← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 337

Sashe 4

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanye take a cikin kayan makarantar da suka amsheta masu ruwan blue colour buje da riga babu batun dan kwali ko hijjabi sai dan hular bareti da ke saman kanta wanda ta dunkule gashin kanta ta cusa a cikin hula yasa dole don yawan gashin hulan ya dan dago ta baya kamar tayi a cuci maza dashi.
Bujen ya tsaya mata iya gwiwanta sai takalman da data sawo masu ita da kaninta wurin yan gwajon su na lagos masu kama da kwabattan maza take jansu hakana don kwarin su.
Bata damu da kanta ba ta dauko kulanda take sayawa kanin ta abinci don tara kada yaga sauran yara naci ya saka kanshi a damuwa .
Yasa a kullun bata yarda kanin nata yaje ba wani abinci a tare dashi kallon mahaifiyar su dake zaune ta kura masu ido kan duk abinda sukeyi na shirin fita makarantar tayi tana fadin.
Umma mun shirya zamu tafi uwar ta dan nida tare da fadin to dahiba ubangiji Allah ya tsare mun ku Allah ya bada sa,an abinda akaje nema a rayuwa.
Suka amsa gaba dayan su da amin don inda sabo sun saba da hakan a kullun idan zasu fita daga gidan zuwa wani wuri.
Suka fito tana binsu da kallo tausayi ga yayan nata kafin ta mayar da idonta tana cigaba tunane rayuwan data baro a baya gida har ta saka yayan nata a ciki wanan halin kangin talauci a yanzu.
Eh dolene yasa hakan a garesu don ta tsaretar da rayuwan su ga baki daya da ake nema a halakasu kan abin duniya.
Hakan yasa tayi nisa da gida nisan da ba wanda ya zata ko ya tsamaci har zata kai wanan garin mai nisa haka da bata da kowa a cikin shi.
Hawayene suka zubu mata a fuska lokaci daya don wanan tunanen da tayi na dan lokaci daya tasa hannu a hankali ta share ta dauki abin karin da Sahiba ta sayo mata don ta karya dashi.
Bayan ta gama ta mike zuwa wajen gidan don tasha iska kamar yadda ta saba yi a akullun ta zauna tana kallon mutanen gidan suna gittaya tunda rashin lafiyan nan ya kamata.
Duk da tasan ta makara hakan bai hanata kai kaninta har makarantar su ba har bakin ajin su ta kaishi kafin ta juya da sauri ta nufi nata wurin karatun .
Tafe take tana sauri kada malamin lissafi ya shigo bata ajin don tasan yau dashi zasu fara darasi a jin nasu gashi kuma mugune don dole saboda halin shi ta koyi lissafi har ta iya yanzu.
Bata ankara ba taji an watso mata irin ruwan dake kwanci a gefen hanya da sauri ta daga kai ta kalli drivern motan dake tafiya a hankali kafin ta sake dago kai ta mayar ga tufafinta daya baci da ruwanba lokaci guda .
Rantane taji ya baci don ganin yadda kayan nata ya baci cikin lokaci guda haka bata san lokacin data bude baki tana fadi a cikin harshen yarbancin daya zauna mata a baki yanzu radau .
Tana fadi a hasale Abi wareni ?
Olesi omo buruku noses ta hada da turanci cikin daga murya da karfi ta yada har mai jan motan zai iya jin muryanta.
Gani mai motan yaja ya tsaya sai can ya bata daina zagin a cikin harshen yarbancin ba sai can taga ya fito daga motan ya tun karo yarinyar daya batawa jikin nata don bada hakkuri shi kanshi bai so hakan ya faru ba har a ranshi hakan ya faru bane wajen kaucewa hanyar da yaje yi ya watso mata ruwan a jikinta gaba daya ya baci .
Ganin haka yasa ya yanke shawara fitowa ya bata hakkuri don sanin zafin abinda ya aikata mata din a lokacin.
Saidai tun daya tunkaro ta din yana jin muryan ta cikon dan hasala ta sake fadin you, you no desi road, see d way you skarter my cloth ?
Mumu man wen no get sense ta fada da karfi tana juyawa ta fara tafiya ta bar wurin don ta makara sosai a lokacin.
Tsaye yayi ya kasa karasowa inda take tsaye din sai faman kakaban kayanta da takeyi rana ta a bace kafin ta ja tsuki da karfi kafin ta soma tafiya rai bace tana fada kamar sabuwar mahaukaciya da ita.
Yana tsaye har lokacin yana tunanen ina yasan fuskan yarinyar nan ne sai kuma ya tuna ina fa zai santa wanan yar kabilan yarobane fa shi kuma baida wani alaka dasu saina aiki.
Ganin ta wuce batama tsaya ba yasa shima ya juya ya shiga mota yana jan tsuki a fili ya ja motar shi ya bar wurin yana fada a cikin zuciyan shi ya koma motan ya shiga ya tayar ya bar wurin zuwa lokaci shima ranshi ya gama baci da abinda yar yarinyar karama tayi mai don rashin mutuncin da ake fada yan lagos basu dashi dama.
Yana fada a zuciyan shi tare da jan tsuki fili yana cewa wani irin garine wanan marasa mutunci da rashin sanin girman mutum.
