Sashe 297
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
da taki sosai. Idan akwai abinda na tsana shine ya kira min kalman amaryata da yanzu yake yawan fada min daga bakin shi. Amarya for where idan nayi aure a yanzu na dauka kaine mutum na fatko da zakai min fada don barin uwata da dan uwana da basu cikin koshin lafiya nace nabi wani da sunan aure. Jin zancen yayi wani bambarakwai a kunnuwan shi kafin naji ya murmusa yana fadin a ina zaki bar mama din dama kina zaton zamu barsu a logos ne mu mutafi wani kasan daban ? Idan nayi hakan naci amanan zaman amanan da nayi da ogana da ace tun lokacin mutuwan shi nasan abinda ke faruwa daku wallahi Allah da ba zaku taba zaman kuncin rayuwa ko kwatankwamcin wanan da kukayi ba a rayuwan ku. Sahiba kin san zama na amana da mahaifin ki yayi dani a rayuwata kuwa banjin zan iya kara barin ku a wanan halin baku dawo kusa dani ba sai idan nayi hakan sanan hankalina zai dan fara kwanciya bisa ga irin abinda nake ji. Na rike wa yanda basu san ya akayi na samu dukiyana ba har kowa nasu balle ku da kune silar komai nawa a yanzu. Da ace kinsan yadda nakejin zafin Ali dcp a rayuwata da ko wanan zancen baki dauko ba a yanzu don komai daya faru daku shine silan hakan a gareku don shi ya boye min gaskiyan zancen ya rufeni. Enough that Ali dcp da kake kira he is my reletive shine uba a gareni shine dan uwan da yai silan komai nasani amma wanan sharia ne tsakanin shi da wanda suka zalunta. Bana son in rasa kowa a yanzu cikin su kamar yadda na rasa nawa mahaifin a baya shiyasa na roki Allah ya cire min duk wani zafi da takaicin su da nakeji na barsu da Allah zaifi. Ba zanso suma iyalinsu suji irin zafin da mukeji ba a zukatan mu don Allah baiyi zukata iri daya ba idan mu mun iya daukan wanan halin wani ba zai iya ba shi a zuciyan shi. Sai zumuncin yaci gaba da lalacewa har abada ba za a samu zaman lafiya a tsakanin mu dasu ba a rayuwa wanda ba zamuso mu zama silan hakan ba don bamu san me gobe zai haifa a garemu. Don haka bari ga Allah shine mafita suje idan don dukiyane da komai mukan mun yafe masu mun barsu da Allah final. Masha Allah ya ambata a cikin wani tsiga na ajiyan zuciya tare da fadin naji dadin jin wanan kalamin daga bakin ki a yanzu barin shine mafita . Ba zaku karbi komai nasu ba ninan na isheku na mayar maku da duk abinda zasu ba ku a rana daya don haka kwarai maganan nan naki abin dubawane sosai Sahiba na fahinci me hakan ke nufi a cikin zancen ki yanzu. Mun dauki lokaci kan dashi muna magana ta fahinta a wanan ranan kuma ya goya min baya ga hakan akan duk abinda na fada inda ya nuna min amincewan shi . Da zaiyi magana a sassauta sharian don kawai diyan su da matan su amma kafin hakan zaije da kanshi ya zauna dasu su san cewa nice na yarda da hakan a garesu. Don haka duk wanda keda wani abu a zuciyan shi a game damu ya fitar a zauna lafiya zaifi sauki ga mutum ba don tsoro kuma akai hakan ba. Nagode idan kayi muna hakan ka gyara komai tabbas sahiba ke yar halak ce na yarda don zuciyan ki daya da mahaifin ki. Da ace sun san da abinda yazo masu lokacin da suka kashe shi da basuyi hakan ba a lokacin don yazo masu da tarin alheri a rayuwa inda zai kafa kowan su ta yadda zurian su zata karfi a cikin duniya. Saidai kadara ta riga fata kwana sun kare a lokacin sune sanadin barin shi duniya a lokacin babu wani mahalukin da ya isa hana kaddara a kan bawa . Zan barki ki huta zan kara tunane mai zurfi akan komai na kuma gode da lokacin da kika bani a yau din nan har na kara fahintar yadda rayuwan ki yake a fili. Sai yanzu zance ya taja jin sautin murmushina a fili tsakanina dashi don abinda ya fada din nace kada kace hakan a kaina yanzu don baka san wacece sahiba ta gaskiya idan an tabani na sani. Shima din murmushi ya sauke tare da fadin hakane amma idan mun zauna a tare zan karasa sanin komai ina alfari da kasancewan ki daya daga cikin a halina koba komai nasan zan samawa gidana mace tagari wace tasan ya kamata ga kowa sai anjima ya kashe wayan kafin na furtawani kalman a garshi sai nabi wayan da kallo ina sauke ajiyan zuciya lokaci guda. Muryan umma ce ke tambaya dawa nake waya tsawon hakane ta shigo tun dazun ta samu ina waya haka Abubakar ne ? Bashi bane umma na bata amsa da mukhatar muke waya yanzu na fada mashi ya janye zancen kwace gidajensu da yai niyar yi kuma a bar wanan sharian a zauna lafiya. Sai gani nayi umma ta zauna tana fadin kinyi daidai yar albarka kamar kinsan da wanan zancen nake kwana a zuciyana nake kuma tashi dashi. Yadda su kudidi suka fada min halinda iyalansu suke ciki a yanzu don har yakai wanan yar da akai auren hadi da dan wurin gyade sun samu rabuwa a tsakanin su duk a kan wanan fitinan . Wai baby kike nufi umma itafa bamu bari yan uwan nata sunji bane a can don kada su tayar da hankalinsu kan zancen Shi kanshi Abubakar yanzu idan kin kula yana dari dari damu tun bayan da zancen mahaifin shi ya fito kowa yasan da hakan sam yanzu ya rage irin yadda yakeyi damu a da can. Idona na lumshe don nina dade da sanin hakan kuma nasan abinda yakeyiwa ke nan ashe itama umma ta gano hakan da yakeyi din. Ban tsaya mata dogon bayani ba don hakan kawai zamuyi mu zauna lafiya da yan uwan mahaifin mu har karshen rayuwan mu. Karba ko daurewa jan wani sabon fitinane a tsakanin mu dasu tunda Allah ya hore muna abin da zamu tallafawa rayuwan mu a duniya don yanzu ko shagon da umma ke zama cikin sa kawai zai shemu muci musha har mu ba wani. Kwana biyu tsakani na samu kira daga kaduna kan abinda ya faru inda yanzu aka gyara zancen kan cewa wai ai an gano gaskiya ba laifin su bane. Amma kowa a cikin dangi yasani cewa su din daine sukayi kisan kuma suka wawashe mashi arzikin shi suka wofintar da iyalanshi da komai nasa daya bari. A can wurin mukhatar kuma yana samun kalubali sosai gurin matarshi data kafe kan cewa ita sam bata yarda da wanan auren daya sakeyi ba a yanzu.