Sashe 60
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
? Saida tayiwa hjy din wani kallon raini take fadin wani abu zaki tambaya bayan baku iya tsawata wa yaran ku idan suna abinda ba daidai ba. Karima ni din kike fadawa hakan tace an fada kewa da baza a fada maki hakan ba wai dama daurin gindin ki suke samu ta zauna a gida tace bata da lafiya amma yanzu ta dawo falo da kawaye suna muna shewa a gida haka . Shewa kuma wani irin shewa ne da banjiyosu ba a dakina af dama ai ba zaki taba jinsu ba ai tunda da sanin ki suke komai da sukeyi ai. Anan fada yaso ya kara kaurewa sai su Nabila din suka ja mahaifiyar su a cikin takaici suka shige part din su ransu na masu zafi ga wanan disgawan da hjy karima din tai masu a gaban kawayen su Da kuma nema ta raina wa uwansu wayau da take son yi a gaban kawayen su din a yanzu don basu karasa fita gidan ba a lokacin. Duk da saurin da takeyi saida ta tsaya ta batawa kanta lokaci wirin fadan da baida dalili ko nasaba don kawai neman nayi a gidan. Irjn haka take masu koda kallo sukeyi duk da akwai kayan kallo a ko wani part amma basu isa su bushi iska su fito main falo suce zasuyi kallo ba a yanzu kamar yadda suka saba yi a baya yanzun ne zata korasu zuwa ciki. Su dai a takaice wanan ahalin a halin yanzu nasu ya samesu basu da kwanciyan hankali idan garin Allah ya waye suna sauraron da wace zata bullo masu dashi na bacin rai a garesu. Zaune nake nayi tagumi gashi na fada sosai a cikin dan kwana ukkun da nayi a kulle a dakin ina cikin fargaba da tashin hankali wanda ba zan iya musulta shi ba a lokacin. Hakan yasa na zauna nayi tagumi ina zulumin halin da umman mu zata shiga a wanan lokacin na kiyasta abubuwa kala kala a zuciyana kan hakan karshe kuma na shiga jero addua a bakina. Naji an tur kofan dakin duk da ban gane lokaci ga hakan amma ina iya amgani da lokaci in fahinci lokavin da ake ciki a wuni. Hakan yasa na fahinci cewa lokacin dai bayan karfe ukun rana ne la, asar bata karasa yi ba a lokacin. Kofan naji anturo nayi mamakin jin hakan don ba lokacin da ake budewa bane a shigo min da abinci don da safe zasu kawo min abinci lafiyaye da drinks sai kuma karfe dayan rana zasu kawo min shi da yamma kuma karfe bakwai daidai suke kawowa . Ban dagoba ban juya ba don ganin mai shigowa din ina zaune takure a inda nake azaune din muryan da ban taba zaton ji a wanan wurin ba shi naji a lokacin . Umma ce ke fadin mun gode daga kofan na juya a cikin wani irin juyi na firgice lokaci guda ina kallon kofan na mike da gudu zuwa wirin kofan da umma din suke suna shigowa dakin da nake ciki din. Umma i miss you dey carry me come here, i don no wetin i do for dem dey kidnap me here sai na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya ina fadawa jikin umma din lokaci guda. Har lokacin yana tsaye a kofa tare da harde kafa yana kallon haukan da nakewa umma din sai da umma ta dafa ni tace stop crying he be ur brother Abubakar son of ur aunti nd his father is ur baba broda. Jin haka yasa na dago kai daga jikin umma da sauri na dan kalle ta kafin na juya gun da yake tsaye ina mashi wani irin kallo kamar na tsoro a lokacin. Ta kara fadin a cikin yarbanci da fatan baki masa rashin kunya ba dai na girgiza kai tare da fadin ban ma ganshi ba tunda suka kawoni nan sai mai ban abinci kawai ke shigowa dakin nan ya kawo min. Naji ta sauke ajiyan zuciya a hankali ta juya gareshi tare datin wani yaren da ban taba tsamanin umma jinsa a bakinta ba, ya amsa mata shima a cikin yaren irin wanda tayi mai din . Wurin shi na nufa na bayan umma din tayi min yaren yarabawa akan in gaida shi a matsayin dan uwana kuma yayana. Na