Sashe 263
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
sansu a wurin ba gaisuwan sama sama nayi masu na nufi wurin motata dake aje. A fakaice yake satan kallon yanayina nayi dan duhu na rame ga yadda yasanni a baya duk da yanayina ya nuna akwai damuwa a gareni daka kalleni. Karfe da tsiya duk saurin da nakeyi sai gashi na shiga taki tashi kuma lafiya kalau nazo da ita wurin aikin ganin yadda nake fama da motan ya turo min wani kan cewa na fito nabar motan a duba min za a sameni gida dashi idan an duba. Dole motan shi nafito NB a shiga drivern shi na nan lagos ya kaini gida saidai isata gidan kuma na samu wani labari mara dadi wai an kulle su daddy a abuja daga sunan yi masu tambayoyi aka rike su a can gaba dayan su. Banji dadin jin wanan labarin ba duk da sun cancanci hakan koma fiye da hakan kawai dai barin su a yanzu shine karin rufin asirin family din mu baki daya duk da duniya ta riga tasan da komai. Don haka zaisa a karshe yan uwa da yawa daga cikinsu su koma marayu kamar yadda muma muka taso marayu din a yanzu wata sharian sai a lahira. Ni kaina yanzu idan ina wani abin har mamakin kaina nakeyi kamar ba Sahiban dana taso da hayakin kai bace a baya yanzu. Tun zuwan ganin gida yola danaga irin halin rayuwan da suke ciki a can da kuma irin hudan da suke muna ga kuma taimakon laluran dake kaina da wani kakan mu ya bani nayi amfani dashi tun can sai abubuwan da nakeyi na rawan kai yanzu suka rage min sosai. Yanzu kan hankalin kowa kusan a tashe yake don ko ta fanin daddy wanan tsare shin da akayi din har ana masu rade,radin cewa suma za a zo a rufe nasu gidan hakan ya kara tayar da hankalin iyalin daddy din sosai wanan lokacin. Ga bangaren hjy karima yakai baby ta dawo gida don fitinan da sukayi da kanwar mijin ta kan abinci mijin kuma na dawowa gida bai tsaya bincike ba ya hau baby din da duka . Wai don me zata hanawa yan uwan shi abinci tayi masu wullakamci kan abinci shida gidan shi. Ko ubanta Ali dcp bai isa ya hanashi yiwa yan uwan shi abinsh ba balle ita yar gadon mugun abu kawai ita kuma tace ai duk su dine yan gadon mugun abu. Shida mahaifin shi suka yanka dan uwan su yakan rago saboda rashin imani nan suka taru dashi da kanen shi dake gidan suka linkida mata kashi da kyar ta samu makwabtan su suka shigo suka kwace ta daga hannun su. Shine ta dawo gida don jinya saboda taji jiki sosai hjy karima a yanzu tayi data sanin hada zuri,a dasu abinda daddy ke mata gudu ke nan ashe ta kasa fahintar shi. Sai yanzu take gane abin bayan an makara kuma ga karamin ciki dake jikin ta yanzu babu yadda zasuyi yanzu da ba cikin nan ita kawai data kashe auren kowa ya huta hakana yarta ta koma makaranta a yanzu tun bai batawa yarinyar lokaci ba. Saida kyat modibbo ya lalashe ta tayarda don da tace duk abinda za ayi ayi sai ta zubar da cikin jikin baby din cikin hasala. Can gidam gwaggo hari kuma ta kasa gane kan danta sai dai idan ta tambayeshi yace mata babu komai gashi bai walwala ko kadan a lokaci. Ana haka ya tarkata kayanshi da rana tsaka yace zai tafi shi sam gwago din bata so hakan ba amma ba yadda ta iya dole ta saka mai ido ya tafi. Saidai a zaton ta kafin ya dawo ya manta da komai yasa ta kyaleshi a cikin yanayin da yake din ya tafi kai inbanda abin maza da basu raina mace idan suna aonta. In bashi ba ina zaI kai wanan yarinyar Sahiba da idanuwanta suke a bude karr da duniya haka don haka taja bakin tayi shiru don kada zancen ma ya fita har wani yaji shi.