← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 257 OF 337

Sashe 257

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ake mashi. Kafadan shi daddy ya dafa yana fadin kyalesu mu tafi amma ku dan ! da baya suma hankali a tashe a lokacin ne modibbo ya fito da wayan shi yana neman layin umma. Daddy daya shiga ciki kuwa rudewa yayi ya kama kwalawa matan shi kira sai mommy ce ta fito take fadin hjy karima ai ina ga bata gidan nan don yara sunce tafita. Ya manta data kirashi zata tafi gidan baby din ta duk da baiso ba dole saida ya barta ta tafi din ta cikin waya don ba yadda ya iya da fitinan ta alokacin. Yace to zamu tafi don anzo tafiya dani Abuja a razane mommy tace Abuja lafiya Alh suwa zasu tafi dakai ? Jami,an tsaro ya bata amsa da gani baya cikin hankalin shi a lokacin kuka ta sake tana fadin akan wanan case din ne kuma za a tafi dakai ko me baffah Abdullahi ne ya bata amsa da shine dai ya taso kuma yanzu saidai bamu san akan me bane kuma yanzu ake neman shi can. Nan dai modibbo da ya shigo yana waya da basu san dawa yake ba a lokacin yake fadin wallahi fa yanzun nan gashima zasu wuce ai dashi yanzu haka ya tsaya yana sauraren wayan tare da fadin to shike nan hakan za ayi don umma tace ya bari na dawo na fita aiki dazun nan zata bincika yasa yace hakan. Bai samu kanshi ba sai wajajan karfe dayan rana ya samu shigowa wurin mahaifiyar nasa dattijuwace baka amma ba sosai ba da zubin irin na kunuri. Tana saye a cikin lafaya mai laushi kana gani kasan mai tsadane ga kamshin turaren su na asali dake tashi a falon tun har waje idan zaka shigo gida kamshine na asali zai tare ka. Da murmushi a fuskan shi ya karaso falon sukai arba da mahaifiyan nasa yasa ya sake mata lalausan murmushin dake karawa fuskan shi annuri. Saidai ya zube a kasa daidai saitin kafafuwan ta yana fadin ya salam tare da dora kanan shi saman kafafuwan ta ya sauke ajiyan zuciya kafin yace. INDA, WATTU UMMI, ta sauke murmushi tare da shafo kanshi daya dora saman jikin ta tana fadin WATTU KILLEFIYA ya dan murmusa cikin jin dadi ya kara noke kanshi saman cinyan nata yana dan sauke ajiyan zuciya karo na barkatai. Amma sun san da zaka zo yaudin ne ko wanan dandazon taron dana gani a waje haka nan ya dago yana fadin nima abinda ya ban mamaki ke nan dana tun karo gidan nan wai hakama a cikin siri na shigoma. Tashi kaci wani abu kafin komai lokacin sallah ya gabato kada wani kuma yazo ya hanaka samun lokacin haka da dare ma zauna idan ka samu kanka. Jin zata mike yasashi dagowa don yasan abinda take nufi shima tashi yayi suka nufi dinning inda abinci ke jiran shi aje alokacin da kanta ta zuba masu abincin ta dawo kusa dashi ta zauna. Kin yin magana tayi a lokacin donshi kawai sai hakan ya bashi daman samun lokacin dayaci abincin sosai tana kallon shi. Har saida ya kusa gamawa take fadin yanzun dai asirin su ya tono ke nan ya tabbata din zargin da kakeyi na shekaru su din ne suka kashe bawan Allah nan ashe ? Sai lokacin ya dago kai ya dan kalleta yace wallahi ummi sune sune da kansu sukai mashi wanan aikin kuma suka tura iyalan shi nisa da gida don barazanan da sukai masu lokacin. Salati dattijuwar ta sake tare da fadin kai duniya ina zaki damune haka wai yau har mun kai dan uwa ya kashe dan uwan shi don saboda dukiya. Mutum mai kirki mai mutunci ga addini da sun barshi ya rayu dasu da Allah kadai yasan abinda zai zama yanzu a kasan nan yau ba gakuba kuma na kasa gareshi Allah ya tsayawa rayuwan ku tai albarka.
Chapter 257 · 0% Book details