← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 337

Sashe 109

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

a lokaci. Banda aiki ranan Saturday amma hakan na kirkirowa kaina fita tun safe na shirya nacewa umma akwai screening da za ai muna a shagon da nake aiki . Kallona umma tayi tana fadin wani screening zaki kuma yanzu keda kikace zaki bar shagon wahala yai maki yawa yanzu zaki daina aiki dasu. Amma ai umma ban barsu ba tukun na kinga dole in je ayi min don sai karshen shekara nake son na aje dama lokacin sun bamu bonazan kaya yadda muma zamuci riban mu dasu. Allah ya tsare umma tayi min na fita Allah ya gani banyi niyar zuwa shagon ba amma haka na daure na fita duk wanda ya ganni sai yayi mamakin ganina a lkacin haka na daure nayi signing na fara aiki kamar yadda muka saba dasu ban damu da kallon mamakin da sauran ke min ba don ba fuskan da wani zai iya tambaya don ko matan ma,aikatan daga gaisuwa ba abinda ke hadani dasu kuma. Ni sam a rayuwana ban yarda da abokiya ba haka kuma bana sakin fuskan da zaka ga damana har ka samu shiga a wurina kowa ban yarda dashi ba haka Allah yayi min rayuwana ni. Wasu mata da mijine hausawa ta shigan su na gane hakan don sunyi irin shiga na arewa har yayayen su biyu suka zo part din kayan kamshi dana gyaran jikin mata. Matar ta daga wani set din man shafi take fadin su dauke shi mijin yace a cikin hausa nifa kin san bana son man da ke saka mutum haske ko ya canza mai kalan jikin shi. Matar tace dashi amm kuma ai naga wanan din na larabawa ne nasan zaiyi kamshi bawau don fari na daukeshi ba mijin ya sake fadin ki dai duba wani zaifi. Lah yayana daka barta ta dauka tunda tana so wanan baya saka haske sai dai ya gyara mata natural skin din ta zai kara kyau ne kawai nan babu kayan karin haske gasu can daga baya ku kun baro wurin wacan yarinyar. Bayani nake masu amma su sun tsaya suna kare min kallo a cikin mamaki har na kare masu bayani suna tsaye sororo suna kare min kallo. Ikon Allah matar ta fada tana murmushi yanzu ke din nan ashe kin iya hausa a bakin ki haka radau kamar jakar kano. Amma dai ke haihuwan arewace ko nace ni bafulatanan jalingo ce saidai a kaduna aka haifeni na kuma tashi a lagos kamar yadda kike gani na yanzu. Ta dan sake dan murmushi har hakoran makkan ta na gold suka dan bayana fili tana fadin aiko ga kama nan mun gani a zahiri da fulani. Amma ke bakuwace a shagon nan mijin ya fada daga bayan ta yana rike da hannun yaran su , nace a,a na dan dade a nan kuwa. Saidai da yamma nake aiki dasu na tashi da dare don ina zuwa makaranta da rana mijin ya dan taka ya barmu a wurin tana dan dariya kamar taga wata yar uwanta na gida. Mu muna nan Apapa ne zaune kusa da Olamide eyes center sai na danyi murmushi don Olamide yana bayan mu kadan nace kinga kuwa muma a ta gaban shi muke zaune ai. Zuwan wasu custemers yasa na barta na dan tafi wurin su ina masu bayani baisa matar nan ta barni ba sai ta tsaya tana jiran in gama dasu. Ban gama da wuri ba har mijin ya kirata suka nufi wani wurin na fita zancen su nikan na kama aukin gabana na saka ido ga kaya tare da jagoran masu zuwa sayan kaya kamar yadda akeyi. Na dauka sun tafi sai gasu sun dawo inda nake matar ke fadin kinga yar uwa har zamu tafi ban san sunan ki ba nace mu dawo don Allah na tambaye ki. Sunana Sahiba amma Fatima nake da Sahiba din ake kirana har a gida gaskiya kina da suna mai kyau shigowan wani ya dauke ma mijin ta hankali