← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 273 OF 337

Sashe 273

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

sun fada. Daddy idan baka fada muna a yanzu mun san komai ba zaiyi wahala mu iya kwatoka a hannun wanan mutumin a yanzu don yana da burin kargameka a gidan maza. Nasan yana da gurin yin hakan don da gaske yazi lauyoyi a can sun fada muna duk wani tuhuma da ake muna wanda mamu nan mun manta da anyi hakan . Daddy ya gyara zama yana fadin watau mudibbo na dade da sanin wanan lokacin yana tafe son zuciyana yana bani cewa da akwai wani wanda yasan komai na Sambo bayan ni. Don hakane na zauna na tsara komai amma kuma kasan dukiya da shiga rai da ace nayi dubara lokacin da kakawo min iyalin sambo da farko na mika masu dukiyan su a hannun su da duk haka bai taso a yanzu ba. Hakane daddy modibbo din ya fada tare da fadin ko zan iya ganin takardan a yanzu inda ka rubuta komai din don asan inda za a fito masu. Dan shiru daddy yayi kafin yace da dan nasa inaga basai an duba wani takarda ba nima a yanzu nafi bukatan na dakawa mutanen kayan su a hannun su ko hankalina zai kwanta ga komai. Daddy idan kayi hakan yayi kyau sosai ga al,amarin amma kuma anya duniya zata yarda da mika masu komai haka tsakanin ka dasu kuwa ? Bandamu da zancen mutane akaina ba yanzu abinda nayi niyar aikatawa shi zan aikata akaina dasu final. Kai ya gyada cikin gamsuwa da abinda mahaifin nasa ya fada lafin yaje bakin shi yayi shiru lokaci guda yana nazari kalaman mahaifin nasa. Kafin ya daga kanshi dake duke yana fadin daddy zan koma Allah yasa mu dace mahaifin nasa ya busar da iska yana fadin amin zan kokarta naga hakan ya faru. Part din mahaifiyar shi ya nuna bayan sun gaisa da kanin shi da a yanzu sauyin rayuwa ya samesu na dan aikin da suka samu suna biyawa kansu wasu bukatu nasu da ba sai sun roka ba an ja masu rai a yanzu. Hankalin shi ya mayar gun mahaifiyar shi ya kara gaida ita a natse kafin ta jefo mashi tambaya kaje kakai masu abincin kamar yadda mukayi dakai zaka kai ? Na dai tura ankai masu don ni banje da kaina ba kamar yadda mukayi mommy don ko naje gidan da kaina ba lalai bane in samu shiga ciki mu gana dasu. Kana ganin hakan yayi maka ke nan kowa ya ganka yasan abinda ya kawo ka ai donme zaka damu sa zancen wasu can a kan ka ? Shiru yayi babu amsa a lokacin don yasan ba zai iya shiga gidan ba a yanzu gaskiya saboda gidan babbam gidane mai tarin mutane da yawa a cikinsa. Don haka ba zai shiga ya dinga faman gaisawa da tarin matan da zai sama a tsakar gidan ba gungu gungu ya dinga gaidasu. Hauwa ce ta taimaka mashi ta jefo mai tambaya akan aikin ta ya tsaya bata amsa har hankalin mahafiyar nasu ya dauke ta shiga daki ya samu ya sulale daga gidan ya nufi nasa gidan kai tsaye. Zaune muke da umma da muniya har matan kanin mijinta da suke zaune dasu a yanzu a wajen gidan mu muna hira mukaga dawowan mijita daga wurin aiki. Itace ta tashi ta nufi wurin shi sai gasu sun samemu a tare dashi zuwa inda muke ya gaida umma dagida dake mai sannu da zuwa. Sun dan taba hira kafin ya juyo kaina yana fadin eh sahiba na your eyes be dis i no see u all dis days. Na dan sake murmushi ina gyara zama tare da fadin i dey wooo bani dai son fitowa wajene koda yaushe na bashi amsa a takaice kafin na dukar da kaina ga wayana lokacin. Zanso ganin ki anjima idan na dawo daga magariba ya fada sai lokacin na kara dagowa ina fadin OK. Basu dade da shiga part din su ba namike na shige namu part din yan aikace aikacen gida nayi a lokacin na dora muna girkin abinda zamuci. Nagama tsab dama ga al,adan bayerabe kafin ya dora girki ya tanadi duk wani abinda yake bukata ga abinda za a girka din muma zama a cikin su haka muka sabadayi. Shiyasa da mun dora girki yan lokaci kadan sai kaga an gama shi a cikin lokaci haka kuma abincin dai bawai wani dahuwa ake bari yayi sosai ba don haka suke girkin su dama. Bayan isha,i saigashi yayi sallama falon ya shigo suna gaisawa da umma na fito muka gaisa yake cewa dani dama ba wani abu bane don Allah tambaya yake son yai min. Zagayowa nayi na samu kujara na zauna ina fuskantar shi yace ya dauka a matsayin da muke yanzu dashi mun zama yan uwa mu dashi. Saidai ashe abin ba haka yake ba mu a wurin mu don inda na daukeshi kamar yaddashi ya daukemu ba zan aje aikina ba tare dana fada masa dalilina ba nayim hakan. No kada ka damu da wanan ni a wurina wanan ba wani abu bane da zan dinga bin mutane ina fada masu dalilina shiyasa ban fadawa kowa cewa ga dalilina ba ai. Amma ai ko bamu fada ba ansan mun daukeka a matsayin dan uwa yanzu don mun wuce makwabtaka damu dakai. Wanan amsan da kika ban yanzu Sahiba bashi zai sa na gamsu ba har sai naji dalilin kina barin aiki din da kikayi. Jin hakan yasa na dan lumshe idanuwana na dan lokaci kafin na bude ina fadin brother matsalan mahaifiyan oga shaabance ta kira waya tana fada min wasu maganganu da har zuciyana ta kasa daurewa nakai ga bata amsa tare da alkawarin zan bar aiki da danta kamar yadda ta bukata har abada din.
Chapter 273 · 0% Book details