← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 317 OF 337

Sashe 317

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

yin wani aiki zan kwana biyu a can naso in tafi dake saidai hakan ba zai samu ba . Don mahaifiyata ta riga ta shedawa kowa zaki dan zauna a nan kwana biyu kafin nazo mu wuce Hong Kong a can zaki zauna don can business dina ke tashi yanzu nafi zama a Hong ko Dubai. Saiki zabi inda zaki zauna daga cikin biyun ya fada yana kallona tare da sakale loman daya diba a hannun shi. Inda hankalinka yafi kwanciya dana zauna duk dayane a gareni koda a nan din ne ma banda matsala ga hakan na fada a hankali ina sada kaina kasa lokaci guda. Hong din yafi don a can nafi zama sosai beside dubai din falmata da yara suna yawan zuwa hutu a can lokaci lokaci kuma gidan gudane. Naso nace dubai din amma kada na nuna kalana a fili sai nace is OK ba matsala kawai na mayar da hankali ga wayana. Hannu ya tsame a ruwan daya wankesu daidai lokacin naji muryan shi yana fadin will you be my guest at dis night ? Maganan yazo min a bazata har yakai ga haifar min da wani ciwon kai lokaci guda amma haka na dake bandai bashi amsa ba sai dan yaken danayi kawai a fuskana. Wayan shi yai kara ya dauka sai naga ya share kallon wayan da yaga na dan kalleshi sai ya dauki wayan tare da mikewa yana fadin hello ya dago min hannu alaman yana zuwa ya tafi . Dan binshi nayi da kallo kafin na mike na fara hada kayan don babu mai aiki nima kuma ban dauki hakan aiki ba na tsaya na gyara wurin saida ziciyana yana tune da zancen daya furta min dan mintina da suka wuce. Saidai duk abinda nake ina jin wani irin kullewan da marana yayi lokaci guda kamar dutse ya danne min maran abinda ban taba jiba a rayuwana. Haka na daure na kawar da komai a dadafe nakai dakina ina jin kamaf abu zai fito min a gabana lokaci guda. Haka na samu na isa bandakin don na kewaya ina tsugunnawa wani jini ya zubo min mai yawa kamar saren nono ya fado min da karfi saida na zabura dan tsoro. Da kyat na samu na dawo dakin na fada samsn gado ina faman nishin wahala da haka na lalubo wayana na kira fatima saidai tana busy a lokacin . Bandade da aje wayan ba sai gata a dakin daidai lokacin ins dunkule abin tausayi dani ina wani gurjin nishi mai nuna wahala ga mutum. Da sauri take fadin innalillahi meya faru anty sahiba da kyat na iya daga kai na nuna mata kasan marana dake min ciwon bala,i a lokacin guda haka. Shiga toilets kigani na iya fada da sauri ta fada toilet din dan ihunta naji lokaci guda ta fito tana fadin anty meye hakan tana tambayana. Ban sani ba na fada da kyar harfa motsi yakeyi nake gani ta fada a dan tsorace tare da kallon kofan toilet din a firgice. Uncle yasan da baki da lafiya ta tambayeni tare da tsureni da ido na kasa kai alaman a,a akirashi ke nan gaskiya wanan ba abin wasa bane. Da sauri na daga mata hannu alaman a,a ta barshi kawai, can wani tunane yazo min da hannu na nuna mata ta dauko min jakkana a cikin wardobe da sauri ta juya ta dauko. Na lalubi abinda nake nema na gani haka na daure ba mike zuwa toilet din har lokacin abin na nan yana motsi kamar abu mai rai. Na dade tsaye ina kallon abin kafin na fidda kwalban turarena na shaka a hancina nasan matsala don haka na daure nayi duk abinda ya dace inyi a lokacin sai lokacin abin mai kamar tsokan nama ko anta ya fara narkewa a hankali ya koma jini duk ina tsaye ina kallo. Ina jin muryan Fatima daga dakin tana kiran sunana anty ko in shigone nace gani fitowa yanzu haka na fito daga bayin bayan na wanke wurin na gyara jikina zakace kona haihune ina wani irin zufa na samu wuri na kwanta tun tana min sanni ina karbawa sai barci ya daukeni ban sani ba mai nauyi. Har ya gama abinda yakeyi baiga na leko ba sai yaga rashin dacewan hakan don shi ya kamata ya biyoni for the first time ai haka yasa ya taso daga dakin zuwa nawa part din. Yana sallama Fatima ta amsa mai idon shi a kaina yadda nake kwance din da sauri yake tambayan ta ko lafiya nan ta kwashe abindata sani ta fada mai. Hankalin shine ya tashi sosai yake fadin shine baku kirani ba bari muje asibiti kawai fatima din tace ta hana in fadamane kuma sai ina ganin ba na zuwa asibiti bane . Ana ciwon da bana asibiti ba fatima kada yazo ya zama mata matsala fa nan gaba bari kawai muje asibiti a tayar da ita lokacin nayi wani irin mika a cikin barcin har suna iya jin yadda kassan jikina ke wani kara lokaci guda . Dole haka suka kwana dani ina wanan mikan sai zuwa asuba komai ya lafa na koma barcina norman kamar bani ba hankalinshi yayi matukar tashi sosai har fatima din. Washe gari ban tashi da wuri ba sai wajajen takwas da rabi na safe na falka ina tashi ba wanan duduken a tafiya na koma normal dani kamar bani bace haka ya faru dani ba. Shima barci yayi don barcin dabai samu ba suna tare dani a halinda nake ciki da daren sai karfe daya yaje gidan nasa. Hira ya samu sunayi kamar ba ita ba ta sake sosai da kannenta da wata bakuwa kana kallonta kasan matar yar duniyace ta gaske. Haka ya wucesu suna gaidashi da kwana ya amsa ya shige yana jin dariyar Falmata din kamaf da gayya tana fadin saike hjyta ina yinki sosai hjyn kare kukanki. Dan ja yayi ya tsaya kafin ya daga kafa ya shige dakinshi duk zuciyar shi babu dadi a yadda yake ji suna jin rufo kofan shi. Take fadin wasa kake da Falmata wallahi baka sanni bane a yanzu mukhatar mu zuba dani daku aga karshen wasan .
Chapter 317 · 0% Book details