← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 337

Sashe 140

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana tsaye ya zuba min idanun shi ba kiftawa jikin shi saye da farar shedata maza mai dinki iya cinyar shi da guntun hannu. Ga shaddan sai maiko takeyi alaman tsada da sabon taka a jikin shi agogon hannun shi silver sai kyali da yakeyi da takalma baki rufafu a kafan shi. Shiru yayi baiyi magana ba sai kallon mamaki da yake min naci gaba da fadin yaya na dauko ko duk dangi sun kimu kaida yan gidan ku ba zaku taba mantawa da muba ai yadda kuka nuna muna kauna. Sai gashi har kun din kun manta damu kun watsar damu a cikin kabila kun fita batun mu kun barmu a nan muna rayuwan kadaici. Haka baisa mun zargeka ba sam don kaima hawan abin kayi daga sama yaya dalili yana iyasa ka fita zancen mu idan kaga abin zai shafi wani naka don haka zaka iya mantawa damu, , , Sahiba ya fada da karfi a lokacin ne wani kuka mai karfi dayafi wanda nakeyi yazo min na dago ina fadin haka ya tabbatar muna da kissan Abban mu ya shafi duk ahalin mu ga baki daya ke nan, , , , , , Sake kiran sunana yayi a cikin tsawa a daidai lokacin da gaba daya yan gidan namu ke fitowa zuwa wurin ga baki dayan su umma har tana hadawa da dan gudu tana saukowa. Kilode sahiba na dago kai na kalleta a cikin hawaye ina fadin ko,sin kankan, ina nuna mata shi da mamaki a fuskan ta yadda manya kan rude wani lokaci idan sunga tashin hankali. Juyowa yayi don jin muryan umma din da magana ya makale mata lokaci daya duk abinda take da niyar fada nakinta yayi nauyi ta kasa fadi lokaci guda. Sai nuna Abubakar din da yatsa da takeyi can ta samu bakinta ya bude tana fadin modibbo kaine yau ? Ya dan murmusa cikin takaici yana fadin nice umma mun sameku lafiya yaya gida ya bayan rabuwa zoka shiga ciki umma ta fada ba tare data amsa mashi gaisuwan shi ba har lkacin kuka nake darza a wurin sosai . Amar na isowa yana sheda fuskanshi ya fada a jikin shi lokaci daya yana kiran sunan shi yana sake kuka mai karfi shima. Duk dauriyan ya Abubakar din ya kasa rike hawayen shi shima din dai kukan yakeyi sosai a lokacin hankali tashe. Nan umma tasa hannu tana fincike Amar din da shima ya rike shi a lokacin tana fadin ku barshi ya shiga ciki kun tsaya a nan kuna kuka haka kowa na kallon ku. Sai kuma ta juya wurin muniya tana fadin muniya broda din mune daya tafi shekara kusan biyar kenan rabon shi damu. Shine wanda ya saya muna wanan gidan da muke cikin sa tana nuna gidan dagani itama umma din a rude take a lokacin don bata cikin natsuwan ta idan kaganta. Inda nake tsaye na dafa mota dayazo a cikin ta ina rusa kuka ya nufa hannuna naji an riko wanda na gane ba hannun umma bane lokacin yasa na juyo da sauri. Shine a tsaye bayana yana fadin zo mu shiga daga ciki ku daina kuka haka gani na dawo da karfin Allah gareku wanan karon insha Allahu kunyi hakkuri ku saurari uzurina don Allah. Zomu shiga ciki ya fada yana mai kura min ido yana kallon cikin kwayan idona lokacin na mike nabi hanya ba tare da masa magana ba zuwa ciki. Shima din jan hannun Ammar yayi suka nufi hanyan cikin gidan namu yana sharewa kanin nasa hawaye tare da danyi mai magana a cikin kunnen sa. Ban tsaya falo ba daki na nufa na fada saman gado naci gaba da kukan da zance ga dalilin shi ba a lokacin dalili daya ya kawo shi shine zuwan yaya Abubakar wuein mu yau. Ina jin muryan su a falo tare da umma bai fadi komai ba shi ummace ke magana duk daba wani abu take fadi ba sai tambayan shi da tayi mutanen gida da sauran su. Barin zo umma ya fada ya mike tare da tambayan ina ciki ko aka bashi amsa da ina ciki ya shiga da sallaman shi dakin ya hangoni nayi rub da ciki kwance saman gado ina kuka. A kofa ya dan tsaya ya kura min ido kafin ya karaso cikin dakin yana kiran sunana jin ya zauna a bakin gadon kadan kusa dani yasani motsawa lokacin. Kara kiran sunana yayi yana fadin kukan ya isa haka don Allah nasan nayi laifi babba na tafi na barki da fama dasu umma da Ammar amma ki saurari uzurina kan haka. Mikewa nayi na fito falo wurin umma ya bini da kallon tausayi don yasan irin zafin da mukeji a lokacin ya dan kada kai ya mike ya fito daga dakin. Ummace ta kalleshi tana fadin sahiba badai rikici ba idan ta tashi yi yanzu murnan ganin shi kukewa kuka haka ko baku so ya dawo garemu bane yasa kuyin kukan nan. Barsu, suyi umma don a zaton su na tafi na barkune da wani manufa Allah ne shedana tafiyane ya kamani tun