Sashe 256
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zubur ya mike tsaya lokaci guda ya fara zagaye dakin shi kadai yana tunanem inda yasan wanan sunan ko fuskan wanda yake kallo a screen din laptop din tsawon awa daya da rabi. Wani irin abu yaji a zuciyan shi lokaci daya yaja ya tsaya yana sauke numfashi a lokaci guda ya dan furzo iska mai zafi daga bakin shi kana yakai hannun shi akanshi ya shafo zuwa fuskan shi. MUKHATAR USMAN MARWA fittacen dan kasuwan nan mai harka da ma,adanai na kasa kasa matashin da yai saurin fice a wanan harkan lokaci guda kuma yana matsayin basarake daya fito daga nahiyar gabas mai fada aji akasa saboda sun kawowa kasa cigaba sosai ake damawa dasu sosai. Mukhatar dai kowa yasan ba mutum bane mai lokacin kanshi balle na iyalan shi ko yan uwa mutum ne wanda a yanzu ganin sa ma aikine. Yayiwa harkan shigan wuri harkan kuma ta karbeshi yashige cikin turawa ya saje dasu ana gwagwalmayan rayuwa tun tasowan shi. But why ya tsoma kanshi a cikin wanan harkan a yanzu yake tambayan kanshi saidai a halin yanzu ba amsa a gareshi. A gurguje ya shiga bathroom ya watsa ruwa a jikin shi ya fito ya shirya yana kokarin daura belt din shi a kwankwason shi ta turo kofan da kuka wiwi . Hakan yasa ya juyo yana kallon ta duk da bata bude baki tayi magana ba yasan kukan ta bai rasa basaba da abinda ke faruwa a gidajen su a yanzu. Juyowa yayi a fusace yana fadin ke meye hakan meye zaki shigo min dagi a wanan yanayin na tashin hankali haka kuma ? Haba modibbo kaji wai a kan wanan case din yarinyar nan wai anje gida an fitar dasu mama fitarwan wullakaci gaba dayan su gidan, suna titi a watse da safen nan fa suka dira masu a gida sukai masu wanan wullakacin. Uhummm ya fada ya juya yana kara saka wandon jikin shi da kyau ita kuma tayi tsaye sororo tana binshi da kallo cike da takaicin ganin rashin damuwan da bai nuna ba ga abinda ta fada mai din. Wani irin kuka mai sautin tausayi ta sake lokaci guda har ya kare shirin shi yana jinta saida ya fesa turare bayan ya gama tsab ya juyo yana ce mata. Yanzu kukan nan naki shi zai saka wani abu ko kuma kijawa kanki wani matsala nima kuma ki tayar min da nawa hankalin ? Dole inyi kuka saboda nina nasan zafin da radadin hakan dana ke ji don kai naga abin bai shafeka ba ka nuna min yanzu. Kome zaki fada ki fada yanzu don kina da daman fadan hakan saidai kada ki manta da cewa nima abin ya shafeni ai ko kin manta da hakan ne. To ba laifina ya kamata yanzu ki gani kiga laifin iyayyen mu da sukabi son zuciya suka aikatawa bayin Allah irin haka a baya yanzu lokacin namu fuskantar tashjn hankalin ne yayi. Da ace basu bi son zuciyarsu da kuma hassada ga dan uwan sy ba da yanzu kowa na zaune kalau a cikin salama amma yanzu ba yadda muka iya don zakanya ta girma ko tsakiyan daji ni kaina abin a yanzu na kara gaskanta sakaiyane kawai ke bin iyayyen mu na abinda suka aikatawa dan uwan su a baya. Yana kai nan ta dago kai da sauri tana mai wani irun kallo kamar zata cinyeshi danye ya gyada mata kai kawai ya figi suit din shi dake saman gadon daya gama feshewa ya fita nan ya barta zaune tana mai matsakancin kuka cikin tashin hankali. Gidan su ya nufa don yana son ganin daddy a wanan lokacin kan binciken dayayi din saidai yayi rashin sa,a daddy din baya gida a wanan lokacin. Yana tsaye yana mamakin inda mahaifin nasu yajene don yasan baya sakkon fita irin wanan lokacin haka sai idan wani abu mai muhinmaci sosai ya taso gareshi. Bai kaiga karasa isa wurin motar nasa ba wasu mutane suka iso ya sheda su dan yasan wasu daga cikin su kusan irin aikin su daya saidai ba a ma,aikata daya suke aikiba don kowa da nasa bangaren wurin aikin ne. Nan dai suka sameshi suka gaisa dashi suke fada mai sunzo neman maigidan nan ne don basu dauka daddy shine mahaifin shi ba a zaton su wani aikine ya kawoshi shima wurin daddy din . Yake cewa dasu shima ai wurin shi yazo saidai baya gida OK babban nasu ya fada zamu dawo munzo ne mu tafi dashi dama don ya amsa muna wasu tambayoyi da muke so daga gareshi . Basu tsaya mashi bayani ba suka juya nan suka barshi a tsaye cikin jimame a lokacin hjy karima ta fito zata fita unguwa zuwa gidan yarta don haka a gabanta aka fadi komai. Itama dai hankalinta ne ya tashi sosai a lokacin jin abinda jami,an suka fada take fadin wanan tashin hankali haka dame yai kama ? Haka jiya bamuyi barci da wuri ba a gidan nan don su hamza da yara su ya Nuhu sun dade a gidan nan tare dashi wanan