← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 337

Sashe 13

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau kusan kwana biyu ke nan ina zama a wurin ko zanganshi in rokeshi ya karbi kudin shi sai dai ban gashi ba har wanan lokacin.
Dole na daina fitowa tunda ya fada min dama wani yazo nema a unguwan don haka ba lalai bane in kara ganin shi kuma.
Gashi yanzun ba wani ciniki sosai don ruwan dake hana mutane samun sukuni yin cinikaiya a garin.
Don haka nake faman yin dan buga buga don mu samu abinda zamuci nida umman mu da dan kanina Amar da shima dai bai faye lafiya ba sosai.
Ga wanan kudin da aka ban umman mu ta hana a taba ko abinci mu saye dashi mu danci irin na kowa ta hana sam nima dai da farko na tsorace da zancen kudin.
Amma yanzu da ban kara ganin shi ba sai tsoro hakan ya fita min zuciya na koma harkokina na neman kudi kadan kadan don mu samu abinci da zamu ci kada mu kwana da yunwa.
Yau na makara da fita don ban dawo daga makaranta da wuri ba don haka na yanke shawaran kawai na je sarin kati in hada da bara lokaci guda ko Allah zai bani sa,a
Sai dai tunda na tunkaro wurin Indibisi dake bani sarin kati na hango shagon shi a rufe hakan na nufin bai nan ke nan a lokacin.
Gabana ya fadi da tsoro da fargaban kada mu kwana da yunwa a ranan haka na karasa ina tambayan makwatan shi sai da kyar dayan ya kalleni lalace yace bai nan ya tafi garin su an masa rasuwa.
Haka na juya da sanyin gwiwa ina tunanen ina zan dosa a lokacin gashi yamma tayi sosai don biyar da wani abu na yamma a lokacin.
Come now indibisi customer maker give u for today naw ai indibisi yana bamu labari ki u are good customer now oya come meke u quic quic go and come back in time b4 eight.
Tsaye nayi ina kallonta kafin ta kara fadin oya come naw ko ruwa zaki dauka gashi mai sanyi sun fara kankara a hankali na gyada kai tace da sauri tana mikewa taga kasuwa .
Don ni da niyata in dauki kati sai in hada dayin bara ko zan samu abinda mukai sai abincin da zamuci ga Amar ba lafiya kwana biyu ke nan tunda ruwan sama ya dukeshi hanyan dawowa daga school.
Allah da ikon shi duk da sanyin da akeyi sai gashi na sayar da daukan farko da nayi na dawo da murna nace zani gida ta bani share dina tace I beg me u cary anoda one now try u go sellam all please help me sellam .
Matar ta ban tausayi na dauka nakoma titi na fara bin layin motocin dake dawowa daga wurin aiki wasu daga kasuwa ina fadin buy cool water,
Pure water oga buy cool water daidai wata mota green dana tsaya ina kallon motan aka zuge glass din motan akace pure water.
Da sauri na haro wurin motan kafin in karaso har masu ruwa irina sun kawo ko naji a na fadin No you how much is your money inji wanda ke jan motan yana nuna roban ruwan da nake dauke dashi.
Nace da sauri three hundred naira i carry daga gefen shi aka miko kudi ana fadin in karba sai driver ya miko min daga haka ya motan shi suka tafi ina fadin oga u no carry d water naw.
Tsayawa kowa yayi yana kallona ganin haka sai na soke kudin a cikin jikina don ba abu mai wuya bane yanzu wani ya kwace a hannu na.
Na karasa yawata saura ruwa Allah ya kara ban sa,a na sayar na koma da sauri na mayar da kayan na hada da dan gudu wurin sayen abinci kada ya kare.
Na biya chemist na sayo magani wa umman mu da Amir na doso gida da gudu duk da akwai mutane a wurin lokacin amma suma ba abin yarda bane

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ANA DARA GA, , , , ,

6️⃣

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILAHI RAHAMANIN RAHIM IYA KA NA, ABUDDU WA IYAKA NAS, TA, IN, , , , , , , ,

