Sashe 118
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
kuwa don shi baida shayin kowa idan ya tashi tsula tsiyar shi shi yasa bai kula kowa kaf dangin shi saboda bahagon zuciyar shi da take mai baudai shiru shirun muguntane gareshi don ya tsotsina fulani a jinin shi. Abdulhamid ne ya shigo har falon mu bayan sallah isha,i suka gaisa da umma ina daki ina jin muryan shi tunda yayi sallama don kwana biyu ke nan muna haka da umma. Bawai bama magana ba a,a kawai dai tana fushi dani sama sama ne dana ga haka na rage zama a kusa da ita nafi zama a dakina idan ina gida. Ina kokarin shafa maganin nan da suka amaso baki amfani dashi ba duk dare ina shafawa kafin in kwanta barci tunda saboda ni aka karbo Sahiba fa naji Abdulhamid ya ambata don ya kamata ta koma aikin ta hakanavnaji muryan shi yana fadi yaci gaba da fadin. Don yau sun tambayeni ita nace ta samu lafiya sosai don naga tana shiga school. Eh to Sahibace yanzu Abdulhamid ta dauko wani sallo kuma bari dai a kira maka ita kuyi magana idan tana ra,ayin komawa nan din. Sam banji dadin jin kalamin umma ba datayi mai a kaina don dai itace zance ta dauki abindaya faru da zafi ai kan almustpha din da yazo dawata manufa garemu yanzu. Amar ya shigo ya fada min umma na kirana nace gani tafe bai dade da fita ba na fito saye da dogon rigan barci na daura zani a sama sai yar hula dana daure gashina na dunkule a ciki. Gaida shi nayi kafin ya ce dani gobe ki fara fita aikin ki Sahiba don aikin yana da muhinmanci a kanki sosai sai dai ba lalai bane ki gane hakan yanzu. Idan kinyi hakkuru nan gaba zakiji dadin hakan da alama ya fada yana kallona dan shiru nayi kafin nace bawai bana son komawa bane sai dai yanzu irin kallon da mutanen wajen sasuyi min shine kawai. Ba wanda zai kalleki dawata manufa yanzu don duk su san ke din ta dabance so suna tsoron yadda zasu tunkare ki ko su wani tsaya a gabab ki balle mu manyane muka san da abinda ya faru din. Ganin yadda umma tayi yasa nace shike nan zan shiriya gobe na fara fita idan Allah ya kaimu na kara da fadan nagode uncle yace shima ya gode. Ya juya zuwa part din su ya fita daga part din mu sai naji wani iri a raina yadda na bi umurnin shi kuma yaji dadin hakan ko ba komai na fahinci suna kokarin maida mu wasu na jikin su . Duk da banyi mamakin hakan ba don irin halarcin da umma tayi masu a cikin yan kwanaki da sanin mu dasu wanda hakan na hango zai zama muna alheri nan gaba watakila Lokacin mai tsawo na dauka ranan banyi barci ba koda na koma daki ina tunanen yadda zan kasance da abokan aikina idan naje aikin . Ba komai nake guduba sai sanin da nayi masu akan camfa abu yanzun zasu iya cewa da wani juju nake aiki ko wani kungiya nakeyi nake gane abinda mutum yake ciki. Washe garin da zan fita gun aikine muke magana da umma kan Almustapha wai na daina abinda nayi mashi ranan don bashi nayiwa hakan ba kamar ita na tozarta a gaban shi ai. Umma kin manta da warning din da yayi min kan kada na nuna nasan shi ko a wani wajen umma nafa fada maki yadda mukayi dashi lokacin. Yanzu ma din da wata manufa yake zuwa nan umma sai kiyi hankali kisan yadda zaku zauna dashi ki kama bakin ki dako mu waye a wurin daddy don abinda yazo ya sani ke nan ina fadin hakan na dauki jakkana tare da gyara hijabina nace sai na dawo umma. Shiru tayi ta bini da ido kawai har nakai kofa na murda zan bude naja na tsaya na juyo ina fadin shi din kin sani mai laifine da yansanda suke nema ruwa a jallo a cikin su harda yaya Abubakar ki kula umma kar zuwan shi ya jawo muna matsala muma a nan. Kofan na bude na fita ta sake bina da kallo