Sashe 75
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
kara fada haka da kowa koso nake plain din mu ya rushe ne idan ina hakan oda nace na wuce abinna . Duk da naga yaran sun manta da hakan ban yarda na shiga zancen su mun dawo gida lafiya bayan mun taso zuwa gida suke nuna min assignment din da nayi taci su tana murna dayan tace nima na koya mata na ta yau nayi banza da ita. Haka yaran suka zo suka tare muna a dakin mu dole umma tayi min tsawa na zauna na koyawa yaran suka fice can kuma suka sake dawowa sai ga uwar na kiran su sun daje still suka dawo kuma sai dare sosai suka bar part din nice na rakasu zuwa part din mu. Haka dai zaman namu a gidan daddy yake tafiya kadaram kada ham wani abu da nayi notis a ranan girkin anty shine duk naci abincin ta haka zan zauna na amaye abincin tas a cikina sannan zan ji dama a karshe kuma kaina ne zai ta min ciwo sosai sai can ya lafa min. Ranan gashi ina ji yunwa sosai tundare har safe banci komai har sha biyun rana mikewa nayi zuwa kitchen din su na samu mai aiki da ita suna girki. Una weldone nace dasu tare dan raba ido ga kayan abincin dake kitchen din baga ko mai ba nace i wan cook indomie. Juyawa tayi ta kalli hannu na tana fadin whare is d indomie nace i tink say you have it here ta juya kawai ta kyaleni a wurin taci gaba da aikin ta a wurin suka fita batuna. Na juya na fita a hasale ban tsaya ba sai part din mu na dauko kudi na dauki dan gyalena na dora a kafada na dagani sai dan riga karami ya dan wuce gwiwana na fice daga gidan. Wani shago danake hangowa idan zamu tafi school a unguwan na taka na tafi na sayo duk wani abinda nake so na juyo zuwa gida da kaya a blue leda. Ban kallon kowa sai tafiyana nake a cikin dan rigana sabar sabar dani motar data wuceni ne ta dan dawo baya ta tsaya a daidai inda nake na zo na wuce ta ko kallon gefen ta banyi ba. Najji anyi horn hakan ma baisa na juyo na kalleshi mai shi ba sahiba naji an ambata na juyo da sauri cikin mamakin jin an anbaci suna a nan din. Mukai ido biyu da ya Abubakar a cikin motan yana zaune fuska a murde yake fadin from where are you ? Nace i go by indomie that shop what ya fada har yana dan kallon gefe idan babu wanda yaji abinda na fada a lokaci. Oya inter ya fada yana bude motan gaban shi na dan daga kai na kalli get din gidan da baida nisa damu lokacin. Nace No i can trake, no far from here, yace a cikin tsawa common inter d car jare jin hakan na fada motan daya bude da sauri. Ina shiga ya fara fada yana fadin babu abincine a gidan nace akwai saidai duk ranan da anty din nan tayi girki naci sai nayi ta mai kaina ya dinga min ciwo sosai tun jiya banci abinci ba yunwa nake ji . Kuma nayiwa anty magana a kitchen idan akwai indomie ta ban na dafa ta kyale ni shine na dauki kudi na sayo. Yayi shiru kafin yace na fadawa hjy nace ban fada ba don ban son na dame su na fada ina kawar da kaina gefe shima shiru yayi har muka shiga get din gidan. Yana bude motar yace dani wait for me there naja na tsaya wuri daya har ya fito daga motan bayan ya rufe ya nufi hanyar shiga gidan yana fadin follow me nabi bayan shi da sauri. Part din mahaifiyar shi ya nufa suna falon ta ita da yaranta da yanzu a nan suke zama muka shigo tare dashi yayi sallama suka karba mai. Ya juyo yana fadin na aje kayan dana sayo a gaban hjy na dan yi darrr don yunwan da nakeji a lokaci. Haka dai na aje din a gaban ta ta kalli kayan da mamaki ya nuna da hannu yana fadi a cikin hausa ga kayan nan yazu na hadu da ita wai ta sayo a waje zataci yunwa take ji. Amma wanan yarinyar da tonon asiri kike wallahi hjy ta fada tana harara na ya tare da fadin a, a mommy nasan halin yarinyar nan tace taje kitchen ta fada suka kyaleta . Yaci gaba da fadin ta fada min wani zance da ya kamata a zauna ai nazarin sa don idan taci abincin anty wai amai takeyi kamar zata mutu wanan maganan a duba mata ne. Aduba meye ta fada rai bace yarinyar nan bata son a zauna lafiya a gidan nan nake gani zan zauna da uwarta muyi magana tunkan ta hada wani fitina kan hakan. A a mommy wallahi nima kusan kullun naci saina amayar dashi saina daina ci dole Fa,iza ta fada daga gefen su. A dai duba din tunda haka ne kada azo rashin kulla da hakan ya haifar da wani matsala nan gaba. Jeka modibbo nace zan duba wanan zance naga ya da za,ayi ya juya wurin Nabila yace bata wani abu a nan idan akwai taci banda bread da butter ba wani abu a nan yanzu ok kawai ya fada ya fita daga dakin. Sai kuma ya dawo yana fadin Fa,iza dauko gyale kizo da ita ku sameni a mota yasa kai ya fita ba abinda uwar zata ce sai kallon juna da sukayi da diyan ta kawai nikan na duka zan kwashi kayana in tafi. Fa,izan tace dani in biyo ta mu tafi sai hjy din tace dani hakan nan zan fita ta nunani da hannu tana bata rai na danyi kasa da idanuna fa,iza din ta fito daga daki tana fadin mu tafi nabi bayan ta tsomai tsomai dani muka bar part din ban fita ba saida nakai kayan dakin mu na aje da sauri na biyo bayan su. Wani gidan abinci ya kaimu akai muna take away har leda biyar sai kayan drinks daya saya muna muka juyo zuwa gida. Muna sauka ya mika min ledan abinci biyu na drinks din daya na duka ina godiya na shige part din mu da sauri sai dai kash yuwa yacini a lokacin ban iya cin abinci ba Allah ya taimakeni akwai fura mai sanyi nasha sai barci. Bayan sallah magariba muna zaune su umma suna cin abincin da na shigo masu dashi don ban boyewa umma komai ba don ban iya karya ba a rayuwana. Sai ga mommy tayi sallama dakin ta shigo a falo ta samemu zaune muka shiga gaida ita ta zauna tare da kallon wurin da aka aje muna abinci bamu taba shi ba tace. Dazun yar nan ta tafi sayo abu suka hade da yayan ta take fada min wani magana daya ban mamaki wai idan taci girkin hjy Karima sai tayi ta haraswa . Wallahi hjy nima hakan yana ban mamaki don ranan har marinta nayi a dakin nan na tursasa ta sai da taci loma biyu saida ta kwata ciwo tun wanan ranan na kyaleta ai da abincin ko kamahin shi taji yanzu matsalane hakan . Ikon Allah wanan wani irin matsalane haka ya samu yarinyar nan kuma ta dan kura min ido na dan lokaci