← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 184 OF 337

Sashe 184

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gidaba ma balle ka gansu a yanzu ? Mikewa yayi yana fadin shi zai tafi amma dan uwan nasa yadai kara dubawa kan wanan shawaran daya kawo a karshe. Bai dago kai ya kalleshi ba kawai yasa kai ya fita sai lokacin ya bishi da harara yaci arzikin uwarsu daya da kuma abinda inna ta fada da zata mutu da ranan yasan koshi waye shima. Dan nasa ya dannawa kira a waya tare da tambayab kana inane yace gani nan zan tafi tudun wada kazo ina son hanin ka ya fadawa dan nasa. Idan mun fita umma takan kunna kira,a ya tayata hira tana bin karatun haka na dawo na sameta ita kadai a gidan . Gaida umma kawai nayi na fada saman kujera tare da dafe goshina da hannuna daya na lumshe idanuna ina tunane. Ganin haka umma ta kira sunana na dago kai na dan kalleta kafin na cire hannun ina kaiwa kwance nace umma yau nayi waya da wanan mutumin . Wani mutumi kenan fa umma ta tambayeni na sake fadin wanan Alh Nuhun wan mahaifin mu a ina kika ganshi ta tambaya cikin mamaki ? Dagowa nayi daga kwancen da nake ina fadin kusan kudin company da muke nema yana a hannun su sun rike haka bincikena ya nuna min. Saidai ban yarda munyi magana dashi a yau na fada mai ya jira har lokacin haduwan mu dashi yayi. Haka kikace dashi nace kwarai umma ban shirya haduwan mu dashi a yanzu don haka ba zan tsaya magana dashi ba ko mai zai fada min kuwa. Kibi a sannu don mutanen nan basu da kirki ko kadan sanin koke waye a garesu yanzu zai kara saka masu tsanarki a zukatan su . Da ace tun farko nasan suna cikim zancen nan babu abinda zaisa na yarda ki fara aikin nan mai yawan kasada a rayuwan ki yanzu. Nasan da hakan umma nima saida muka zo din nafara bincikene na gano dasunan shi da wasuma da bamu zata ba a cikin wanan harkan. Allah dai ya shige muna gaba nace amin muka dayi shiru kafin ta dago tana fadin dazun yayan ku yazo ya kawo muna goro da alawan bukin Baby da za ayi. Na dago ina fadin yaushe yazo tace dazun nan bai dade da tafiya ba kuka dawo ya karbi takardan nan dayace zai duba ranan dake waje na. Da sauri na dago kai ina fadin umma ya tafi dashine tace a,a yadai duba ya ban ajiyan zuciya na sauke tare da lumshe idanuwana . Kafin in dago ina fadin umma ban takardan in duba in gani yau din nan ba bata lokaci ta mike ta dauko min ta kawo min. Mikewa nayi dashi zuwa dakina na kwanta na fara karantawa a tsanake ina bin rubutun mahaifin namu da kallo da yadda yake tsara rubutun shi. Da gani basai an fadama mai ilimi bane shi don irin turacin dake cikin takardan lokacin idona lumshe saiga hawaye sun zobo min a hankali nagoge. Bayanin irin rayuwan da yake ganine a cikin yan uwanshi sai bayani kan rayuwan shi har neman gwago hari da hanashin da akayi ita kafin ya dawo ya samu tayi aure. Sai kuma irin ci gaban daya samu da aikin daya fara da CBN tare da business din da yakeyi kafin in budo wani shafi daya rubutawa rayuwa mai kunci da takaici . A wanan shafin kafin na karanta nayi kuka nayi kuka mai tsuma zuciya sosai ni kadai a daki don abinda na karanta a cikin takardan sharfi ne kan irin barazana da matsi daya fara gani daga yan uwan haihuwan shi. Ban fito dakin nan ba saidana karanta wanan kudin sai tsakar dare na fito neman abinda zanciwa cikina lokacin. Babu kowa a falon don dare yayi sosai a lokacin haka yasa nayi amfani da wayan hannuna wurin ganin haske a falon har na samu na debo abincin na dawo na fara ci a cikin duhu. Naci kamar cibi hudu na dagata don motsin dana faraji a haraban namu duk da suna da nisa sosai da inda gidajen mu suke amma hakan bai hanani jin takon suba kuma na gane an shigo wurin namu lokacin. A hankali na taka zuwa inda window falon mu yake numfashina naja sai na zabura kafin a mayar dani na furta wani abinda bansan na furtashi ba lokacin. Na koma na kwanta abincin da banci ba ke nan kuma saida safe don kwanciya nayi dan wani irin barci daya ziryaci idona a lokacin mai nauyi. Kamar a cikin mafalki take jin ihun yar ta dake dakin ta kwance kusa da ita zabura tayi don jin ihun yar natane dai ba wani a lokacin daga ita sai daura gaba a jikin ta tanufi dakin a gigice take lokacin. Tura kofan tayi da karfi a daidai lokacin da sauran mutanen gidan suma suka fito don jin ihun daya karade gidan nasu a lokacin shima kanshi maigidan a rude daga shi sai dan short irin na maza katon cikin sa a waje ya karaso dakin a gigice . Abinda kowa yagani nr yake sasu komawa baya da