← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 253 OF 337

Sashe 253

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Taben da lauyan mu yayine ya dawo da hankalin kowa a kotun aka dan rage surutun da akeyi a lokacin kowa na fadin ra,ayin shi. Kallon su akeyi yana kallon daddy yana murmushi har ya isa wurin shi ya tsaya yana dan jijiga kai. Ya kalli daddy din yace well Alh kotu taji bayanin ka a yanzu saidai idan ba damuwa akwai dan tambayoyin da nake son in maka. Yana fadi fuskan shi a wurin alkalin dake zaune yana dan rubutu a lokacin a farar takarda daya dauke mai hankali ya gyada kai alaman an baka. Ya dubi Alh yace Alh a cikin bayanin ka naji kace kun sami sabani da marigayin akan wani abu nasa lokacin ko zaka iya fadawa kotu abinda ya jawo maku wanan matsalan. Sai a lokacin ne aka san ya shigo dame kareshi a kotun ya daga yana gabatar da kanshi tare da fadin wanan tambayan ai an wuce wurin tunda yayi bayani ko . Alkali ya daga mai hannu alaman ya bari a tambayi daddy din ya koma ya zauna shi kuma yaci gaba da kallon daddy din yana sauraren shi. Daddy ya gyara tsayi yana fadin eh to a lokacin dai daya ban ajiyan ya kawo min shawara naji rejecting to ba wani abu bane illa nayi amfani da kudin wurin gina wani wuri a garin lagos a lokacin. Inda ya nuna min don me zan masa hakan bayan ga kudirin shi nason ya gina gidajen mai shine burin shi. To mu a nan marigayin yayi bayani a takardan sirin shi cewa ka bashi mamaki don ka dauki kudin shi da yake da buri ka gina babban hotel a garin ikko na kanka dashi. Haka abin yake ko kuma kana da abin fadi a nan dan murmushi daddy ya sake a fuskan shi yace shine dalilin fadan namu dashi. Dama nasan idan na fada mai hotel zan gina don yafi wanan burin nasa da make ganin shirmene a lokacin ba zai taba yarda da hakan ba. Don shine ma ya nuna min baida ra,ayin gina hotel a rayuwan shi don irin abubuwan da za a aikata a ciki. Amma sai naga rashin wayaushi nabi baya nina gina a kashin kaina sai wanan yayi matukar batawa shi sambo din rai sosai har yakai ga furta min kalami da fadin. Brother kana ganin kamar ka cuceni ne ni kadai to kasani kanka ka cuta da wanan abin dakai min don bani kadai ka cuta da hakan ba. Fadin hakan sai naji raina ya baci dashi nace yau ni kake fadawa haka sambo akan dukiyan ka sai ya kalleni yayi murmushi bayan ya mike yana fadin. Ka bani mamaki sosai brother ban taba zaton kai zaka iya yin wanan abin na sonkai ba gareni . Anan lauyan ya tare shi da fadin sai kace dashi me kai kuma kallon lauyan daddy yayi kafin yace naji haushi sosai a lokacin yasa nace dashi akan kudin da bamu tabbatar da ida ka samoshi ba har kake kokatin min rashin kunya. Idan bakai hankali ba sai na saka an bincike ka inda kake samun dukiyan ka haka sai me kuma ya baka amsa lauyan ya tambaya ? Daddy yayi shiru idan ba laifi zan fadi abinda marigayin yace maka lokacin ya kalli alkali ya daga mai kai alama go ahead gareshi. Kaika sani duk inda haram yake bana wajen kada kudi ko dukiya ya rufe ma ido ka dawo kana dana sanin hakan a baya. Hakane ko Alh lauyan ya tambayi daddy din shiru daddy yayi yana fadin yaron nan abinda yai min ke nan lalai hurda damai ilimi yana da wahalan fahinta yafada a ranshi. Na fada daidai ko lauyan ya tambaye shi sai kai kuma kaji haushin mayar maka da hakan da yayi yasa ka dauki alkawarin baiyanawa yan uwan shi duk sirin shi daka sani ko. Wanan ke nan ya wuce wurin ya koma fadin sai zance na biyu shine ko Alh zai fadawa koto inda wanan dukiyan na baya suke yanzu bayan mutuwan mai ita ? Eh to gaskiya zance ni kadai nasan inda kudin sambo yake a lokacin amma sanin kowa yasan ya dawo da wani abu mai muhinmanci wanan tafiyan. Shine na fadama sun sameni a gida kan wanan kudin muka bincika kudin suna nan yadda ya ajesu a bankin shi . To a wanan lokacin muka fito da kudin muka rabashi a tsakanin mu har wurin rabon yaso ya kawo muna rikici a tsakanin mu wanda har wanan lokacin muna rike da wanan zancen. Ko Alh zai iya fada muna abinda kowa ya samu a cikin kason objection my lord dayan lauyan ya fada lokacin dana gimtse idona dake fitar da hawayen bakin ciki. Wanan wani irin rashin kaunane da rashim imani sukaiwa mahaifin mu haka yan uwanka na jini bako bare ba sai kace basu san inda ya fito ba wanan irin son kai da suka nuna mashi. Ashe gaskiyane da ake fadin kiyayya ta asali bata goguwa a zukatan makiya kome ko zakai masu sai ranan da sukaga kanka a kasa koshi idan yana motsi basu barin