abin gaskiya baidai yi dadi ba wallahi . Mutum yanzu in kai masa rana sai yayima dare in ba shi ba wai yau Sahibace da kanta takewa Alh haka a garin nan. Murmushi yayi yakai bakin motarshi ya jingina jikin shi da motan yace me Sahiban tayi kuma anty da ake mata wanan zargin haka yanzu. Modibbo kai yanzu bakaga rashin kunyar yarinyar nan ba haka meye Alh bai mata ba zaman su garin nan don Allah ? Anty idan yai mata ai yayiwa kanshine don wata kila da wani manufa yai haka din garesu mutanen da dukiyan su yana hannun daddy da Allah kadai yasan adadin abinda aka bar masu sai shi wanda keda dukiyar nashi kuma baya raye a yanzu. Tsaye tayi cikin yanayin mamaki da rudewa yadda modibbo da bakin shi yake fadin ha tana kallon yadda yake fadin magana haka ranshi a bace. Abinda bata taba ganin ya faru dashi ba yau ta gani a fuskan shi lokaci guda ya rikede ya koma wani kala dashi lokaci guda zaka fahinci tsananin tashin hankali ne yake ciki a lokacin. Nan dai yayi mata bayanin komai yadda zata gane sai ga hjy na komawa bayan mota takai har tana kai ga jingina jikinta a motan . Lailai muna cikin halin tsaka mai wuya a yanzu don nima wanan fita da zuwa zanyi can gidan mijin baby ance duk yan uwan nasa suna nan gidan a yanzu. Zaki iya zuwa ki duba muna halin da take ciki in yaso sai a san abinda za ayi nan gaba don ba zasu zauna masu a gida haka gata gasu ba. Har hjy ta fita daga gidan da motar ta yana tsaye yana waya da wani abokin shi daya bugo mashi wayan a lokacin. Yana cire wayan an kunnen shi yana kokarin turawa aljihu motan daddy ya danno cikin get din gidan suna tafe tare dasu baffa Abdullahi da baffah hamza da wasu mutum biyu daga cikin yan uwan su. Yana tsaye har suka gama fitowa daga motan ya karasa wurin su yana gaidasu a cikin ladabi suka amsa mai ganin shi baisa dakata da zance da sukeyi ba. Daga can inda ya danja ya harde hannayen shi saman kirjin shi ya jefe masu tambaya daddy waye mukhatar usman Marwa ? Mukhatar usman marwa baffa Abdullahi ya maimaita sunan cikin mamaki daga gefe baffa hamza yace wanan matashin ne da yai arzikin fice a harkan ma,adaina da sauran su. Ai dan asalin kasan maidugurinr shi kuma yana taimakawa matasa sosai akace musan idan yasan sana,an ka kuma kana da sheda kan hakan zai iya tallafa maka ka daga kaima. Wait amma kamar nasan mai wanan sunan a baya duk da ina tantaman cewa shine a yanzu don an dade ban kara jin duriyan shi bama ni. Wanan dai dan maidugurine oh wanan kuma da nake fadi kamar a wurin sambo na sanshi a baya yazo dashi lokacin muna maiduguri har gidana wai ya hadu dashine yaje karatu ya samu matsala ana son aimai wullakanci a can shine ya taimaka mashi. Shi din daine shine wanda a yanzu ya dauki wanan karan da karfi shine case a yanzu ya koma hannun shi kan wasu abu da yake tuhuma garemu sai ya gyara zancen. Salati suka dauka lokaci guda baffa Abdullahine yake tambayan wa ya sanar mai da wanan maganan yanzu sai daddy ya dan yi murmushin manya yace mai yuyuwa su Sahiba dine ko? Don idan basu ba wa kake ganin yasan dashi ko yana tare da marigayin a baya sai su sai ko ni da Allah yasa zan sani din a lokacin. Sam basu bane don su na fara tuntuba koda sun san wani daya daukaka wanan maganan haka suka nuna min basu san komai su. Zasu fada ma gaskiyane daddy ya fada kai modibbo ya girgiza mashi yace tun zamana da su ban taba jin sahiba ta fadi karya ba ko abinda ba daidai ita fa kai tsaye take abinta . Daddy bayan wanan din jamin yansandan siri sun zo gidan nan neman ka na fada masu baka nan sunce zasu je su dawo dan anjima. Ni ni suka zo nema akan wani dalili kuma zasu zo har gida suna nemana ko wanan zance kotu dinne kuma suka biyoni gida kanshi. Ban tsamanin hakane gaskiya don su sai idan ana tuhuman mutum kan wani abu mai girma shine zasu baiyana ai. Nasan da wanan amma kuma zuwan su din shine ya daure min kai a yanzu bai gama rufe baki ba motan su ya danno ya tsaya a wajen gidan basu shigo ba . Ashe motocin har biyune ma bakake sabbi dal dasu suna sheki ga rubutun shi daga federal government suka zo Abuja can babban headquarters din su ke nan na Abuja. Har suka karaso aka gaisa nan suke tambayan waye Alh Ali dcp a cikin su ya dan murmusa jin wai basu sanshi ya nuna masu kanshi. Ok you're under are rest suka fito da takarda suka nuna mashi da sauri modibbo ya karaso yana fadin for what ? Sorry sir ya fada da alaman sun san mukamin shi sukace umurnine daga headquater din mu kan supect da