← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 250 OF 337

Sashe 250

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haba mami kin ko san abinda kike fada ayanzu akan yar marainiyar Allah yarinyar dako lafiya bata dashi na kula maza har kike kokarin aibanta ta da irin wanan kalamin. Me kaji na fada akanta yanzu na aubantawa gaskiya kawai na fasa game da ita shine kuma wani abin aibanta don kawai baku son ana fadin gaskiya idan an ganta. Mami barun fada maki wani abinda baki sani ba akan yarinyar nan yau wallahi mami koda kikaga ina tallafawa rayuwan sahiba da suka fada maki tun kafin hakan . Sahibace ta ceci rayuwana ta wankeni daga mugun zargin da ake min har gaskiya yanzo ya baiyana suka daina harata da sun kamani a wanan lokacin wallahi daurin rai da rai zasuyi min a lokacin. Alh mahammoud da kanshi yake duke yana karatun jarida saidai yana jin su abinda ke wakana a tsakanin su yace. Au itace yarinyar da ka fada min ke nan ashe data boye sani ka ta boye akan bata taba ganin fuskan kabama din da itama suke zargin ta. Yace Daddy wallahi itace tana karama sosai a lokacin ko yanzu ma ai karaman yarinyace girman daine Allah ya bata a cikin lokaci. Kafin ya juya wurin gwaggo hari din da tayi suman tsaye tana sauraren makusantan nata lokaci guda kan bayanin da bata taba sani ko jiba sai yau data tsunci zancen a bakunan su. The boy kai ta nunashi da yatsa yace wallahi mami nafi karfin shekara uku muna wanan case dasu modibbo da kike gani kike tambayan shi abindake hadamu wanan matsalan ne ya kafe akan sai ya kamani ya danka a hannun hukuman su an kaini kasan biyu da suke zargin mu. Labarin komai ya bata har zuwa wanke shin da nayi da fada mai wanda sukai mashi sherin ya kuma bincika har aka gano gaskiyan hakan gareshi. Yanzu ga irn sakayan da take binku dashi ko ranan ina jinku da Addah a gidan kuna mata irin kazafin nan ke ga naki itace silar fitar muna dashi cikin wahala. Yanzu kuma yaran Addah din duka uku ta sanadin ta sun samu wurin da zasu dogara da rayuwan su. Irin wanan halin da kuke nunawa shine yaci yan uwan ku a yanzu dama shi sherri ai dan aikene don komai dadewa watarana sai ya dawo kan maishi yanzu me gari ya waya garesu don Allah ? Don shi Nuhu ya dauka arzikin kota halin kaka yin sa akeyi a zauna lafiya baisan tarin nauyi da wahalan daya daukarwa kanshi ba ga hakan . Idan baku daina hakan ba wanan halin karshe a kanku zai dawo har ita Addah dake da diya mata har uku a gabanta dakema mai da daya tilo ki jawa kan ki fitina a sanadin hassada irin na dan Adam. Shiru tayi na dan lokaci tana kallon su kafin ta kai hannu ta share zufan dake karyo mata a goshin ta duk ko da sanyin Ac daya karade falon a lokacin. Sahiba in banda wayau da suke mata suna amfana da basiranta da Allah ya bata ba wani hakalan iskanci ko shashanci a tsakanin ta da kowa idan tace eh ga mutum ita sheke nan a gurin ta eh din Wai modibbone yaso ya kamaka daurin kuma daurin rai da rai dama ashe har akayi hakan ban sani ba ashe mami ta fada cikin mamaki ? Kallonta dan nata yayi yana fadin wanan kuma kada ki zarge shi don aikin shi yakeyi shi, kowa kuma yasan haka ka,idan aikin su yake tunfarko. A kan me zata zargeshi ma mijin nata ya fada shiba rantsuwa yayi akan aikin shi ba cewa ko mahaifin shi yai abu zai fada . Faizace a gaba muna binta a baya tayi sallama a bakin falon nasu da kamshin girgi da yar aikin gidan keyi a lokacin ya karde gidan tun daga waje. Waya takeyi yarsadan wanda hakan bai bata daman karba sallaman mu ba lokacin sai dai bin mu da tayi da kallo muna shigowa a wanan lokacin ne kuma shima ya tsaya da motan shi kofan gidan. Yaran suna wasan su a falon koda muka shigo babban ce ta dago kai ta kalle mu ta sheda mu sai tayo gun umma tana muna oyoyo kafin ta sake umma ta dawo gareni har Ammar. Wai amma kukan kunci da fari da har yar nan ta yarda daku haka kamar ta sanku dama ai ba wanda ya isa taje wajen shi banda mamanta da baban ta. Wayan ta aje tana cewa yar ke maryam jimun yarinya daga ganin baki sai kiyo kansu da gudu haka kamar ta san su tana zarewa yarinyar ido a daidai lokacin da karamar tazo ta fada jikin umma dake zaune duk da ba,a bamu wajen zama ba munyiwa kan mu matsugunni mu. Su waye wa yan nan kuma ta fada tana kallon faiza don son jin bayanin mu bakine sun zo gaida yayane da jikin shi. A, a umma so you're on the way ? I don't know that you people a coming yanzun nan na fita zan