← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 311 OF 337

Sashe 311

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

komai na cikinsa farine kal sabanin na part dina da yake milk colour. Zaunar dani yayi ya nufi wurin abin sanyin dake dakin sai gashi dauke da goran ruwa da cup a hannun shi yazo ya zauna a kusa dani ruwa ya tsiyaya ya miko min kaina girgiza masa alaman a, a. Open your mouth ya fada yana kai cup din a bakina zaki samu relief idan kin kurba ruwan kisha ko kadan ne ya fada yana kallon fuskana. Kai hannu nayi zan karba daga hannnun shi kai ya girgiza min yana fadin a, a karbi kisha kawai ba musu na dan kai bakina na kurba dan ruwan kadan tare da lumshe idanu. Good girl ina son mutum mai saukin kai kamarki yanzu fada min komai ya wuce ko mu shirya zuwa kadunan ne muna a yau din nan ? Kai na dan dago na kalleshi yace yes saina kaiki a yau din nan na fada masu kukan banza kike min don sun wuce sun bar minke a nan don baki yarda dani ba. Irin kallon da nake masa yasa yace yes koba haka babe baki yardani ba baki kuma daukeni a matsayin mijin ki kuma dan uwan ki ba har yanzu why zaki dinga kuka haka sahiba ? Kina son kijawa kan ki wani matsalane kuma yanzu ki tashi ki dan kwanta nasan akwai gajiya har yanzu a tare dake idan kin samu barci a yanzu komai zai wuce a zuciyar ki duk a cikin harshen turanci yake min magana don dole sai dashi zamu fahinci me muke nufi. Ta fito dan yau itama bakin ta zasu tafi duk da tasan yayi sallama dasu a daren jiya din kuma ya bada mota da za a kaisu airport. Amma zata so su kara sallama saidai tana nufar part din shi ta hango wurin a rufe a zatonta yana ciki har lokacin bai tashi ba. Saidai tana nufa kofar a cikin kasaita sai gaida ita masu aiki ke faman yi taji dayan na fadin hjy oga ya fita tun dazun da safe ai . Cak ta tsaya tana sauraron me maganan tace mene tare da kallon shi tana son karin bayani daga bakin shi yace eh oga ya fita dazun nan . Ina ya tafi da safen nan ta tambayi kanta tana juyawa don barin wurin haka ta koma part din ta har bakin suka tafi bata daina tunanen inda mijin nata ya tafi ba tare daya sallameta ba. Duban lokaci tayi idan ba karya idon ta ke mata ba yanzu shabiyu da wani abu na rana ji tayi ranta ya kara baci fiye da farko sai lokacin ta mike zuwa falo har lokacin abinci na ajiye haka ya karasa ranta baci karo na barkatai. Zama tayi don taci abinci idan ya dawo sai yaci nasa da sauri dayan matan yar aiki ta karaso ta fara zuba mata hannu ta daga alaman ya isa hakana. A hankali ta fara ci bayanta jawo abincin zuwa gabanta saidai da kyat ta iya hade spoon din farko data saka a bakinta tana taunashi kamat maicin magani. Ina mukhatar ya tafi haka koda gidan hjy ne zai tafi atlist zai fada mata cewa zai tafi gaida hjy balle wani wajen . Waya ta dauko dake gefen ta ta danna masa kira ya shiga saidai bai dauka ba har kiran ya katse yana kallo kuma bai dauki kiran nata ba a lokacin. Tsuki taja tare da kai hannu zata dauki spoon din da take cin abincin dake gabanta sai zuciyar ta ya hasko mata ke kodai yana tare da amaryashi ce . What ta fada karda ace mukhatar ya samu kebewa da wanan yarinyar ke nan a yanzu wait ta fada tana kada yatsun hannun ta suka bada sauti. Impossible ta fada tana mikewa tare da daukan wayan nata ta shige part dinta a hasale a nan tabar abincin bata damu da rashin karyawanta ba na ranan. Kira ta sake danna mai wanan katon ma ba,a dauka ba har kira uku bai daga ba abinda ya bata mata rai ke nan zuciyar ta kuma ya kara tabbatar mata da lalai ya samu kebewa da amaryan sa ke nan duk da a gidan ta ya kwana ranan kuma tasani . Me hakan da mukhatar yai mata yake nufi yanzu yana nufin har ya fara juya mata bayane kan yarinyar nan ko me hakan da yai mata yake nufi yanzu ?
Chapter 311 · 0% Book details