Sashe 288
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
kina daukan mu kamar mahaifin ki kin san darajan mu a wuyan ki shiyasa har muka yanke wanan shawaran haka ai. Tunda kin san dai ba zamu taba cutar dake ba kan hakan, yayi mamaki kwarai lokacin dana daga mai hannu a cikin wani irin yanayi ina . Tare da fadin stop that nonsense talk uncle hamza da ace kai ubanane na gaskiya baza ka taba daura min aure da wanda kowa bai sani ba sai cikin dan lokaci. Haka ba zaka taba aurawa diyar cikin kaba aure da bata sani ba yadda kai min din nan a yanzu Sahiba umma ta fada da karfi daga ida take tana matsowa gareni. Ko gezau banyi ba na dago kai na kalli umma din da a yanzu itama komai ina ji zan iyayi kan wanan abinda sukai min din. No kyaleta mairo na fahinci irin zafin da takeji a zuciyar ta a yanzu idan an matsa mata komai zata iyayi baffah Abdullahi ya fada a tausashe daga inda yake tsaye yana kallon abinda ke faruwa. Nima abinda na fahinta ke nan ko kadan banji zafin zancen taba gareni baffah hamza ya fada daga inda yake ya fara takowa zuwa bakin gadon da nake zaune. Ya kai zaune a kusa dani ya dafa kafadana yana fadin yaushe kika taba ganin uba zai iya cutawa yarshi sahiba ? Idan kinyi tunane irin wanan baki kyauta ma son da kaunan da muke maki ba a yanzu mun barku kuda mahaifiyan ku a baya lokacin da bai dace ace mun barku ba. Yanzu kuma kun dawo garemu muna fatan mu baku soyayyan da mahaifi ya dace yabawa yarshi ko irin kauna na uba da yarshi . Da ace mukhatar mutumin banza ne ki sani mune mutane na farko da zamuki yarda dashi koda kuwa kece kika kawo muna shi a matsayin zabinki gareki idan bai muna ba ba zamu taba yarda ki aure shi ba. Saidai ki sani cewa bamu maki wanan zabin a banza ba sahiba munyi hakane don mu nunawa duniya cewa ke din yar albarkace mai bin umurnin iyayye . Duk da wayewan da mutane suke ganin kinyi a yanzu munyine mu nuna masu cewa wayen wanki da rashin tashin ki a cikin da bakiyi ba. Bai hana kiwa na gaban ki biyayya yadda ya dace ba duk ko da irin abinda wasu yan uwan mu suka aikata ga mahaifin ki bai hana kiga girman mu a idon ki. Kwarai kuwa sahiba mutane da yawa suna dauka yanzu baki kallon mu a iyayyen ki sun dauka kin watsar damu kamar yadda muka watsar dake a baya. Saidai har gobe ba duka aka taru aka zama daya ba dole a cikin zuria akwai na gari akwai baragurbin don haka yanzu damu dake zamu taru mu kara dawo martaban gidan mu dana iyayyen mu da wasun mu suka zubar a baya a idon duniya. Shiyasa da tsohuwan nan tazo muna da bukatan son hada iri a tsakanin ku dasu mu kuma mukaji nauyin ta nacewa mu nuna mata bamu yarda da hakan ba tunda duk abinda sukeyi suna yinshine don darajan mahaifin ki a idon su. Sai mukaga idan bamuyi hakan ba wa zamu basu kamar yadda suka bukata tunda shi ammar dana mijine ba zancen aure a gareshi yanzu. Kiyi hakkuri idan muyi maki ba daidai ba sahiba a madadina dana yan uwana harda mahaifiyan ki muna neman gafara akan hakan da mukai maki. Jin maganan shi ta karshe yasa na sake wani irin kuka mai gumji wanda duk ke wurin saida yafitar da hawayen tausayi yadda nake fadin how can stay with this man ? Ba tare da nasan komai daya shafi rayuwan shi ba ba wani nawa wanda yasanshi don ko ya Abubakar ina ganin bai sanshi ba haka kuma sai a yanzune kuka sanshi. Wanan karon baffah Abdullahine yai magana yana fadin indan wanan ne daughter ki kwatar da hankakinki . Bamu daura maki aure da mukhutar ba saida mukai bincike muma mai tsanani a gareshi muka gano shi mutumin arzikine mai mutunci da kima a idon jama, a. Tun bamu san zamu hadu dashi ba ta sanadin ku muka san waye mukhatar a bakin jama, a don haka ba wani abu na muni da aka sanshi dashi gaskiya na zahiri. Ya kare da fadin kodan yadda mahaifiyar shi ta nuna maki kauna da taki mahaifiyar da tayi na,am da wanan hadin kiyi hakkuri ki daure ki zauna dashi. Kodan ki fitar damu kunyan yan uwan mu da suke shirin muna dariya a kanki sahiba ki daure ki zauna da wanan mutumin insha Allahu zakiyi alfahari dake da kowa naki kan wanan auren nan gaba. Umma ta dawo ta saitin kaina tana fadi a cikin yarbacin in rufa mata asiri kada wanan zancen kukan da nakeyi ya fita har zancen ya koma kunnen su taji kunyar hakan tunda yan uwan ubana sunyi bugun gaba dani a yadda al,adansu yake. Kuma basu bayar dani a wurin banza ba insha Allahu zanyi alfahari da wanan auren don Allah kada in yarda in nuna masu ban yarda da irin tsarinsu ba na fulani. Haka dai tayi ta maganganu a cikin harshen yarbanci da baji sukeyi ba har dai na dan rage sautin kukan da nakeyi a lokacin . Dukkan su sunyi shiru a lokacin da alaman rayukan su baida dadi kamar yadda nawa yake a ciki faiza da fatima kuma sun rakube a gefe daya a cikin damu suna kallon abindake wakana a wurin har kowa ya manta da suna wajen ma lokacin. Maganganun su mama kudidi yasa jin zuciyana ya dan sassauta min a lokacin har na dago ina kokatin sauka daga gadon inda nake kwance. Kowa ya bini da ido ana kallon kome zanyi a lokacin gyalena dake saman gado na dauka na yafa kafin na taka zuwa inda kafan baffah hamza yake na tsunguna tare da fadin uncle ka yafe min insha Allahu zan yi maku biyayya kamar yadda al,adan ku yake na gida.