Sashe 202
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tafe yake cikin tako irin na mazan zamanin da suka san kansu a cikin isa da izza ba sai ya fadi koshi wani bane a wajen wayewan don kallo zaka mashi kawai hakan zai nuna kansa. Ba komai yasashi cicika da shakan iska ba a yau sai zancensu da maminsa data tare shi dashi da safe na wai ga Nabila nan ita take son a hadasu don zumuncin ta da dan uwanta ya kara karfi a tsakanin su bayan na diyar gwaggo Asiya da muka sha biki a baya. A cikin mamaki yake fadin wata Nabila dai mami yana tambaya a cikin mamaki don shi indai Nabilan daddy ce sam bata taba burgeshi ba yarinyar yaji mami din tace Nabila dai yar wurin yayana Aliyu mana daka sani ita nake nufi kasan dai mutane suna fadin dani take kama ko sosai kaima kasani ? And so what mami don kuna kama ai bake din bace don ni bata taba burgeni ba a rayuwan duk da kaman da ake fadi ta dan kwaso ki. Asalima dai ni ban taba jin kowan su yan dangin nan acikin zuciyata ba gaskiya mami na fada maki idan na tashi aure ni da kaina zan kawo maki yarinyar har gidan nan insha Allah amma ni ban faye son wanan aure na hadin da kuke son ayi ba garama idan kai ka gani kace kana son abinka. Jin hakan mami tayo kanshi tayi mai kaca kaca a lokaci har hakan yasa ya guda ya dauki key din motarshi ya fita zuwa hotel yaje can ya kama daki ya wuni a ciki yana barcin shi hankali kwance don sanin gidan nasu yau da taron jamma, a. Sai yanzu daya dawone kuma ya samu iyayyen nasu dukansu biyu kamar hankalin su a tashe yake don yaji mami dake rike da wani flasks a hannun ta tana juyawa take fadin gaskiya Alh abinnan yana da mamaki sosai amma haka kawai yaya sunan zaizo daya da nasu haka. Idan ba diyan marigayi brother bane ta yaya zasu rubuta sunan shi da Sahiba Sambo namadi da Ammar sambo shima dayan ? Jin sunan da mahaifiyar tasu ta kirane yasa ya dago kai yana kaiwa zaune saman kujera ya dago a cikin girgiza don jin abinda mami din ke fadi lokacin yana mata kallon mamaki. Kasa hakkuri yayi yana fadin wace Sahiba dai kuke magana a kansune yanzun mami badai Sahiba dake lagos zaune da kaninta da mahaifiyan ta ba wace tayi zama nan garin gidan daddy shekarun baya ? Wani kallo iyayyen nasa suka jefo mashi mai dauke da tambaya uwar tace kasan sune dama ? Ya dan kada kai kafin yace kwarai kuwa sanima na sosai tun tana karama tana talla a lokacin nasanta a lagos. Sai kuma yai shiru kan abu biyu daya tuna na farko kallon da iyayyen nasa suke mashi sai nabiyu yana son sanin akan me ake maganan su yanzune wai ? Wai dama mami kin sansune wai ? Ya tambaya a cikin mamaki kamar ya nasan sune kake min wanan tambayan hauka a yanzu kuma ? Indai wace kasani ne abaya din itace yanzu ta bullo muna da wani zancen daya dade da shudewa a garemu cewa wai ita din diyar marigayine yayan mu dan gidan Baffa namadi marigayi ne ita. Da wani irin mamaki a fuskan shi ya dan dago daga saman kujeran da yake kai zuwa bakin kujeran yana fadin . mene mami kika fada Sahiba dai da kaninta diyan uncle dai dana sani wanda aka kashe aunguwar mu na farko sai kuma ya koma ya mayar da jikin shi saman kujera da kyau yana lumshe ido kafin can ya budesu yana fadin ? No wander nake ganin yaron nan Abubakar ko yaushe tare dasu wani lokaci ashe yasan irin halakan dake tsakanin sune amma aini basu taba fada min komai ba kan hakan. Kuma is hard inshaga lagos banje wurin su ba don haka kawai Allah ya hada jina dasu don suna da kirki sosai kuma suna ban tausayi abinda ya hadani dasu ke nan tun farko ba wai nasan kosu suwaye a gareku ba. Zuwa lokacin da yake zancen wani irin kallo iyayyen nasa ke mashi a lokacin na mamakin jin abinda yake fada mai kama da almara a bakin shi. Hakan bai dameshi ba yaci gaba da fadin ashe gaskiya duk haduwa uwar da yaran zasu tambayeni ke suce a gaidake sai na dauka kulawane hakan kawai suke nuna min ba tare daya damu da canjin yanayin mahaifiyar tasa ba a lokacin. Wani irin kuka mami din ta fashe dashi tana fadin yanzu dama mairo tana raye ashe su yaya sun sani basu fada muna ba ? Gara da bai fada ba din don karshe sanin ba zaiyi dadi ba a lokacin yanzu ko sunyi sake da alama dan zaki ya girma don ANA DARA GA DARE YAYI NE A YANZU KAN A WANAN GARIN. Gidan Alh Nuhu da shima iyalan shi sun samu kyautan a wurin hjy karima don yan uwa masu ido da kwali ta rabawa kyautan