ranan dana aje ku a gidan nan. Gaba daya nida iyalina muka bar kasan nan sai kuma nayi kuskuren daukan layin ku a lokacin don azatona zan kara zuwa na dauki layin ku ko kuma lokacin ba bukata tunda zan dinga zuwa kai da kai ina ganin ku. Saidai gaskiya nayi mamaki kwarai lokacin dana dawo kasan nan naji cewa tun lokacin ba wanda ya neme ku har zuwa yanzu din. Bansan da haka ba a bakjn Amira yar hjy karima nasan basu tare daku ashe yadda na zata abinda ya ban mamaki kwarai ke nan a lokacin. Dakuma nayi tunanen cewa nima kaina gaba daya wani tunane a kanku ya gushe a zuciyana yasa na fara zargin cewa dole akwai wani dalilin hakan an matar damu ku an cire muna ku a zukatan mu ga baki daya. Saidai abjn mamaki ba a cire ku a zuciyae Amira da Faiza tare da fatima idan yai zan shiga cikin gida don mu gaisa zakaji Amira tace yaya ka kaini wurin sahiba. A sauri don Allah ita kuma Fa,iza zata labe tana tambayana yaya ka samu layin sahiba din ka bani wanan ya kara min karfi a zuciyana jiya tana tambayana na koma gida na kwana da shirin zuwa duban ku yau din nan. Karshema kuma kyautan da sahiba ta turawa yan uwan nata ya kara karfafa zancen ku a yanzu don yadda hjy karima ke fada min cewa saida takai ga dukan yaran kan tambayan da suke mata ko da acikin darene. Kunji abinda ya faru wanda nasan wani kulline akan hakan don Allah kuyi hakkuri da abinda ya faru banayi bane don wani manufa a gareku. Haba modibbo idan kana da wani munufa akan mu tun farko aiba zaka daukemu ka kaimu wurin dangi ba tsawon shekaru ba kuma zaka nema muna wurin zama a nan ks hanemu da yawon hayaba ai. Kayi muna hanyar da zamu dagora da kanmu nabada haya a dayan bangaren kudi na shigo muna ta cikin sauki a yanzu duk da yake hayan ya zama kamar gidane don wanda ke ciki a yanzu kamar dan uwa muka koma dashi a nan. Mutumin kirki muka samu don tun lokacin bamu sa wani a gidan nan ba yana rufene kawai sai lokacin da wanan mutumin ya shigo rayuwan mu a karshe kuma sai gashi ya samu matsala da gidan da yake haya shine muka bashi nan su zauna a cikin sauki don wurin aikin su daya da sahiba shine sabon mu dashi. Ya dago yana fadin Sahiba din aiki takeyi yanzu wani irin aiki takeyi a yanzu din kafin umma ta bashi amsa wayana dake gefe yayi kara na dauka. Felix ne da zolayan sbi ya fara mun hira yana ban labarin wai yau sun tashi oga na fada masu cewa sun danyi wasu sauye sauye taron da za,ayi don haka na shigo karfe hudu mu zauna kan sabon tsarin da akayi din. Kinsan masu kudin nan da wahal da tallaka ya dauka mu bamu da abunyi ne a garin sai nasa tsarin koda yake fa muna samu oga badai kirki ba kan don nasan bamu tashi a taron nan banza. Jin abinda yake fadi yasa na danyi murmushi daya baiyanar asirin kyawawan dumple dina a fili har suka dan lotsa kyawona ya baiyana a fili sosai. Daga inda yake zaune yana satan kallona ya lumshe idon shi yana ambatan subbahanallahi haka yarinyar nan take dama ashe ? Na sake dago kai lokacin da Felix din ke fadin kedai yarinya fito da katon jakarki gobe zamuji dumus a wurin ogan mu sosai na sani. Fararen idanuwan nawa da suke farare tas gashin ido dogaye don wasu na dauka ina saka eyes lashes ne a idona haka gashin gira na suma a kwance bakikirin dasu kamar an jera min su. Dariya nake sosai ina kara juyawa kamar da gaiyya nake juyasu a lokacin wanda ma ban san ina yin hakan bani sam. Ido ya kura min yana kallona tare da tunanen yadda na sauya ga baki daya ko magana na yanzu abin kallone don a cikin wayewa da isa nani watace nake wayan yana kuma jin kalaman mu da Felix din. Nan dai muka dauki lokaci a wayan ni da Felix din indan na dago kaina har fararen idanuwa suka sauka a nasa ganin zan kallo inda yake sai yayi saurin kawar da idon shi gefe da sauri. Subbahanallahi yake iya ambata don ganin yadda nake sauke idon ganin yadda wayewa da natsuwa yake a tare dani ga wani irin kwanciyar hankali daya hango . A take yaji wani irin faduwan gaba ya sauka masa tare da tsoro da fargaba yanayin nan da yake kallona a cikin shi zaune gaban shi lokacin. Don dai komai nawa har nasu umma din da Ammar a yanzu ya sauya muna ba kamar yadda muke a cikin wahalan rayuwa ba a baya. Saidai kuma yasan ba karamin kudine zaiyi wanan aikin ba a garemu haka dole dai da akwai babban madafan da muke dafawa a rayuwa daya sauyamu haka lokaci guda yanasa a zuciyar shi. Daidai lokacin da yaji ina sallama da wanda nake wayan ya mike yana
Chapter 140 · 0% Book details