duka har kasa a cikin ladabi na fara gaidashi yana mamaki ya amsa min a takaice yana fadawa umma shi zai dan fita don Allah mu saki jiki kamar muna gida a nan. Ya rufo kofan sai lokacin umma tabi dakin da kallo ta ko ina sai kuma ta fashe da wani irin kuka da ban san dalilin yin shi ba a lokacin. Saida tayi mai isan ta don kanta tabari tara fadin sahiba na rabaku da gatan ku da yan uwan ku kan wani dalili da na zabawa kaina daku hakan a rayuwan mu. Ko yanzu ina nadaman komawa a cikin dakin ku da zakuyi don ban san ko dukane suke da akidan dake rike a zuciyar su ba akan ku. Ku yaranane a yanzu fada maku wanan labadin baida amfani a gareku yanzu don ba zaku taba fahintar me hakan da nayi yake nufi ba. Suma din zasu dauka ra,ayunane na son in shakata wata kila ya fitar dani a cikin su bar kowa nawa zuwa nan inda bamu da kowa na jini a nan din. Kallon kaina nayi jin umma tace ba zamu iya fahintar abinda zancen ta yake nufi ba a yanzu idan ta sanar damu niko gani nake ai na girma nakai munzalin da zan fahinci wani abu yanzu ai . Yanzu ba zan iya cewa mahaifin ku yana raye ko baya raye ba sai dai ga maganan Abubakar din yanzu da muka hadu na fahinci dai mahaifin ku shima baya tare dasu. A kullun zancen mahaifin ku shine makomar ku a cikin yan uwan shi don hakane yake taka tsatsak da ke a lokacin baya yarda ki rabi kowa idan ba niba ko shi saiko wasu daga cikin dangina kuma. Yanzu wanan mutumin ya min alkawarin ba abinda zai samu rayuwan mu dagani har ku muddin yana a raye a duniya. Haka kuma ya ban zabi akan idan ba zamu iya zama a can gida ba zamu iya dawowa nan din mu zauna tunda nan muka saba dashi din. Wanan ya kara ban kwarin gwiwan da har na yarda na amince zan je gidan kodan naga halin da mahaifana da yan uwana sule ciki a bayan mu. Tana fadin haka tayi shiru tare da shiga cikin tunane kafin ta mike tana fadin inane ban daki zata kewaya tayi sallah nan ta barmu zaune munyi shiru shi dai Amar yana bin fakin hotel din da kallin mamaki. Kafin nace dashi ban san ko inane nan ba don bansan lokacin da suka kawoni wirin nan daga shiga mota na tsunci kaina a dakin nan. Na fara bashi labdin yadda abin ya farune umma ta fito bayin tace in tashi inje inyi sallah in roki Allah tsari ga duk wani abin ki a gare mu. Bayan mun idar ne umma nake tambayan umma yadda har ya gane cewa ni din yar uwarshine haka. Murmushi umma tayi kafin tace kuna da kama na asali da zai iya gane hakan idan dama yasa da bacewan mu kuma ina zaton ya sani din dama. Umma ban fada bane ya dade yana bibiyata tun baro wancan unguwar da mukayi har zuwa yanzun da Allah ya bashi sa,a akaina yanzu din. Dakin fada min da wuri zamu gusa daga garin nan muje can nisa dasu ko yanzu din bawai zan yarda in bishi haka kawai bane sai na kalli hankalin shi na gane manufan hakan a garemu da yake son yi. Umma idan hakane ni zan bishi naje naga yan uwanmu in yaso indawo in fada maki irin taron da sukai min a can din. Tsawa umma ta daka min tare da fadun ke yarinyace sahiba kina zuwa rayuwan ki zasuyi kokarin nema su kashe ki. Su kasheni umma na fada a cikin mamaki ina kallon umma din don mamakin abinda umma din ta fada game da zuwan namu wurin yan uwan mu din. Kafin umma ta bani amsa aka turo kofan shine wani na biye dashi a baya da wasu trolers guda biyu ya shigo dakin misalin biyar da rabi na yamma. Kaya sawa ne namu dana umma a cikin akwatin don mutumin ya koma ya dauko daya ya dawo dashi nan yake nunawa umma nata sai nawa da na amar yake fadin zamu iya amfani dasu din mu sa ya sayo muna su din don Allah mu saki jiki dashi don bai daukomu da niyar wani ya cutar damu ba a yanzu kuma.