Sashe 91
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
tare da mommy din ya nufo can. Sun gaisa ne mommy tayi mashi bayani tiryan tiryan tundaga farko kallona yayi tare da fadin Na, ur mamiyota tell u dis torry in ur dream, or what, sai kuma yayi murmshi yana fadin yanzu me daddy yace akan hakan ? Zaifa shigane idan ba an masa da gaske ba mommy ta fada a cikin damuwa ya mike yana fadin daddy ne baisan wanan yar tasa ba don har magani tayi talla a lagos, Don haka ba abin mamaki bane idan tana fadin hakan a yanzu ni ba abun mamaki bane a wurina don nasan waye Sahiba. Ya fita yana fita ya nufi wurin daddy suka gaisa yake tambayan shi matar shi yace tana lafiya bissimillah daddy yayi mai yace ban koyi brush ba na zo nan . Daddy ina key din garejin nan ya kallo dan nasa yace yana nan yace a dauko wancan dayan motan dake ciki a wankrshi kafin daurin aure sai a kai wanan din ciki ajeshi. Kaima ka yarda da zancen su ke nan ko yayi murmushi ya mike ya soma tafiya zuwa waje kana yace ba kasan yar nan taka bace daddy har yanzu . Bai yarda yabar gidan ba saida aka fito da wata motan aka fara wankewa yace zai tafi gida ya shirya kada ya makara sukai sallama . Mommy ne tazo take fada muna yadda akayi hankalin kowa ya kwanta saidai kuma mommy tace waye wanan mutumin da sahiba ta gani a cikin mafarki? Hakana na shirya muka tafi don ranan ne bukin gashi kuma hankalin mu ya kasu gida biyu kan wanan zancen. Muna gidan bukin aka bugowa su mommy waya motan daddy ta kama da wuta a cikin gareji sai da kyat aka samu aka kashe wutan . Gaba dayan mu muka koma gida tare da wasu yan uwa nasu abin dai baiyi kyau ba gaskiya don haka kawai akaga motar ta kama da wuta. Kusan motar muce ta karshen dawowa a gidan muna fitowa ido yayo kanmu caaa har saida muka tsargu da kallon da ake muna din ashe mommy ne ta fara fadin dama Sahiba ta fadi. Ashe abinda zai faru ke nan ya tsaya ga motan shine mutane suka sako muna ido da muka shigo gidan a take sai akaso a juya zancen wasu suce kila ina sikiro ne naso na cinye daddy din. Sai da daddy yake fadin ita kuma nata baiwan ke nan sanin abu a cikin mafalki abinda zai faru ke nan ta gani ta fada muna dazun ashe ? Haka kowa ya tafi yana fadin albarkacin bakin shi su Anty kuwa cewa akeyi yaya za ayi haka kawai mota tana ajiye ta kama da wuta idan ba wani kullalan da akayi masa su dai kan basu taba ganin haka a gidan su. Duk da naso komawa gidan bukin ban samu hakan ba don kaina dake min mugunciwon nan dai da yakan dameni idan haka ya faru dani. Kwantawa nayi sai bayan magariba umma ta tayar dani daga barci tana fada dole haka na tashi naje nayi wanka sanan na danji dadin jikina. Don maitan Fa,iza a kaina ina shirin kwanciya sai gata dakin mu wai ta dawone muje wurin dinner da za ayi mu tafi tare. Naso naki zuwa amma sai umma tayi min magana akan nashirya mu tafi wata kila idan na dan fita jikin nawa ya kara walwale mun a can . Dole haka na shirya muka fita zuwa wurin bukin inda ake dinner din wurin ya cika sosai da mutane har wajen wurin. Haka muka samu muka kusa muka shiga bayan mun nuna pass din mu dukko da anko din dina din dake jikin mu a lokacin.