← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 337

Sashe 143

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da inyi shiru gara ina tunatar daku gaskiyan abin ki biya shine ka,ida ki karanta don namu ba irin nasu bane namu ba takarda bane rubutune ta yanan gizo ki biya ki karanta shine ka,idan abin yar uwa kin biya ki karanta a cikin salama ba tare da shiga hakkin wani ba bawai ina magana akan nawa ba kawai a, a yar uwa idan ance paid novel ne son Allah kikai zuciyat ki nisa ki daurekibashi bayan don kariyan ma,aunin ki sai mai hankali da imani zata fahinci kalamina Allah yasa mufi karfin zukatan mu a matsayin mu na musulmai ku yafe min idan na fadi ba daidai ba gareku. Falon ne yai shiru na dan lokaci kaina na kasa duke ina danna wayana da ba komai nake duba a ciki ba lokacin don kawai na kawar da shirun da falon yayi ne a raina. Jin shirun yayi yawa yasa na dago kaina naga me yakeyi a lokacin kawai sai na samu niya kurawa ido ashe yana kallon abinda nakeyi da wayan. Nauyi da kunya naji lokaci guda cikin sarkewan murya na daure na kokarta na dan zamo saman kujera ina gaidashi cikin girmamawa. Saida yai dan jim ya amsa min da yaya gida da aiki nace Alhamdullah ina komawa saman kujeran na zauna. Shirune ya kara biyo falon na kamar minti biyu kafin yayi gyaran murya duk muka dago kai muna kallon shi lokaci guda. Yace a cikin muryan nan nasa mai taushi irin na ustazai ina fatan kin san dalilin kiran ki da nayi a wanan lokacin a cikin hausa. Na girgiza kai alaman ban sani ba ya dan murmusa a karo na biyu danaga murmushin shi na farko a jos da yake tare da kakan shi sai kuma yau dayai min a falon nasa. Naji yace OK menene ra,ayin ki akan bukin da za ayi sturday na mahaifina ko bake kika turo min da sako bane ya fada yana tsureni da idanun shi. Ban dago kai ba don nauyin shi da nake ji sosai saima wasa da nakeyi da yan yatsun hannuna da suke zara zara sun sha penti don fashin sallah da nakeyi na digasu da safen nan don kwaliya. Muryan shi naji yana fadin kinyi shiru ko bakya magana ne kece fa kika kawo wanan sharan yanzun kuma sai ki min bayani yadda ya dace inji a gaba idan zan iya. Na dago kaina fararen idanuwana suka sauka akan shi dana dan kalleshi kafin in bude bakina ina sake dan murmushi daya kara baiyyanar da asirin kyau na a fili ina fadin Sir . Subbahanallahi yace a zuciyar shi yana lumshe ido gaskiya badai kyau ba amma bata waye bane har yanzu don akwaita da sauran wayewa saidai akwai kamun kai da ake son macen musulma dashi kam gaskiya. Nasake fadan Sir saboda naga haka baya cikin tsarin musuluncine kaima ka sani don haka da wanan abin gara kawai ayi abinda Annabin Allah ya koyar damu game da mamatan mu da zaiyi saurin kai lada a garesu. Shine addua ta hanyan kai sadaka tare da abin sallah a masallataiya da sadaka a inda ya dace mai zai hana a aika da sadaka ga gidajen marayuwan na gaskiya da suke neman taimako irin haka a ciyar dasu da niyar ladan yakai ga marigayin. Masha Allah yace ba tare da sanin kalman zai fito a bakin shi ba lokacin don tunda na fara magana suke kallona dashi da Felix din suna kallon yadda hakorana farare suke jere kamar anjera min sune haka ga wani dan wushirya a tsakanin su daya dan kara min kyau idan ina magana. Mai akin shice ta shigo dauke da tire da dan kofi a cikin sai data gaishe mu ta aje mai tana bude kofin a gaban shi hayaki ya dan tashi daga cikin kofin mai nuna zafin ruwan shayin a lokacin. Bayan fitan ta dan shiru ne ya kara maye gurbin falon saida ya dauka ya dan kurba sau biyu ya rike kofin yana fadin . Ummm,humm ya ustaz ya fada a baiyane ke muke saurare ko kin gama bayanin ki ke nan kallon shi nayi na dan sake murmushi don jin sunan daya kirani dashi da ustaziya dan kawai na fadi ga yadda za ayi a addinan ce. Shiru nayi naci gaba da wasa da yan yatsuna ban dago kai ba bayan murmushin dana danyi da farko can naji muryan shi yana fadin. Kinyi shiru ko baki tsara komai bane game da hakan nawa kike ganin wanan tsarin naki zaici ko baki lissafa ba kika gabatar da shawaran ? Da sauri na dago kaina don jin abinda ya fada don na zaci a cikin fushi yayi maganan saboda shishigin da nayi masu nabada wanan shawaran. Kofin shayin shi ya kara kaiwa bakin shi ya kurba ya aje saman table din don ya fahinci ba zan fadi wani abu ba akan hakan . Ya aje yana fadin cikin mamaki ok kina nufin wani zan saka yayi wanan tsarin da kika kawo a yanzu ko me dole