← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 248 OF 337

Sashe 248

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

gansu kasan a rude suke da ganin mu alokacin gidan. Hjy mairo wai kune a tafe haka suna mikewa tsaye lokaci guda, mune fa umma ta fada har da fadin ikon Allah yanzun nan kuka saukane ? A,a anan dai muka kwana jiya mukazo da dare zamu yola ne muka ratso nan mu gaida modibbo da jikin sa. Ayyah aiko kinyi zumunci hjy hari ta fada tana wani dan kame kame a, a Ammar kin koyi waya da mutumin naka kuwa ? Yace No a cikin turanci don shi yadda nake dan jin hausan baya ji sam sai guda guda yakan fada kuma ba daidai ba . Zaune dai nake a inda na zauna sai mamakin su nakeyi don abin nasu ya kara kulle min kaina sosai lokaci daya. Yanzu kan nasan tabbas wa yan nan mutanen ba zasu taba son mu ba kenan a rayuwan su gwaggo hari matar da muke ganin mutuncin ta sosai. Don ta nuna muna so har da kauna a fili yanzu take fadan wanan maganan haka a kan mu mara dadin ji can da sauraro ga kunnuwan masu ji. Ke ku fito ga Sahiba mommy ta fada a cikin waya nasan da yaran ta take wanan wayan lokacin ba dauki lokaci ba kuwa saiga Faiza da gudunta ta fito. Muka rungume juna da ita ana yaushe rabo duk da raina yana bace a lokacin amma ganin Faiza din sai na dan sake jikina da ita. Yan jan ajin saida suka dauki lokaci suka fito sun fito da fara,an su da farko amma lokaci daya fuskansu ya murtuke. Don sun tsorata sosai da ganina wani irin kyau da dress cikin shiga ta alfarma irin namu na manyan yan matan lagos. Su kansu yanayina kawai ya nuna masu a yanzu ba ajin su nake ba mun gaisa dasu a cikin girmamawa kamar yadda aka saba a can baya ban nuna masu komai a fuska ba suka samu wuri suka zauna. Faiza ke fadin kwanaki kikace zaki dawo baki dawo ba Sahiba nace sorry my dear wallahi tafiyace ta kamani zuwa england daga can na wuce dubai mukayi kwanaki. Na fadi hakan ne kuma da gangan a gaban su mommy din da diyan ta kice dai har fita kikeyi yanzu abin dai ko sauku babu ashe. Nace kin san yanayin aikin namu haka yake muna shiga kasashe da dama ko yaushe da wuya ki sameni a lagos yanzu ai. Dan guntun tsoki Nabila taja daga baya dukda taki sake sautin shi amma nasan ko umma taji wanan sautin na dago ina fadin Anty Amarya fa ? Oh sun fita wallahi dasu Fatima dazun ana buki walima a gidan babban yayarta duk a cikin harshen turanci muke magana. Diban lokaci nayi ina fadin umma mu tafi a cikin yarbanci gwaggo hari harda fadin ba zaku tsaya akawo maku abin sha ba yanzu ta aika yar aikinsu ciki ai No abarshi kawai zamu tafi jirgin karfe biyu zamu bi zuwa yola yau . Amma muna son don Allah idan ba damuwa Faiza ta nuna muna gidan Abubakar din mu je can kallon juna sukayi don ita kanta gwaggo hari rikicin shi da matar shine ya kawo ta gidan. Eh to ko yana gidama yanzu waya sani eh zamu daije gidan mu gaisa dasu koda baya nan idan tazo za a fada mai mun gaida ku ai umma ta fada tana mikewa. Tare da fadin idan Alh yazo muna gaidashi suka amsa kamar ba komai a zuciyan su gaba dayan su kuma suka rakamu zuwa waje din ganin kwan koda me mukazo. Rudewa sukayi lokacin da sukai arba da rantsatsiyar motan oga da muka shigo zuwa gidan nasu wanda nice kuma ke ja bamuzo da driver ba. Umma ce tabawa su Nabila kudi har suna musawa tace bazan baku alher ku karba ba Nabila ko kuma kuna cikin masu zargin muna aikata wani abinda bai dace bane a can. Da saur har suna hada baki