← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 260 OF 337

Sashe 260

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

asalima munzo ne don mu roke ku gafaran abinda ya faru mukayi maku gaisuwan rashin mahaifi dan uwa jigo a garemu watau mahaifin ku. Wani kallo na jefo mai dan yan kan na kiris su tashi min a lokacin badon gyaran Allah ba jifa wai gaisauwa sukazo yi muna na mahaifin mu a yau din nan. Kamar yasan abinda nake kallon su dashi naji yace don a lokacin da abin ya faru munzo daga can Hong Kong inda ya barmu da niyar zaizo yayi aiki a nan sai labarin mutuwan shine ya rikemu. Munzo mun nemi dcp Ali lokacin don shi mukafi sani a cikin yanshi amma sai ya dauka wani abune na daban ya kawomu gareshi lokacin . Don ya zaci munzo kan wani zancen kudine ko wani abu da zamu karba a wajen marigayi din mun nemi mu ganku sai aka fada muna kuma wai kun bata. Wanan zancen ya daure muna kai a karshe dai haka muka gaji muka koma ba tare da mun gane komai ba akan ku wurin su sai gashi lokacin da kuka fara wanan case kwatsam labari ya riske mu. Yasa na turo a tsayawa case din sai kuma naji ance wai ke kince kin yafe komai daga garesu illa fili kawai kuke so a baku. Ni kuma nace ban yarda ba a yanzu komai da suke ganin sun sameshi a yanzu sai sun mayar dashi ko kuma su hadu da mumunan fushi a garemu. Musan wanda ya mutu lokacin sane yayi amma ta sanadin su ya tafi don haka mu a wurin mu sune suka kashe shi don haka muma iyalan shi ba zamu kyalesu ba a yanzu da gaskiya ya fito. Fuskan shi ko muryan shi nake kallo a lokacin na rasa wani daga ciki ya dauke min hankalina haka ? Saidai maganan shi na karshe da yayi cewa su iyalan Abban mu ba zasu kyale a yanzu ba yasa naji wanan kalamin a wani bambarakwai. Su iyalin shi ta ina ya akayi suka zama iyalin shi din yanzu don haka duk wanda zai kiraku akan waye ya daukaka kara a babban kotun Abuja kuce dashi. Babban yaron shine mukhatar usman marwa ya daukaka kara a yanzu don ku kungama naku fanin an gani yanzu nawa fanin ne wanan . Ku gafarce zance a karshe dani da abokina na rashin zuwa gareku a lokacin daya dace ace munzo mun taimaka maku alokacin da kuke cikin wahalan rayuwa. Duk da hakan ba laifin mu bane an boye muna komai daya shafe kune a lokacin don haka kada ku zargemu da laifin hakan gare ku. Da fatan zaku fahince mu don Allah ku yafe muna kan abinda son zuciyar wasu yasa muka aikata maku na rashin zuwa gareku na tsawon lokaci. Saiya dukar da kai yasa kyale yana sharan hawayen dake zubo mai lokacin a idon shi ganin hakan yasa na juya zuwa dakina da sauri. Saman godo na fada ina wani kuka mai tsuma zuciya kafin na koma tunane alokacin don ina ganin mu munfi kowa matsala aduniyan nan. Daga wanan zuwa wanan matsalan sai yaush ne zamu koma kamar kowa mu shiga yan uwa muma mu san muna da dangi kamar kowa a duniya ? Sallaman su na fara ji suna ma umma sallama hakan baisa na fito ba har yakai na daina jin muryoyin su a falon namu haka yasa na gane cewa mu kadaine a gidan lokacin. Ban fito falon ba sai safe na tashi don zuwa wurin aiki har lokacin akwai rashin walwala ga umma dole na tsaya naga ta karya kumallo. Bayan mun gama karyawa ne na mike naje na shirya sallama nayiwa umma na fita zuwa aiki misalin sha daya rana sai ga wayam umma ya shigo mmin
Chapter 260 · 0% Book details