja mara abuja irin haka ?
Allah ya kara lafiya Alh hjy Addah ta fada don ta gane me karima din take nufi a lokacin a zaton ta hjy na fada hakane kawai don ya kasance ranan girkinta ne goben shine bata son yayi tafiyan dayace zaiyi din don hakana.
Dan murmushi Addah tayi kafin tace ikon Allah wani irn dare ne jemage bai gani a rayuwan sa saidai wanda ba,ayi yana raye ba kuwa hjy ta fada.
Ko ya gani yana son kara gani don hakan bai ishe shi ba ai itama karima ta mayar da amsan gareta.
Yanzun nan zaku bar wurin nan ya fada rai bace likitan yace shine abinda yasa nake son daukeka a gaban su tunda sun zama haka a yamzu.
Ke hjy keda nake dauka mai hankali zaki biyewa wanan da kurciya ke dawainiya a kanta lafiyan mijin ku shine abin nema a yanzu ba wanan shiriritan ba gaskiya.
Kyalesu dr nagane duk shirme da jin dadine ke rudin zuciyar su a yanzu idan na tafi sun huta ai da ganina.
Hakan yasa duk suka ja bakunan su sukai shiru don yadda yai maganan a cikin bacin rai da nuna takaici a gare su.
Chapter 26 · 0% Book details