har ya barmu mukai musayan lamba da ita da kwatancen gidajen mu sai gasu sun tako zuwa inda muke daga bayan mu ana fadin. Kai madam yau kece da kanki kika shigo shagon mu ta waiga tana dan murmushi tare da fadin wallahi oga Sha,aban . Nice fa yau a shagon naku mai a lbarka nace bari dai yau na biyo shi nazo naga shagon naku don oga saidai yazo shi yana ban labarin girman shagon nan Good day sir na fada daga bayan matan inda nake tsaye na juya ban jira amsan shi ba nasa kai na bar wurin ga baki daya. Wani irin faduwan gaba nake ji wanan ne karo na biyu da muke haduwa dashi a shagon sai kuma ranan nasan ainihin masu wanan katon shagon haka. Zasu tafi wanan matar ta kara magana akaina don naga duk sun juyo gaba dayan su lokaci guda sai kuma sukaci gaba da magana don ina dan nisa dasu banji me suke fada ba a lokacin. Da hannu ta kirani nazo da sauri wanan karon don ganin su tare da wanda nake zaton a yanzu sune masu shagon nan da muke aiki a cikin sa shine kuma wanda ya kaini gida ranan idan baki manta ba don yanzu ankai wata shidda sai ranan kuma na sake ganin shi na kuma shedashi. Take care of her ya fada lokacin da suka dan fara tafiya da mijin matar sai matar tace dashi wanan ma ai kusan ta fika iya hausa zance. Yayi murmushi sukaci gaba da tafiya da gani suna wani magana ne mai muhinmanci a lokacin don yadda naga suna zancen daga nisa. Kin gashi can shike da wanan shagon a waje yake zama don rayuwan shi gaba daya a can yayi shi . Yadda ma,aruf ke fada min sunyi karatu tare dashi aminin shine sosai suna karatu saidai kasancewan shi dan masu hali suna gama karatu ya fara harkan business shi kuma ya fara aikin gwaunati a nan kasan. Shidin dan wani shararen dan kasuwa ne dan arewa saidai mahaifiyar shi ta kasance yar garin nan ne ita don haka yake ruwa biyu shi. Yana zama a kasashen labawa ne shi can yake harkokin rayuwan shi sai dai a yanzu naji Ma,aruf na fadin yana son ya dawo nan gida Nageria da zamane. Wanda nasan mawuyacin abune ya iya hakan Allah sarki azuciyana kuma nace wai fadi ba,a tambayeki ba ke nan mata da bakin zuba haka sai kace wata aku. Ni a tsarina ban son yawan surutu gaskiya haka Allah yayi min rayuwa na hannuna naji ta rike tana fadin zo mu zaga ki tayani zaben kaya dama ya hanani zabe shi kuma ba mace ba yar uwana. Ina mamakin wasu abin komai tsadan su zanga ta dauki biyu har dai takai mun gama a daidai lokacin da suma suka dan fito mijin na fadin idan ta gama ta sameshi waje. Sai bayan anyi komai an saka kayan a cikin leda ne kawai naga ta miko min dayan ledan tana fadin wanan nakine kanwata don yau kin debe min kewa sosai wallahi. Ga abokan aikina sai bina da kallin mamaki sukeyi har dai lokacin da suka tafi na dawo cikin shagon naci gaba da harkokina ban dawo gida ba sai dare lokacin dana saba tasowa daga wurin aikin na shigo gida. Umma har sun kwashe sun shiga ciki nayi mamakin hakan sai kuma nayi tunanen saboda sanyin da akayi ranan ne yasa ta kwashe da wuri haka zuwa ciki. Da kayana niki niki da matar nan ta saya min na shiga gida da sallamana umma na zaune a falo da gani hankalin ta a tashe yake. Ledan dake hannu na tabi da kallon har na aje ina fadin umma sannu da gida na juya wurin Amar ina fadin kai how far ya kake ? Ke gidan ubanwa kika shiga haka umma ta fada a cikin wani murya da ban san tana dashi ba nima dan tsorata nayi ina fadin umma na fada maki shago zan tafi ai dazun da safe.
Chapter 109 · 0% Book details