keda kika tsara abin kece zaki aiwatar da komai daya shafi hakan a yanzu shiyasa na kiraki a nan yanzu. Ya mayar da kansa ya jingina a kujera yana fadin ina fatan kin shirya yin hakan daga yanzu don yau wednesday babu wani sauran kwanaki garemu. Milayan nawa za a baku ki gudanar da wanan aikin da tsare tsaren ki ki fada yanzu a tura maki kudin sai a fara komai yadda ya dace ayi. Shi aikin Allah idan za a yi ba dole saida kudi mai yawa ba ko kudi kalilan sai su wadatar da wanan plan din ai. Sai naga ya bini da kallon mamakin jin abinda na fada sai kuma ya koma lumshe idanun shi kamar ba zaiyi magana ba a lokacin. Wani irin mamakine yake yi na yarinyar nan don ya gwadata da dama a fannin kudi tana cinye jerabawan shi da yake mata din. Felix ya ambata yayi wani amsawa da sauri yace ka miko min chack dina da biro a daki na rubuta mata yanzu felix din da bai san zancen da akeyi ba don shi baijin hausa kuma a cikin hausa muke maganan dashi a lokacin. Felix na shiga bai kara kallon inda nake ba sai zaman daya gyara yana lumshe ida da tokare haban shi da hannun shi daya ya dora fararen kafan shi saman dan table din gaban shi yana cigaba da tunane akan abubuwa. Na dago kai na dan kalleshi idon shi a lumshe sai kuma nakai kallona a inda tsufin nan suka tashi dazun da muka shigo naji gabana ya fadi lokaci guda. Sake kallon shi nayi yana zaune a yadda yake din nace Sir dai ko ba kudi mutumin kwaraine shi ga kyau ga kirki ga kuma kwarjini na fada a raina. Ido na tsura mai ina kare mai kallo dan gashine irin da matasa zamani ke bari yanzu a fuskan su zagaye a fuskan nasa bakikirin ya karawa fuskan nasa annuri sai dan baki karami hanci har baka farine kuma sol dashi kamar wani jinsi ne na wani nahiyar. Abinda nake ganine yasa nayi magana da ya maye gurbin shirun da falon yayi a lokacin ina fadin ya kamata ka dinga nisanta kanka ga duk wani wanda ya fito daga fannin mahaifin ka mace ko namiji don suna binka da mugun nufi a koda yaushe. Idon shi ya bude ya tsaya yana kallona har na gama fadin abinda zan fada din ya wani murmusa tare da fadin nasan da wanan tun ina karami basa kaunana sam gaba dayan su Yanzun ma da abinda suka shafama a kujeran nan idan da son samune lada ka yarda ka zauna a saman shi sai bayan gama bukin nan baki daya don manufan su su jefeka ka kafadi daga wanan bukin da zakuyi. Fitowan felix ne dakin dauke da abinda ya aikeshi yakawo mai ya mika mai shine ya hanamu cigaba da maganan. Rubutu yayi saman check din ya miko min tare da fadin gashi ki karba ayi yadda ya dace aikomai na taso daga inda nake zaune. Na nufoshi don na karba a cikin ladabi ina fadin Allah ya karba yasa haske yakai gareshi dashi da sauran mamatan mu ga baki daya. Ina isowa wani irin kamshine mai kashe jzuciya yaji ya daki hancin shi lokaci guda saida ya lumshe idon shi yana amsawa a cikin taushin murya da Amin ya Allah. Don gaskiya yaji dadin wanan adduan nawa don shi yana son yaji wani nama mahaifin shi addua irin haka. Har na juya naji yana fadin ki tabbatar da kunyi amfani da kudin sosai ga family din ki nina baki bakin hakan ki dauki iya bukatanki ki bada saura ga wanda kike so final. Ina fita ya kalli felix da ke kokarin mikewa tsaye lokacin yake fadin a samo wasu kujeru yau din nan a saka a falon nan ka kwashe wanan a fita dasu. Ya dago kai tare da fadin oga wanan fa basuyi ko wata uku ba da aka shigo dasu falon nan ko ka manta da hakan neya fada yana kallon kofan dana fita. Yace dashi a cikin dan tsawa do as i said felix ko ka manta da mahaifiyana zata shigo gobe da yan uwan ta ne kasan nan wurin adduan . Yace sorry sir ya dukar da kanshi kasa shi kuma ya shige zuwa ciki zuciyar shi cike da tunanen zancen da mukayi dashi a falon. Tun safe take tsaye tana faman aiki duk da ba wani aiki bane takeyi umurni ne ga abinda zasuyi mata don girki da gyaran gida saboda wayan da tayi da mommy ta sheda mata dawowan mijin nata a ranan da ita mahaifiyar ta tursasa mashi sai ya dawo gida matansa ta dawo dakin ta itama. Yayi mamakin jin haka don shi sam baiso haka baima cikin tsarin shi a lokacin don gaba daya yaso ya basu mamakine da sai sun girgiza dashi amma kuma aikin gama ya riga da ya gama mommy ta bata masa tsarin komai yanzu. Tana zaune ta tsala kwaliya daga ita har yaran ga wani irin kiba data zauna tayi a yanzu tun bayan haihuwan yar su na biyu ta fara wanan kiban daya kara munanta ta a yanzu.
Chapter 143 · 0% Book details