← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 337

Sashe 48

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

see dis small girl no someti like magic kafin tace wani abu nace make give u dis for free ur hair go grow dan dis u will look anty yayalash if ur hair start growing. Ta farkom tace No give me d one my oga die for me, on bed, if we are making sex ido na dan rufe kafin in tuna da wanda ya ban yace na wanan harkan ne. Nace if u user am today, tomorrow u will, come back, to look for me, for anoda one, tace oya make u give me dat one, a daidai lokacin kuma motocin dake gaban su suka fara muna horn su basu hanya don haka muka dan gusa kadan suka sake kirana a takaice dubu goma na samu a hannun wa yan nan matan don wanan abin. Wasa wasa ina tallatawa wasu su zageni su koreni wasu kuma su kirani su saya sai gashi zuwa yamma na hada kudi mai yawa ga wanan tallan maganin. Jin dadin hakan yasa na ware dubu uku daga ciki don irin riban dana samu ta wanan sana,an naba wanan tsohon daya ban maganin na tallata . Shi kuma jin dadin hakan yasa ya zaunar dani yana min bayanin yadda sa,anan nasu yake da abubuwan da yake amfani na kwarai da wanda baida karfi.. Anan na shiririce wurin sa ina daukam ilimi ice da ganye wurin tsohon bahaushe din . A karshe nace ya kara ban sari don gobe ba zan shigo wanan unguwan ba wani wuri zan nufa shima kuma na bashi shawaran ya gwada hakan yace zai gwada insha Allah don nan kawai ya sani yasa yake zama a wurin har nomban wayan shi na karba don kira idan wani abu ya kakare min a rayuwa. Ga wanda ya ban yace nayi amfani dasu don tsari don sana,an sai kaci ka koshi ake sanin ka ni duk ban damu da hakan ba . Ni kawai naga wurin samun kudi na karba nayi godiya tare da sallama na kama hanyar komawa unguwan mu da yamma lis sai dare na isa gida da dan kumshin kayana a cikin buhun siminti. Duk da warim ganyen da sake saki da umma keji bata tsaya tambayana ko me na dauko ba a lokacin har saida na gama abinci da naman kai dana kwaso muna a gidan. Wanka na fara yi kafin in fito in zauna muci abincin sai bayan mun gama umma take tambayana abinda na dauko a cikin buhu. Hannu na tura a cikin kwagiri da ban yarda in ajeshi ko a dakin mune don masu shigowa dakin na fito da damin kudin da zaikai dubu ashirin da dan kai . Na fara bawa umma labarin duk abinda ya faru a ranan jikin umma yayi sanyi sosai take fadin bana tsoro nace da zuciya daya na karbi wanan sana,an nan dai da daren na fara yan hayakin da tsohon nan ya ban nasha nasha. Barci nayi ranan sosai har da makara saida umma ta tayar dani don makara agurguje nayi komai diban ruwa ne naso makara don layin dana samu a wurin. Nagama na shirya na fita haka nake samun alheri a wanan harka sosai don sukan sun yi amanna da maganin gargajiya so sai a garin. Har ya kai na hada da irin nasu dana sara a wurin wata mata da na yan ghana ina sayarwa ina kuma samun alheri ga hakan tsohuwar bayeraban cema taso kawo min matsala sai da zan tafi kome ta gani kuma ta ban sari na hada ina yawatawa ana saye kuma sosai. Duk ban sani ba tun ranan Chiku yana biye dani duk inda na saka kafa yana ba ogan shi bayani a kaina. Saidai ogan baya gari yasa baiyi wani kwakwaran motsin da zan iya gane hakan ba ina harkoki na don har gidan mu a yanzu ya sani yasan lokacin fitina da dawowa na gida. Haka rayuwa taci gaba da tafiya har na tsawon makoni ina hatkokina na sayar da magani da yanzu yafi min komai kawo kudi don har an fara sanina ga wanan harkan . Saidai inda nake samun matsala shine wurin sayar da maganin maza saboda wasu yan iskan zasu iya ma maganan banza amma haka nake matse fuska ina saida masu shi. Duk