tafi office din mu wani aiki dama. Kafin ya juya akan mu yana fadin Sahiba you are welcome Yusuf how far now ta sake juyowa da kyau ta zuba min ido don jin sunan daya ambata a lokacin. Wai wanan din ce Sahiba dama ta fada tana watso min wani kallon tsana da nima na bita dashi jin ta ambaci sunana ya jiki mukai mashi kafin ya juya yana fadin ina matar nan mai aiki sa a kawo masu abin sha mana yana kallon matar nasa. Wace tayi kamar bata jishi ba lokacin umma tace a, a abarshi dai wallahi a koshe muke mu kan ba kishi ba yunwa an gode ta fada tana murmushi a fuskanta tare da dan shafan yarsu data kwanta mata a jiki. Uban yace kinga mama ko Aimana sai umma tace ashe bata manta damu gaba dayan su sun shedamu hakan ya bani mamaki sosai wallahi. Wani kallon mamaki takewa kowa na falon na yadda muka san yaran nata haka bata da labarin komai ita shine ya daure mata kai hakan. Muna cikin magana ya bamu labarin rashin lafiyan nasa yaran anty Amarya suka shigo gidan da sallaman su ai nan na manta da ita muka buge da hira sosai dasu kamar a baya. Mikewa mukayi zuwa waje don sunce suna son muyi hotuna a tare dasu kafin in tafi har umma suka fito suka sakemu a wajen hakan ya hana muyi sallama da ita har muka tafi bayan nayiwa su Fatiman har Faiza alheri daga jakkana muka kuma sauke tsaraban da mukazowa yaran ya modibbo din dashi. Mun isa Yola kamar yadda aka shirya cewa zasu zo su taremu daga gidan babban wan su umma dake cikin garin yola yanzu zaune. A wanan ranan na sheda ashe muna da yan uwa raye a duniya irin so da kaunan da suka nunawa ganin mu don mun samu gidan nasa a cike da yan uwa da sukaji zuwan mu sukazo don ganin umma din damu. Nan kuma aka zauna ana jajanta mata abinda ya faru tare da adduan samun nasara a kansu sun dai sha tsina da mugun fata a wurin dangin umma din. Kwanan mu uku a yola cikin jin dadi da nuna muna karamci muka nufi kauyen su umma din kai tsaye a ruggan su mukaya da zango . Nan ma munga kauna da so a wurin su sosai anan na sheda idan asalin kyaumu ya fito duk zaka gansu zubin daya dogaye farare masu kyau da zubin filanin farko dasu har saika rantse su din wasu yare ne na waje. Saukin abin dai nama ne don haka ina cin abinda aka sarafa muna naman dashi ba wani kyama amma duk abinda ya danganci abin ruwane shi ko menene kuwa ko kamshin naji zan bar wurin idan ba Allah ya gyara ba har amai nakan yi wani lokaci. Idanuwana sukan juye su canza kalla zuwa ja jajir kaina ya dinga ciwo tsawon wani lokaci wanan yasa a yanzu dana fara wayau nake kiyayyewa bana yarda da abinda zai jawo min matsala kuma. Saidai ashe wai haka yan uwan mu na gefen umma dana gefen mahaifiyat mahaifina suke dayawa din su suma basa cin abin ruwa saidai ba duka ba suma don akwai irin su umma da kan danci itama din ba damun ta yayi ba sosai. Tsaraba sosai mukaje dashi kwanan mu biyu a wurin su kuma muka kara gaba zuwa wajen dangin mahaifin mu ta fanin mahaifiyar shi. Naji dadin wanan tafiyan na kuma san muna da gata ashe a duniya mmuma kuma muna da yan uwa na jini dake matukar son mu a duniya. Nakan ji manyan su na fadin kamata sak da wace ta haifi mahaifiyar Abban mu da tsayina da komai wai har yatsun kafa nata ne na kwaso suke fadi. Ana gobe zamu shiga kotu muka koma laduna badon mun so rabuwa dasu ba suma din hakan tare da muna alkawarin wasun su zasuzo har idan muke su gane mu suma. Tunda muka shiga kaduna barci nakeyi ban falka ba sai yamma lis don gajiya da kewan yan uwa ina faman rayawa a raina cewa yanzu kan naga inda yan uwa suke masu son mu. Bayan sallan magariba ne muna zaune falon gidan wayan umma yai kara ya Abubakarne ya kirata yana tambaya ko mjn dawo ko muna yola din. Muna cikin kaduna dazun nan da yamma muka dawo umma ta bashi amsa yayi muna sannu da zuwa yake fadin. Gobe insha Allahu za a shiga kotu daddy ma yana nan ya dawo sati daya ke nan watau tun tafiyan mu yola ya dawo shima kasan. Washe gari mun dan so mu makara a lokacin don zuwan kotu har mutane sun dan fara kus kus akan rashin halarta mu din sai gamu. Hakkuri lauyan mu ya bada aka fara shari,a yadda ya dace ayi din inda alkali ya nemi daddy daya ba umurni dawowa kasan don tuhuman da ake masa yazo ya kare kan shi a kotun. Dadi ya fito cikin kamala da shiga na jallabiya mai ruwan madara sai yar hular dara ja akanshi daya saka don kare mutuncin shi duk wanda ke zaune ya bishi da kallo. Kamar yadda akewa kowa tambaya
Chapter 250 · 0% Book details