Sashe 306
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
bane na nan da aka saba gani ina jin gwaggo hari na fadin dankari saidai muce Allah yasa mu cika da imani kawai masu kudi na inda suke kasan nan ashe. Aikuwa ciki taga mun shiga kai tsaye nan ta suma zaune tana raban idanu har motocin sukaja suka tsaya aka soma fita ga guda yana tashi a ko ina. Bin gidan kowa keyi da kallo kafin wata mai zakin murya ta sake sake guda da habaici lokaci guda da sauri wanda ke tsaron gidan ya garzayo yana fadin sannun ku da zuwa. Ikon Allah gwaggo ke fada tana fitowa yayin da suka zagayo a bangaren da nake zaune cikin motan gwaggo kudidi ta karaso ta bude bangaren da nake zaune naji gwaggo amina tace dakata da ita. Wanan gidan fa kamar babu kowa a cikin sa kudidi sai nake ganin kamar ba nan bane ai kuwa nan daine gidan nata wata daga cikin yan uwanshi ta fada daga bayan su. Inaga a nan zata zauna ita wancan dayan gidan kuma uwargida ke ciki tare da yan uwanta koni na dauka ai a gida daya zasu zauna tare sai naga an nufo nan yanzu. Bin gidan sukayi da kallo kafin gwaggo Asiya tace dankari gwaggo haro tace bari kedai anty na aini nayi shiru ga baki daya wallahi. Da sauri daya daga cikin yan rakiyan mu daga lagos ta iso dauke da buta a hannunta tare da sabon kafet din sallah magana tayiwa su gwaggp akan zanyi alwala nayi nafila kafin na shiga gidan ga yadda al,adansu yake. Allah ya taimaka sai mere baki gwaggo sukayi don jikin su ya mutu a lokacin suka kauce na fito daga motar da taimakonta nan suka nuna min gefe na tsuguna na daura alwala kafin na gama sun shinfida carpet din na hau na tayar da sallah din raka biyu . Kafin na daga hannayena biyu sama inayi suma sunayi da dan karfi duk wanda ke wajen yana amsawa da amin don sunsan addua sukeyi duk da hakan ya zama bakon lamari a wajen su kuma. Kafin na shafa tare dasu sai lokacin wani kuka yazo min suka fara addua tare da rike min hannu kaina a kasa ina kuka wiwi zuwa cikin gidan da aka riga aka budeshi ko tun shigowan mu get din gidan. Duk wani wanda ke wajen a lokacin na bashi tausayi dan yadda nake kuka wiwi zuwa cikin gidan a daidai shiga kofan suka tsayar dani . Kafin su fara da hasbunallahu wani, imal wakil kamar a waka baka jin komai sai muryoyin su a haraban gidan lokacin.