abindake wakana tana ji daga part din ta don Alh Nuhu har ciki ya shigo ya karewa hjy Addah fada dk bai samu miji su da yayi tafiya a gida ba lokacin. Wani irn shu,umin dariya ta sake dataji fitan shi yanawa kanwar tashi warning kan lalai dan nasu ya dawo gun matar shi watau yar su zuwa gobe in ba haka ba su hadu da fushin shi dukkan su. Son tun lokacin da yar tasa ta bugo mai waya tana kuka a cikin dare tana fadin Abba Abubakar ya cuceni yaci amanata ashe dama da gaske ba son auren mu yake dani ba gashi yana shirin mayar dani karamar bazawara a yanzu. Ke ke Nazifa ki kwantar da hankalin ki kimun magana yadda zan fahince ki Alh Nuhu ya fada cikin dakatar da yar tasa lokaci guda don duk son da yake masu bai hana inta baci ya tsawatawa diyan nasa kan abinda sukeyi. Ki kwantar da hankalin ki ki fada min abindake faruwa ya fada a dan hasale don kukan nata yana taba mashi zuciyar shi. Don akwaishi da son diyan shi har bai iya boye haka a gaban kowa waye don son kai da yake dashi balle ita Nazifa da yar yar gaban goshin sace sunga wurin ci ne ga Abubakar din suka dauki yar suka bashi. Lokacin da wanan zancen nason hadi da diyan shi yazo masa don shi bai amince da irin wanan hadin auren da iyayye da kakanni suka bar masuyi ba a yanzu. Don shi ya fara aurawa diyan shi bare na waje wanda basu da alaka na jini dasu don bai yarda da hadin nan ba a karshe yarinya taje tana wahala. Kuka take sosai rake labartawa mahaifin nata abinda ke faruwa tun bayan tafiyan Abubakar din wai ko wayan ta idan ta kirashi yanzu baya dauka. Ga dan iskan yaro Alh Nuhu ya fada yana fadin shi din me shi din banza ni ina da wani manufa akan shi tasa na yarda na bashi auren ki don kar ya dauka ko wani abu yake dashi da har zai fara wullakanta min ke a yanzu. Wani iri Nazifa taji da zagin da mahaifin nata yayiwa Abubakar din a yanzu don da Alh Nuhu yasan yadda a yanzu take son guy din da bai furta haka a gaban ta ba taji. Don tun asali tana son Abubakar din har kasan ranta ahiyasa ma tayi amanna da aure ba tare datayi gardama ga iyayyen nata ba. Don a yanzu data dandana ko waye Abubakar din jinshi take shine komai nata shine ma kamar rayuwan ta gaba daya a yadda take jin shi a cikin ranta a yanzu. Amma jin kalamin daddy su sai take ta dan sauko ba kunya take fadin daddy kayi mai magana kawai ya tafi dani ko ya dawo. Allah daddy gidan nan yai min girma da bashi a cikin sa kuma kasan ni ban saba da zama haka ni kadai ba. Abban nasu ya fahinci halin da yar nasu ke ciki a yanzu yasa ya dan sauko ga yadda yake jin zafin wullakanta masa ya da Abubakar din ke shirin yi a yanzu shine yaje gidan su hjy Addah tun da faran safiya ya buga gida suka tashi ya shiga yayi mata masifa ya fito sai gidan yar nasa kuma can yaje ya karbi wayan ta ya kira mijin nata ya zuba mai tunda safe. Dole hjy Addah ta kira dan nata cikin bacin rai tayi masa fada sosai tare da umuratan shi akan kome yake ya dawo gida zuwa gobe. Wanan dalilin yasa ya taso don ya fahinci ran mahaifiyar nasu a bace yake kuma koda bata fada mai ba ya gane Alh Nuhu yaje ke nan yayi mata barazana irin wanda yayi mashi shima da safe. Don haka ya shirya ya dawo kaduna din don mahaifiyar tasu ba don wani ba can yace a zuciyar shi. Yayin da hjy karima kuma ta shige sakewa hjy din arashi a yinin ranan kan auren dan nata tana fasin mutum ya daukowa kansa alalkakai don son kai ko tace gamu gani rashe ya na shirin juyewa da mijiya idan mutum yace son kai ya iya shi. Wanan dalilin tafiyan nasa yasa ua dakatar da duk wani shiri da yake dashi duk da kiran da chiku yayi mai ya sheda mai ya gano wasu abubuwa a tare dani a yanzu.
Chapter 48 · 0% Book details