← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 337

Sashe 188

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

amsa da to kawai. Don yana ganin mahaufin shi ba zai taba wanan badalan ba shida ke kawowa mutum ayah kan komai da mutum zaiyi zai sa hannu ga wanan aika aikan haka amma zai gwada don ya tabbatar da gaskiyan lamarin. Sun dauki lokaci a tare dashi gaba dayan su ya fadawa kowan su matsalan shi wurin ita umma akan yan uwanta akai mata magana kan lalai tayi gagawan zuwa garesu tun lokaci bai kure mata ba sai Abdulhamid shi kuma an fada maicewa yan uwanshi sun masa abinda kada yayi arziki don suma basu tara ba sai don haka idan yana son kanshi da arziki ya daina nuwa ko matarshi yana da budi ko wasu abu suna shigo mashi a lokacin. Malam akace yayi gagawan komawa akwai mara lafiyan da suka zo daga nisa dake son taimakon shi duk da sun san ba zai iyaba amma ya nemo wani suka fada mai inda zai sameshi wai shine keda makarin ciwon maralafiyan dake jiran shi dain agida lokacin. AKarshe yayi masu alkawarin cewa zai fita bada dadewa ba in Allah ya yarda hutu kawai suke ba godiyan su a yanzu. Abu wasa wasa har suka kai goma da rabi a gidan mu ana abu guda zuwa lokacin an kira malam yakai sau biyar wai yazo yayi baki daga katsina. Haka dai sukaiwa umma sallama suka tafi kowan su cike da mamaki abubuwan daya wakana a wurin a mota malamin ke fadin lalai akwai manyan abubuwa masu karfin gaske akan yarinyat nan . Nisawa yayi daga inda yake tukin motan din shi tunanen zancen mahaufin shine ya tsaya mashi a rai da baisom ya gaskanta hakan kada ya zamo gaskiya da wani ido zai dubi wa yan nan mutanen idan hakan ya zamo gaskiya. Bayan ya sauke malam sunyi sallama ya kawo abinda zai bashi ya bashine ya tafi ya samu sunyi barci a falo ya rufe gidan ya tayar dasu haka ya kwana yana tunanen maganan aljanin har yana jan tsuki. Washegari bayan sallah asuba ya koma ya kwanta don barcin dake idon shi bai falka ba sai bayan tara yayi wanka yana shiryawane umma ta kirashi a waya a daidai lokacin nazifa zata shigo dakin taji yana fadin yaya jikin nata mama da sauki dai ko ? Bataji me aka fada ba hakan ya tsaya yana sauraren umma dake fada mai yanayin jikin nawa a lokacin yana fadin masha Allah zai shigo anjima idan ya fito. Sunyi sallama da umma din ya juya yaci gaba da shirin shi jin batayi magana ba yasa shima bai juyo gareta ba tunda bata iya gaidashi da kwana kullun yana mata fadan hakan. Wai wata mamace kake wanan wayan da ita tun jiya hakane ta tambayeshi tana mai tsureshi da idanu ya juyo a cikon mamaki yana kallon ta tare da tambayanta wata mamace ? Ina ruwan ki da sanin ko wata mace ko banda ikon waya da kowa sai kin san wanda nake waya dashi kiji da abinda ke gaban ki kafin ki shiga hurumin wani. Wani kallo tayi mai tana fadin bangane wanan na kamar ya naji da abinda ke gabana meye a gabana din ta sake tambayan shi. Wani kallo yayi mata tare da fadin ohh ke yanzu halinda yan uwanki ke ciki duk garin nan ya dauki zance ba abin damuwa bane a gareki ko ? Koda yake banyin mamaki don banga shitin hakan a gareki ba dama ko kadan yaja tsuki kuka ta fashe dashi tana fadib dama shike nan kuma da abin ya shafa kai min gorin hakan balle wani na waje. Wanan muma ke kika daukeshi a gori tunda suke asibitin nan kin dafa abinci kin kai masu ko ki sai wani abu akai masu daga tambayan dawa kake waya zaka fada min wanan maganan haka. Ina ruwan ki da wace nake waya kije duk abinda zuciyarki ya naki shine din ya fada ya dauki hular shi daya dora saman gado yakafa a kai tare da daukan agogon shi ya daura a hannun shi yana nufar hanyar fita daga dakin. Itama mikewa tayi tabi bayan shi tana fadin wallahi idan ma da watace kake waya in fada ma kayi kadan wallahi kace zaka kara min kishiya a yanzu. Jin hakan yasa ya tsaya a kofan yana kallonta a cikin mamaki yace haka zuciyar ki ya baki dama to haka din ne don kin canka a daidai ya fice daga gidan ga baki daya. Gidan su ya nufa har lokacin yana jin rashi a bace yake mai sun gaisa da mommy yake tambayanta mahaifin shi tace da safen nan yayi tafiya zuwa ghana daurin auren yar abokin shi. Ok kawai yace yayi shiru kafin ya kara fadin yaushe zai dawo ke nan tace zuwa jibi nasan don bukin baby ya kawo jiki yanzu ina zai tsaya can kuma. Hakane ya fada yana mikewa tare da fadin shi zai tafi sukai sallaman da mommy din ya kawo falon sune yaji muryan Faiza na fadin yaya na daina samun sahiba a waya kwanan nan. Wallahi naso tazo wurin bukin nan ko zan ganta inga yadda ta koma yanzu wallahi yaya naso ace zata zo din. Murmushi yayi daga inda yake tsaye yana fadin kinsan lagos akwai nisa da nan din kuma aiki takeyi kin sani yanzu. Kamar wani buki can ta damu mutane Allah yasa sahiba tazo idan sahiban tazo ma waya damu da zuwan ta kin damu mutane. Ban daiyi dake ba idan ma kowa bai damu da itaba nina damu da ita hakama nasan akwai wa yanda suka damu tazo don nan bayan ni. Ba wani buki bane bukin yar uwan naki Nabila kadafa ki manta baby yar uwar haihuwan kice look ban son inji ko inga wani abu ya fito daga wurin ku har a kare bukin nan ya nunasu da yatsa duka ukun cikin daure fuskanshi garesu. Ba zakaji ba brother insha Allahu hauwa ta fada daga inda take zaune cikon ko in kula da zancen da sukeyi mai tun shigowan shi. Mommy ne tafito daga dakin tana tambayan meya faru kowan su yayi shiru na dan lokaci saishi ne yace na fada masu kada naji wani tashin hankaki daga wurinsu kan lamarin bukin nan da za ayi. Mommy takai zaune tana fadin me zaikai bakin yaro a ciki iyaka dai ayi a watse lafiya shike nan bukin da ajirace ake damu mu tanka a sauke muna abinda akeson fadamuna dama me zai kaisu fitina nadai fada masu gaskiya ai. Nima abindana fada masu ke nan yanzu ya fada yana kallon mahaifiyar nasa kafin yai mata sallama ya nufi inda yake son zuwa kai tsaye tsohon office din ya nufa. Bayan ya nemu izzinin shiga an bashi don sanin koshi waye a wurin su din kwatancen da akai mashine yabi zuwa wurin kantan komai bai mantaba yadda aka fada har yakai daidai wurin files din . Idon shine ya sauka saman jan file din na kasa ya jawoshi yana kakabe kuran da takardan kedashi yaga an rubuta murder case da kwanan wata da komai a cikin sa.
Chapter 188 · 0% Book details