Sashe 175
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
a lokacin. Wallahi ba komai bane sai Sahiba dana tuna ranan da mommy ta aikemu wurin gwaggo muka samu yaya a gida mun fito muna gulman shi ashe yana falo a kwance yana waya. Ya jiku Hauwa ta tambaya yajimu mana tana surfa mai zagi da katon banza a saman jikon maman shi ya kwanta gashi da wani geme kamar sai gashi gaban mu. Dariya suka kwashe dashi dukkan su lokaci guda me yayi mata ko bai nuna yajiku ba ai kin san halin Sahiba mana anty karasa tayi duk da yana jinta kuwa. Wanan yatinyar ai yar iskace ta kwarai Allah yaga abinda ya gani ya barta a cikin tsiya da suke ciki yar iska kawai. Wallahi ni yarinyar bana son zancen ta kodan ta faye zama fayau ne duk inda kaje da ita sai ansan da tana wurin zakaji wai mutane fa sai su dinga tambayan ka diyar waye ita din shiyasa ban son fita da ita wallahi. Wani kallo Faiza ke mata daga inda take zaune kafin tace kai kai mutum ya dinga aibanta dan uwan shi haka don kawai tafiki tsari. Waye tafi tsari din Nabila ta tambaya har tana dagowa don bacin rai tana fadin mommy wallahi kiwa yarinyar nan magana kona fafasa mata baki yanzu a wurin nan. Kaji min yar iska ni ta ina Sahiba yar kabilu waccema ba a san asalinsu ba sun zo su danganta da uban wasu har zaki wanice dani tafini. Sahiba din ce bata da asali uwar ta dago kai tana tambayanta a cikin mamaki sai ta bata rai kafin tace mommy to waya san ubanta din. Ni mommy ta fada rai bace duk suka kallo inda take a cikin mamaki taci gaba da fadin na karaji kin dangata yar nan da mugun suna zan bata maki rai a gidan nan wallahi. Wai mommy dama kin san mahaifin su ashe shine Anty Nabila take fadin wai basu da asali kila daddy suke kokarin lakawa ita yasa aka koresu. Salati mommy ta fara yi tana tafa hannayen ta a wuri daya kafin tace yanzu sherin da kuke kokarin kulawa mahaifin ku ke nan akan yaran nan dama ? Da sauri Nabila tace a, a mommy nima ji nayi ana fada wallahi cikin dangi yasa nazo ranan ina fada masu abinda naji din amma bani na kawo zancen ba. Kasa magana tayi a lokacin din bata san me zata fada ba ga yaran nata sai mikewa tayi ta shiga dakin nata ta barsu a wurin zaune. Nabila ta kalli faiza cikin dan kwantar da murya ta kada mommy tajisu tana fadin na fi karfin sahiba kema kin sani duk kika kara hadani da yar matsiyata din nan mai kama da yar wanke wanke wallahi saina balbala ki a gidan nan ranan don ta dan sayo maku gwajon lagos ta aiko maku kike wani rawan jiki akansu haka. Nayi shirina ranan monday na fita wurin aiki tunda na tsayar da motana udanuwa suka dawo akaina na mutanen dake ma,aikatan . Sam ban damu da irin kallon da suke min ba don inda sabo a yanzu na saba hakan a wurin su. Ban yarda na shiga office din da muka saba zama don yin aikin muba aranan don haka na zaro wayana na fada masu zamuyi aikin yau a cikin office din babban accounter din ma aikatane. Don haka nasan a nan zan samesu na fito yadda na saba ina saye da wandon jeans na yayi sai yar riga fara mai dan ado daga gaban riga daya tsaya min iya gwiwana kaina yana saye da hula baki kalan wandon dake jikina zakace tare akayi su. Na wuce naji wasu na fadin kai ga mace dai kan har mace amma kuma kafira bata sallah ina wayana na wuce su ina mamakin dan adam da daukarwa kanshi fitina yake. A daidai shiga na hadu da oga bala da sauri zai fito yana waya yana ganina yadan razana ya daburce don gani din da yayi a bazata. Gaisawa ya tsaya mukayi dashi sama sama kafin don ban tsaya ba ina tafiya muka gaisa din da dan murmushi gefe a fuskana na wuce zuwa ciki. Suna zaune ina tsaye ina karanto masu abinda nayi nazari a file din farko dana bude tare da bayanin abubuwan da na gano a cikin sa. Kafin na dauko computer na daga inda nake tsaye din ina tura bayanan da muka gani acikin sa aka turo kofan office din. Oga bala ne tare da manager suka shigo a dan rude duk muka dago muna kallon su a cikin mamaki kallo daya nayi masu na mayar da hankalina wurin computer da nake tura sako ciki. Bayani yakeyi a rude yana fadin sunzo don Allah akwai wani files a ciki da basu dabganci wanan zaman naku ba zamu dubasu cikin nan. Ba tare dana fago kaiba na fadi a cikin yarbanci su basu su duba din naci gaba da aikin da nakeyi ban dago kaina ba. Ban dago kai ba still ganin suna damuna nace dasu wanan kuke nema ku dauka ai mun gama dashi zaku iya tafiya dashi yanzu. Lokaci daya suka dago kai suna kallona kafin su juya su kalli junan su kuma suna mamakin hakan. Manager ne dan fara ja baya kafin ya juya ya fita daga office din oga bala yabi bayan shi ba tare da sun tsaya amsan file din ba don sun san komai yagama tonuwa a cikin shi ke nan. Kallon su nayi ina fadin zamu shiga kano gobe idan Allah ya kaimu da safe Adnan zamu tafiya da motar kane dana Abdul zuwa can don haka ku sha mai da wuri da zaikaimu ya dawo damu a yau din nan. Sai mun hadu goben na fada daga haka na fita don ban iya tsayawa hira a rayuwana har yanzu sabo da rayuwan ujula dana tashi a cikin sa har banda lokacin da zan tsaya yin dogon hira da mutane. Basai mun tambaya ba don da ganin wurin hankali a tashe yake nikan ban tsaya ba wurin motana na hara direct na bude zan shiga. Da sauri Bello ya karaso inda nake ya tsayar dani yana fadin wallahi madam akwai matsala don suna son su hada kan mutanem wajem nan ai muna bore a koremu. Nothing will happen insha Allah na fada na bode motana na aje kayan dake hannuna tare da juyowa gareshi ina masa godiya. Na shiga na tayar da motar na halba aguje nabar haraban wajen suma suka shiga muka fice zuwa inda masaukin mu yake. Haka yasa suka dawo da hankalin su wurina har na bace kowa na fadin albarkacin bakin shi a kan mu yarinya yar firit kara sai bakin wayau da fitinan tsiya haka. Wasu suce da ganin wanan yar ta karantu sosai tayi ilimi tun tana karama irin tashin turai din nam ne kana ganin ta kasan ba tashin kasan nan bane ita.