a ranan ba, aba yaku bayi ba wai sai gaba. A babban falon gidan matan shine da yaran su suna rike da gifts din a cikin jimame sai nanata sunan da maida magana kan yadda sunan yazo daya haka. Don su abinda yasa basu yarda wasu nasu bane sunan Ammar din a sanin su ai ya dayace a lokacin kuma sunanta Fatima sunan mahaifiyar shi Sambo din ke nan aka sakawa yar ana kiranta da maamah. Wanan kuma ance sahiba take da Amar shine ya dan rudasu a lokacin don haka basu yarda ba sunane kawai yazo daya dai amma ina aka samo Namadi din kuma shi suke muhawara a kai yazu. Yo idan ita dince ma sai me tunda su basu kula da mutane ba mune zamu bisu haka kawai ai akace sun bar gida muguwa mata kawai duk a ance basu ma raye a yanzu ai. Hjy salma bakanuwace mahaifiyar Nazifa matar ya Abubakar itace ke wanan zancen don a watse a bar maganan don sunyi har ya ishesu a lokacin ta gaji. Guduwa fa tayi don sheri mutuwan mijin ki da yan kwanaki ki kwasa ki gudu ai ta gamu data Allah a can ta mutu a wullakance cikin duniya. Inma yarce bata mutu ba ta dawo wa zai yarda da ita a yanzu tunda bata da shedan hakan kumama ai bata san komai ba yarinyar dake karama sosai a lokacin me zata karas a lokacin. Gyaran muryan maigidan da yakeyi naku natsu gani tafe yasa wasu suka kwasa da gudu wasu kuma suka zauna a tsorace sun kasa gudu lokacin. Sannu suka fara mai suna mikewa bai tsaya ba basujin kuma ya amsa masu ya shige zuwa part din shi kai tsaye. Matan nasa ne suka kalli juna lokaci guda suna fadin kada dai ki fada masa wanan labarin yau son ba zamu sha da dadi ba gidan nan kin sani laifin daba namu ba ya shafemu mai suna Ladi din dake da girki tace waya aikeni aiken fadin mutuwan sarki ba a bakin Ladi ba kan. Daddy ya gama karantawa ya dago kai yana kallon yan uwan haihuwan nasa da matan shi kafin yace tabbas nagani diyan Sambone ba karya sukayi ba . Kafin ya dukar da kai na dan wani lokaci ya dago yana fadin ku koma dakunan ku wanan zancen mazane ai bai shafeku ba. Baffa Abdullahi yace wai naga saboda su akace yar tazo wirin taton a yadda mata suke fada min kafin inzo don ma ban tsaya sauraren suba nayo nan. Su tafi daga baya saji duk yadda akayi daddy ya fada cikin daure fuskan shi lokaci guda haka yasa suka mike hjy karima zuciyar ta na cike da tambayoyi akan hakan banda mommy da tasan komai wanan ranan takejiwa gashi ya fara tunkaran su a yau din nan . Allah ya gani wanan hanin da taiwa yarinyar a ranan dama ya daga mata hankali sosai tunda gabanta ya fadi har lokacin take jin kanta a wani irin yanayi na daban. Modibbo ma ya mike zai bi bayan mahaifan nasa yaji muryan uban na fadin ina kuma zaka ai sai ka tsaya kai masu bayani don shi ya san komai akan ganin su din can Ikko. Ikko suke suka tambaya yace kwarai amma yanzu bansan a inda suke ba tun bayan da nasan ganin nasu ba alheri bane ga ahalin mu ga baki daya nasa ya mayar dasu a lokacin baki a laikum basan yadda akayi ta dawo ba yanz. Baffa Abdullahi ya gyara zama yana fadin af tunda tasan gida me zai hana ta dawowa kuwa a yanzu ni a ganina tunda sune ai sai a nemesu kawai yanzu zaifi. No ku bari ku gama da jama, a zaifi sauki modibbo ya fada a kausashe ga iyayyen ido tar ba tsoron komai a lokacin mahaifin ya kura mai idanu . Ya mike yana fadin nasan ba zata sake dawowa ba ko wanan don Faiza da Amira da fatima tazo amma rayuwan ta yanzu ba a nan yake ba kuma. Yai masu saida safe ya fita don shima hankalin shi a tashe yake lokacin da abinda ke shirin faruwa a ahalin su don yasan mutum dadaya ne kawai rigiman bai shafa ba a yanzu. Ni kaina nasan na kashe kudi ba kadan ba don kudin dana taba din ina kokarin muna tanadine a lokacin amma ciki nayi karfin halin tabawa na labta wanan uban sayayya da nayi din na bukin. Bin tarin kayan falon na sake yi da kallo ina fadin ba zanje wurin yinin bukin nan ba umma amma da dare zamu halarci dinner da za ayi don lokacin ne nasan yan family din maza da mata suna zaune wurin . Ki dai bi a hankali don kowa ya rigaka kwana yana rigaka tashi sun fiki sanin ta kan duniya zasu iya yin abinda zai shafi lafiyan ki ko mutuncin ki kin sani. Ban fito ba umma saida na nemi sa,ata a wurin Allah don haka Allah yana tare damu ko yaushe tunda bamu da hakkin su akan mu tace wanan haka yake Allah ya kara tsaya muna na amsa da amin. Nasan Faiza ta zuba ido kuma zata kira waya