don jikin ta ya mutu da abinda na fada kafin na fita amma idan har hakan gaskiyane dole tayi taka tsatsan a wurin zancen ta yanzu. Na isa wurin aiki tun a kofa da zan shiga na fara haduwa da wani babban ma,aikacin a wurin yayi wani irin ja baya da sauri ya kauce min tun a nan na fara kaduwa da kalubalin dazan fuskanta a wurin. Nayi signging kamar yadda kowa keyi ina kokarin zuwa inda nake tsaro naji muryan Abdulhamid a bayana yana fadin ba a nan zanyi aiki yanzu ba . Sun canza min wuri zan koma wurin accounter muyi aiki tare dasu a a ciki mamaki da kaduwa ne ya kamani lokaci daya najin hakan. Nasan wurin don haka na nufi wurin da suke na samu suna bakin aikin su muka gaisa suka nuna min wurin zamana kenan zan zauna zaman saka ido a komai har kudin dake shigowa da jama,an dake zirga zirga muna gani a wurin. Gaskiya na sani matsayina da komai baikai in kai wanan matakin da suka ban a yanzu ba a wurin don kosassun mutane da suka kwarai da aikin suke wanan wurun suna aiki. Nawa dai saka idone idan suna aikin da sauran abubuwa don haka mai min bayani yana dagawa daga wurin na sauke ajiyan zuciya tare da bin wurin da kallo. Gashi su kaf duk da manyane amma bai hana suyi wani haba haba dani ba mu biyu ne mata a wurin saidai dayan gaskiya ta girme min ga komai irin wayayyun matan nan ne na lagos masu ji da kansu do haka take zuba wani sallo da yauki a wurin. Aiki kan ranan anyi an tashi lafiya lokacin tashi yana yi na fito daga wuein bam saba da zama a cikin irin wanan sayin haka ba. Ina fitowa muka hade da Abdulhamid yake fadin ni yake jira nazo na ya kaini wurin motana dake aje a waje don yasan ban sanma kalar motan ba har lokacin. Dan yajayin fuskana na sauya kafin nace ya bari watarana zan ganta na san hakan amma yanzu muje kiga motar kawai kafin mu saka ranan da zaku fara koyon motan. Irin kallon da yan wajen ke min suna kus kus a kaina yasa na fara tsarguwa da hakan zan tafine na bashi amsa na fara tafiya don fita daga wanan wajen. Ya sake fadin zaki jira mu koma gida a tare don yanzu zan fito mu tafi daga nan sai kiga motan sai kuma ya dan juya ya kalli inda nake kallo yayi dan murmushi yana fadin. Yana juyawa ya nufi inda suke aiki ya dago jakkar aijin sa ya nufoni muka fita bamu bar wajen ba saida ya nuna min motan dake matsayin nawa yana rufe a wuri sabuwa dal da ita. Mun kama hanya duk jikina yayi sanyi ga tsarguwa da tunane da ya addabi zuciyana a lokacin ya dan kalleni yana fadin. Wanan sai ya faru dama suna zancene kan yaushe kikazo nan kika samesu har a kaiki wanan wurin aikin wasu kuma kan abinda ya farune suke shakkan ki a yanzu. Saidai dole sai kin kara taka tsatsan da kowa mu saman wanan wurin da oga yace a mayar dake yanzu don duk wanda ke wanan wurin sun san kan aikin su sun kuma karanta aikin tun farko keko haye kikayi. Don haka ki kula ki sa ido dama ina zargin don hakan oga yasa akaiki wanan wurin ki aiki dasu don abubuwan da ake masa a wanan wurin ba kadan bane wallahi. Zaki canza yanzu dole zaki zama big girl a cikin dubu komai har dabiun ki dole ya kara canzawa a yanzu don hakane ma ya karasa ya bayar da wanan motan. Godiya nayi mai bayan hakan ban samu bakin kara furta mashi komai ba har muka kai gida inda muka samu su umma a waje tare da matar shi suna muna sannu da dawowa. Na tsaya mun gaisa dasu kafin na shiga ciki itama matar muniya tashi tayi tabishi zuwa nasu part din suka bar umma tana hada kaya zata rufe shagon don yamma yayi a lokaci. Ranan ban samu sukuni ba don ni abin kamar a mafaki nake ganin shi lokacin wai yau nice a wanan matsayin anya kuwa zan iya kuwa.