wurin cewa yaran nasu su karba nidai na bude motar na zauna sai lokacin na kalli Nabila nace anty ya aiki kuma ? Kallon juna sukayi kafin suyi magana Faiza tace cab aiki a yanzu ana dai nemane ai kaina na dan girgiza daga cikin motar nace ko zaku iya aiki a company nan garin. Yanzu kan naga fuskan su sosai don washewa sukayi lokaci guda zamu fadawa daddy suka fada nace OK idan kun shirya saiku hada takardun ku zan tura akarba. Daga haka Faiza ta shiga muka dauki hanyar gidan yaya Abubakar muka barsu a tsaye suna bin mu da kallon mamaki da al,ajabi. Aiki fa yarinyar na ta fada gwaggo hari ta fadi tana sauke ajiyan zuciya nima wanan zancen barazanan ai nake mamaki yanzu. Ku hada takardun naku koda yaya baisani ba idan yayi magana kuce dashi ninace ku bata muka karyan arzikin nata inda ya tsaya wanan kuma wani sabon sallo wai asan ita watace komai ? Tasan cewa daddy ba zai yarda da wanan zancen ba yasa ta fadi hakana amma ai zamuga karyan ta a lokacin muna kwanan gidan ya Abubakae kiran su ya shigo ta wayan gwaggo hari take fadin. Zancen aikin yaran nan a ina zasu sameki da takardan nasu ok za a aiko a karba ranan Monday din nan mai zuwa sai su fara fita . Mun gama wayan ban tsaya wani abuba na kira malam bello na fada mai komai yace an gama har inda nake son a jemin su koba komai nayi hakane mu rama alherin dan uwan su garemu. Suna ko gida ko awa daya ba akai ba aka sallama anzo karban takardun su da komai nasu ga opper din aikin guda uku an kawo masu har albashin da za a dunga biyan su a company sugar din dana filawa. Waya mommy ta dauka ta kira number gwaggo hari da imani ya kasheta tana dauka take fadin me kika samu kuma ko daki ban shiga ba fa yanzu na iso gidan. Bari ke dai yar uwa abin mamaki zai kasheni yau wallahi wai kin san yarinyar nan da gaske takeyi an kawowa yaran nan takardan aikin su har gida da albashi su da komai a wata. Ke don Allah ki daina wanan zancem zolayan ina Sahiba taga wanan daman mustaphan ta dake zaune ya dago jin an ambaci sunan sahiba . Mommy tace wallahi Allah zancen wasa ya wuce ga takardan a hannuna imani ya cikani nan zaune hari. Wai ya akayi wanan yar ta samu wanan daman hakane waya tsaya mata take wanan iskancin da take so hakane . Addah waiko kin san kila irin wanan baiwan na mahaifinta ta kwaso don in baki manta ba shima haka yake fa duk abinda ya dafa sai yayi albarka sosai wallahi. To yarshi shita gado a yanzu ke nan kome don kaina ni ya daure ga baki daya don wallahi, , , , sai taji ta kashe wayan ashe Anty Amarya ce da yaranta suka dawo a lokacin. Lafiya dai na ganku haka Anty Amarya ta tambaya saida ta nisa take fadin aiki yaran nan suka samu yau aiki kuma a ina aiki ya fito haka tsawon wanan lokacin da ake neman sa. Wallahi ikon Allah daine idan rabon ka ya rantse sai maishi Sahiba ce tazo gidan nan itace daga tambaya sai ga opper mun gani har gida na company tauraro. Sahiba fa a gidan nan tana ina ta sake tambaya tana dan waige waige sun tafi ai suna gidan modibbo dama shi suka zo gayarwa. Mama don Allah mu bita can mu ganta Fatima data dan fara tasawa yanzu ta fada tace kuje ku gani ko zaku samesu a can din. Yana da wuya su sameta don sauri sukeyi tace yau zasu tafi yola suyi sati daya a can jirgin karfe biyu zasu bi. Yaran suka mike da sauri suka fita har sun manta su karbi kudin Napep saida uwar ta kirasu ta basu kudin suka kama hanya suna Allah Allah su samenu a can.
Chapter 248 · 0% Book details