LITTAFIN KUDINE KI BIYA KI KARANTA YAR UWA A CIKIN SALAMA, , , , , , ,

Zan shiga gidan nayi kicibis da wani mutum wanda ba yafita ko yaushe a gidan mu sai jefi jefi zaka ganshi koda darene ya fito.
Hakama ba ruwan shi da kowa a gidan sai dai zaka ga manyan mutane suna sintirin zuwa wajen safiya da marance yana daki shi a can kuma zasu same shi dakin suyi duk abinda zasuyi a dakin wanda bamu sani ba mu.
Na shigo da sauri don tunanen irin fadan da umma zatayi min don daren da nakai yau har misalin takwas da rabi nasan a lokacin hankalin su yana tashe da rashin dawowa na gidan da banyi ba akan lokaci.
Don duk iya dadewana a waje shine bakwai na dare zan dawo ko ina nake da duk abinda nakeyi zan barshi in dawo gida a wanan lokacin.
Sai gashi yau tunanen halin da muke ciki a dakin mu yasa nakai wanan lokacin a waje wurin neman kudi ban sanda shi tsaye a wurin ba ina zuwa da sauri ina haki don gudun dana danyo mukaci karo dashi har dan abincin da na sawo ya bare a kasa don zafin da naji ban san lokacin dana sake abincin ba wurin.
Abi ware ni ?
u no de si road u de warker wit ur eyes closed daya daga cikin yaran mutumin ke fadin haka da suka taso kamar zasu cinyeni danya a lokacin.
Ina kasa ina bin abincin dake kasa zube da kallo da takaici sai hawaye ke zuba min daga idona a lokacin nace.
Na dan dago a hankali daga duken da nake na soma fadin god go ponish u ina nuna wanda ya tureni din da yatsan hannuna ina hawaye.
Na sake fadin god go ponish u wetin i go gibe my mama today na d food i buy for dem naw u push me with dis ur big bodi d food don fowl down all.
Wani dan gidan bisi da muke kira iya bisi da sunan shi yana fitowa ya same mu a wurin yace ehh ya sayiba na d food wen your mama de wetin for nayin u puur ?
Hungry go kill u nd ur mama today wani irin haushi na kara ji a raina na sake fadin na dis yeye push me down.
Dayan da suke tarene ya daga hannu zai kai min mari sai wanda mukai karon dashi cikin tsawa yace mashi.
Takwabe don't toch her give her dat money make she buy anoda one na kalleshi a fusace ina fadin .
Me i no wan money my mama go beat me if i kwalet de money u wan give me na food i want na fada a gadarance.
C dis yeye girl wen de talk rubush i beg mey u carry d money go don't west our time joo sai naji ogan ya kalleni yace carry d money first meke he bring food for u inside.
Nan yacewa dan uwan ya dauko wanan abincin na dakin su ya kawo min shi dayan ya tura min kudin da yace a ban da karfi a jikina har saida na dan ja baya ya taka zuwa dakin da suke zama wanda gidan hayane ba ruwan wani da wani a gidan.
Ina tsaye ina dan kakaban ledan maganin dana sayo wa su umma wanda duk mai ya bata yana tsaye yana kallona har dayan ya iso da irin ledan nan na abincin resturan mai sunan shagon a jikin ledan ya miko min a fusace na karba sai kuma na kalli kudin dake hannuna nace.
Carry ur money back dis one is ok for me i go nak ur darty mouth if u no live dis place wanda ya ban ledan ya fada a fusace.
Ganin zasu iya dukana na wuce ina fadin my mama d come now if i go inside na wuce da sauri na bar wurin.
Ina jin shi yana fadin cary ur wahala go yeye girl u na disturb people for nothing hungry girl omo jagu.
Ni dai na shige da sauri a kofa na hango umma tsaye tana diban ta hanyar da zan fito da daren nan .
Ina karasowa take fadin Sahiba irin tarbiyan dana baki ke nan ki tsaya kina fada da maza a bainar jama,a haka yanzu fa iya wale ta kwankwasa min take fadin gaki can kina fada da maza a bakin kofa.
Umma tureni yayi fa abinci ya zube shine nake magana a kai sai kika ce su biya ki ko ?
Ta fada a fusace tana kallona a dan maraice nace ni ban ce su biyani ba sune dai suka bada kudin nan gasu na miko mata kudin da abinci .
Ta kalla tace na meye shi kuma kudin bayan abincin da suka bayar sai mukaji muryan wanan daya dauko min abincin a daki yana fadi whare are u come carry you vein u be lucky girl today our oga have macy on u.
Ya jefo min dan gyalen dana barshi a can da nake yafawa inyi sallah dashi idan sallah ya riskeni a waje.
Chapter 13 · 0% Book details