Har yakai inda zai tafi ransh yana bace har lokacin yana fada a zuciyan shi kafin abokin aikin shi ya jashi da fira duk da ya fahinci ran shi a lokacin kamar ya baci sai bai kula da hakan ba gare shi sosai don ya dauka dare fuska na dayaga cikin dabi,un shi don ko yaushe shi fuskan shi a daure yake.
Haka yasa yaci gaba da masa bayani har ya manta da komai na bacin ran da yake ciki da farko sukaci gaba da tsara yadda zasuyi su cin ma abinda ya fito dasu a lokacin har zuwa yamma kafin su rabu ya koma masaukin shi.
Sai dai duk abin nan hankalin shi naga abinda ya faru dashi da safe don ranshi ya baci da zancen abin daya faru din dashi na yadda yarinyar ta zage shi tsab da safe.
Don haka ya zama mai dole a yanzu yayi taka tsantsan da kowa a garin saboda ya karanci halin sune rashin mutunci dai.
Sahiba kuma dai a nata bangaren ta kasa suke jiki a makaranta don haka tun shiganta ajin take zaune a cikin class sai faman cika take tana batsewa ga banza tana fada a zuciyanta ita kadai.
Har ta dawo gida tana zaune tana cire takalman dake kafatan da safa ta take labartawa mahaifiyar ta abinda ya faru da ita dasafe a hanyarta na zuwa makarantan ta
Nan uwar take mata fadan ta daina zagin mutane haka tayi mai uzuri wata kila shima basan rashi ai ya watsa mata ruwan kwata ba da gagan sai dai idan yanayin hanyar dake kwancin ruwane yasa har motar ya watsa mata ruwan bai sani ba.
Da yarbanci take fadin umma shi makahone da ba yaganin mutane a kasa suna tafiya, kawai dai wullakancin sune na masu kudi shiyasa yayi min haka .
Ai da naga ya fito a fusace na gudunayi ai kada ya sameni a wurin ya dakeni a banza umma tace dako kin tsaya abinda zai maki ke nan ya dakeki ya daki banza.
Iya wale dake jin hiran su ta juye baki tana fadin kin san kuwa baku da kudin zuwa police station yin kara.
Jin ta tsoma baki kuma sun san hakan neman fitina kawai takeyi dasu irin nata yasa da ido umma tayi ma yar nata signal da tayi shiru.
Suka kyaleta don zasu iya cewa dasune kawai iya wale bataje police station ba wurin sharia a gidan duk da yawan da gidan ke dashi na yan haya tallakawa irin su masu karamin karfi a garin suke dandazon zuwa wanan unguwan don kama haya acikin saukin kudi.
Karshe dai mahaifiyar sune tayi masu nuni da su tashi subar wurun jin iya walen bata bar zancen ba har lokacin.
Suna shiga daki Sahiba ta fara shirin fita uwar na kallon ta yadda take sauri tace yau ina zaki ke na ?
Ta juyo tana saka hula a kanta tace kati zan sara in kai titi in gani ko za a dace don yau na makara da fita taba mahaifiyar ta amsa tana mikewa daga duken da take tana daure igiyan takalman da zata fita dasu.
Dukawa tayi gaban uwan tana fadin zata fita sai ta dawo ta kalli yar nata tana mata adduan kariya da samun sa,a ga wanan fitan da zatayi din kamar kullun.
Shagon da suke sarin kati su yawata a cikin gari ta nufa da farko mai shagon ya hana mata yace yamma yayi a lokacin.
Sai dai yawan rokon shi da magiya data dinga yi yasa ya ji dan tausayin ta don sun saba dashi tana yawan zuwa shago yasa ya dauko suka kirga na dubu biyar ya bata katin don yasan yarinyar tana da kwazo sosai ga wanan sana,ar.
Ba nawa da sauri ta yanke shawaran a ranta ta bin layin motoci tana sayar da katin don idan an hada go slow wani lokaci suna ciniki a wurin sosai.
Nan ta fara bin motocin a gurguje da dan sauri tana fadin buy credit mtn or eirtel glo yin ko, inda wasu suna saye wasu kuma su koreta akan ta damesu da yawan talla din a lokacin suna cikin uzuri.
Har karfe shida ya buga ba tare datayi cinikin kwarai ba don ko layi daya ba ta kai ga sayarwa ba a lokacin.
Ganin hakan sai jikinta yayi sanyi hankalin ta ya tashi sosai ga yamma sai kara karatowa yakeyi a lokacin.
Hakan ya kara tayar mata da hankali sosai a hankali taja jiki zuwa gefen titi ta zauna don duk motocin dake jere a titin tabi ta tallata kantin basu saye ba .
Gashi tasan da cewa abincin su ya kare idan sunci yau dan cinikin da tayi ba zai ishe su shiga makaranta da safe ita da kanin ta.
Duk tunanen da takeyi bai hana idan mota tazo wuce ta gaban ta tace dashi buy credit Oga five hundred, two hundred own or one by credit na all services we have .

ZAINB IDRIS MAKAWA

ANA DARA GA, , , , , , , ,

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILAHI RAHAMANIN RAHIM ALAHAMDULLILAHI RABBIL A,LAMIN, , , , , ,
Chapter 4 · 0% Book details