sauri suna salati ga makwabta a lokacin har sun fara fitowa don ba karamin ihu yarinyar takeyi ba yana bin dare. Innalillahi Alh ya ambata tare da fadin Sanda kanka daya kuwa da hankalin ka kuwa kasan abinda kake kokarin aikawa ga kanawarka a yanzu. Baya cikin hankalin shi don haka bai jin tsawan da mahaifin nasa da sauran yan uwanshi ke masa a lokacin. Ganin zasu tsaya ya illanta mata yarta yasa uwar yin kundunbala ta fada ciki ta fincikoshi da karfi hakan yasa yaranta maza biyu suma suka taimaka mata wurin bambare shi sukaja yar uwansu tare da yaba mata zani da sauri a jikin ta. Aiko binta yayi bayan mahaifiyar nata yana kokatin jawota ala dole sai yakai a jikinta kamar yadda aka umurce shi yaje yayi din. Alh da baisan matakin dauka ba a lokacin nufar dan yayi ya kifa masa mari uku masu kyau rai bace ya fara magana yana fadin. Don ubanka ka shiga hankalinka mana ko nan cikin gidana aka turaka kayi wanan aika aikan da zakazo kana neman hakewa yar uwanka haka ? Jajjayen idanuwan shi da suka rine suka sauya halita don kana ganin shi kasan baya a hayacin shi gabaki daya yayi wani irin gumji ya juya yana kokarin cakumo yar dake makale a jikin uwarta yan uwanta sun masu kariya a lokacin. Kai ranan nan dai ahalin gidan sunga tashin hankali don haka ya koma kamar mahaukaci saida aka ja yar a cikin dubara zuwa wani daki aka boye ta shi kuma maza sukai waje dashi don a samu natsa shi . Alh ne yace a kawoshi falon shi kafin ya shiga wani daki ya debo wani abu da hayaki yana yayyafawa dan nasa dake rike ahannun mutane. Haka gari ya waye kafin kace meye labarin hakan ya fara karade unguwa zuwa cikin gari har aka samu masu kari a zancen suka gyara labarin tare da kwaskwarima don zancen yayi dadin ji da bayarwa. Irin barcin da nayi ranan bana kau sake bane don da kyar na iya tashi nayi sallah kuma na kwanta a wurin sai karfe daya saura na falka na shiga wanka tare da dauro alwala na fito. Tsab na shirya na fito umma tayi mamakin hakan nace zan leka na dawo don ban san irin barcin da nayi ranan ba. Na isa wurin aiki sai bina da kallon akayi niko ko in kula da irin kallon da suke min din kai tsaye na shige inda muke aikin mu. Duk Sunyi mamakin ganina a lokacin niko ko in kula da hakan na zauna na bude laptop dina na fara aiki a cikin sa bayan gaisuwa ban kara magana da kowa ba a wurin sai kai da nake kadawa idan wani yayi min wani tambaya. Aiki nayi sosai a ranan don har kusan biyar na yamma ina cikin ma,aikatan lafin na nade nu,uran na fito zuwa gida. Ko a gidan ma bana magana Abdulhamid umma ta sama take fada mai halinda nake ciki shida matar shi suka biyo umma zuwa gidan. Duk yadda sukaso nayi magana banda bakin hakan karshema na barsu a falon na shige ciki don kallo daya zakaimun kagane ba a cikin hayacina nake ba lokacin. Hankali tashe aka kira Nazifa da sassafe ana sheda mata abinda ke faruwa a gidan kan yan uwanta. Kukata saka a wajen hakan ya jawo hankalin mijin nata dake execise a lokacin ya fito yana tambayan ta abinda ya faru take wanan kukan haka. Kasa fada mashi tayi don bata san me zata fada maiba a lokacin don maganan nada nauyin fada a bakin ta. Daya matsa sai cewa tayi dashi gidan mune ba lafiya wai suna asibiti da safiya da ya umar cikin mamaki ya kara tambayanta da meya samesu haka lokaci guda tace saidai idan naje zanji. Ga mamakinta sai taji yace da ita ki jirani muje tare mu gano su yanzu Allah dai yasa ba wani abu sukaci da yajawo masu kwanciya asibitin ba haka lokaci guda. Ai kuwa dai taren sukaje suka samu yan gidan cirko cirko a haraban asibitin kowa ransa a bace ana ganin su hanlalin kowa ya koma garesu. Bayan sun gaisa dasune yake tambayan su cikin son jin abinda ya samesu din sai kowa yayi shiru yana dukar da kanshi kasa lokaci guda. Da yake yasan kanshi bai matsa masu ba ya wuce zuwa ciki ya kai tsaye don ya tambayi likita abinda ke samun su din ? Saidai baikai ga shiga ba a bayan filawan dake wajen yaji muryan kawun nasa na waya yana fadin wallahi akwai matsala babba Alh ina fada maka. Gaba daya hankalina a tashe yake don wanan abin ana ganin shi karamin magana yana son ya zamo muna babbba a garin nan. Don gaba daya yarinyar nan tana son juya muna hankali tayi muna wasa da hankali wai yaron dana tura ya gama da ita jiya shine ya dawo ga kanwarsa haukace yana neman aika abinda na umurceshi dayaje yai mata a can. Sahiba kawai ya anyana a zuciyar shi lokaci guda haka yasa ya juya bai shiga ba don ya gama jin komai a inda ya
Chapter 184 · 0% Book details