ka sai ya daina matsin. Saidai su wa yan nan sun kashe macijine basu samu sare kan shiba da ace sun sanda hakan duk inda muka shiga cikin duniyan nan Allah nuhu sai ya nemo umma damu ya halakamu a lokacin. Dukda abune mai wuya irin nisan shakon da umma tayi zuwa semi boda Allah kadaine ya gyara bata tsalaka kwatano damu ba a lokacin. Ko can din take zai iya zuwa ko ya tura akashemu da ace yasan da hakan a lokacin Allah ne kawai zai kwacemu a hannun shi. Duk yadda lauyan mu yaso yakai daddy makura saboda yasan logon sharia ya kasa kayar da daddy a ranan don iya duniyama. Sai rokom kotu da daddy yayi kan cewa yana son kotu ya bashi dama ya halartawa iyalan mamacin dukiyan su a hannun su dake wajen shi tunda yanzu lokacin hakan yayi. Jin hakan yasa na dago idona ina kallon daddy din wanda ni kaina bazance ga irin kallon da nake masa ba lokacin kamar ance na duba gefena ya Abubakar ne zaune dasu baffa hamza a kujera guda. Idona a cikin nasa alaman daga kai yayi man wanda ban fahinci nufin shi ba a lokacin sai muryan mai bayanin kotun dake fadin ko zamuga wace ke kara muji na bakin ta a yanzu. Duban inda nake mutane keyi ranan dai shiga shigen na hausawane duba da inda muka fito yola yasa nasaka atamfa amma buje da riga matsatsu da suka kame jikina sosai. Gyalen dake saman cinyana na dauka na dora a kafada don gaskiya babu wani zancen hijjab a gareni don ban saba sakawa ba tun ina karama. Wanan yasa ko a yanzun niko a jikina hakana tashi tinkis tinkis dani suka bini da kallo masu tausayi na tausayawa masu jin haushi naji hakama masu mamakin mu a wurin. Daga yanayina zaka gane a gajiye nake ko kuma cikin wani yanayi na daban can mai nuna rashin jin dadi a gareni nazo na tsaya a inda ake tsayawa din lauyan ya kalleni yace dani. Shabi u hear what he said now ? Waitin he talk na sake jefo mashi tambayan nima a wahalce yace dani kan dukiyan mahaifin ku dake hannun shi da yake son ya danka maku su a yanzu. Which kind of wealth he dey talk now i beg may he forget about dem shaaa. Ni a yanzu kawai bukatana garesu shine su sakar muna mara muyi rayuwa kamar kowa ina son kotu ta kafa muna sheda damu dasu akan duk abinda ya shafi rayuwan mu a yanzu sune. Aiko nan kotu ya dauki hayaniya masu dariya nayi irin yadda nayi maganan zakace ni din wata tsohuwar bayerabiya dani ga kuma na nuna ba dukiyan bane a gabanmu mu. Shima kanshi lauyan dariya na bashi sosai yayi dan murmushi yana girgiza kanshi dan abin ya bashi mamaki matuka nace yes now. We no wan de money and erverything daya fito a wurin kowa daga garin nan tunda ba zasu dawo muna da mahaifin mu ba su rike komai mun yafe mu. Aikuwa kamar mutane su cinyeni danye don abindana fada ina kuka ina share hawaye har alkali yaita dukan gudumar shi wurin yai shiru ya dukar da kanshi yana rubutu kafin ya dago yayi gyaran murya aka kara natsuwa sosai ana saurarenin. A nazarin kotu a bisa tsarun da doka ya shimfida ya zama dole wa,yanda ake tuhuma su gagauta dawo da duk abinda suka wawasa na daga dukiyan mamacin ba tare dako kwandala ya bata ba a cikin shi kamar yadda ya rubuta dukiyan shi a tsare ya bari. Nan aka shiga jero masu abubuwan daga ciki har da gidaje da filaye kiwon shanu motoci da sauran abubuwan amfani na gida. In boni handi yoooo Alh gyade ya fada yana zubewa kasa tare da fadin Nuhu kai shushe mu ka shuci rayuwan mu kace muci ba a komai ya gashi zan tashi ko kwandala bandashi a duniya. A take kotun ya rikice da koke koken diyan su dana yan uwa kowa da gefen da yake bi a cikin su yayin da Alh nuhu yayi tsayuwan da baisan inda yake ba a lokacin. Alkali yaci gaba da bayani bayan haka kotu ta yanke hukuncin Alh Ali dcp taran naira miliyan ashirin ga magadan don kamashi da cin amanan mamacin da kuma sassaucin dauri na shekara daya ko taran naira miliyan biyar ga kotu. Haka kuma zai iya daga karan idan hakan bai mashi ba yaje gaba iya abinda kotu zata yanke yanzu ke nan kan Ali dcp. Sai su Alh nuhu da zasu mika komai da suka mallaka ga ko magadan su haka kuma zasu fuskanci daurin mara sassauci da tara ga kotu kan kisan dan uwan su da sukayi. Shi buhari ya wanke kotu ta bata kamashi da laifi asalima an yaudare shi anyi amfani dashi anje kissa an kuma boye mashi hakan. Jarrr kaniya Alh nuhu ya fada da karfi kowa dake cikin kotun hankali ya koma akanshi lokaci guda ya fara fadin akan Sambo za ai min daurin rai da rai a gidan wakafi. Kana da daman daga kara idan sharian mu bai gamsheka
Chapter 253 · 0% Book details