← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 291 OF 337

Sashe 291

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

don Allah ku bar yarinyar nan da abinda ya isheta daddy ya fada rai bace. Kafin ya juya wurin dan nasa yana fadin kai meya hadaka da dan uwanka har yakai ga batanci ga iyayyen ku ? Shiru modibbo din ya danyi kafin yace wai fa daddy samuna yayi har gidana dacin mutunci aai akan zancen aure sahiba nine duk na kullashi. Nan dai ya kwashe yadda sukayi tiryan tiryan ya labarta masu saiga gwaggo hari tayi shiru kafin tace shi boy din ya fada ma hakan ? Gqaggo zan maku karyane naci riban me a hakan idan na fadi ba daidai ba daddy ya kalleta yace kinji ke ku dinga bincike kafin ku auwatar da abu don Allah. Yanzu waya fara zagi a nan daga zancen baki kawai kuma ya koma ya fada maki kekin hau haka ni ai na dauka duk daya suke a wajen ki ashe ba haka zancen yake ba. Wallahi yaya rainane ya baci idona ya rufe wai ace modibbone ya fadi hakan garemu ashe shidin mara kunya ya fara fada bai nuna ba. Ba zai nuna ba yanzu dai kun girma kusan ya kamata ku kun fadi hakan kamar yara me wasu zasu fada kuji zafin sa ? Kai daya fadama meyasa ka biye masa kuka kai ga hakan wanan ai fada mata ko yarane su aka sansu dashi haka baku maza haka magidanta ba. Ayi hakkuri munyi kuskure gwaggo kuyi hakkuri don Allah ranmune ya baci har muka kai ga hakan ya fada yana dukar da kanshi kasa cikin ladabi. Toh yanzu dai in zaku daina ku daina don mu ba tabbata zamuyi tare daku ba a nan in kun rike zumuncin kun kyautawa diyan ku nan gaba idan kuma kunci gaba da hakan kundaiga yadda abubuwa suke a yanzu. Bayan fitan shi gwaggo hari ta shiga wurin mommy sun dan jima a tare suna tatauna wanan matsalan na diyan su kafin danta ya isheta da kira ta bar gidan. Kwana biyu cur bamu fita dan gara su sun dan fita zuwa wurin sayayya ni dai kan ko kofa ban leka ba ina dakin kwance sai faman tunane dake cin zuciyana. Ba komai bane ya tsaya min a raina lokacin sai yadda rayuwana a yanzu zai kasance min da kuma yadda zan barsu umma na tafi wani uwar duniya da sunan aure kai ina nace a raina. A daidai lokacin da akai nockig din kofan tare da turo kofan lokaci guda jin hakan baisa na dago don ganin mai nocking din kofan da zai shigo ba. Wani kamshin ne ya daki hancina lokaci guda wanda yasani dago kai ina kallon kofan shine a tsaye kaina ya zuba min idanu kamar ranan ya fara ganina na farko. Da sauri na lalubi hijabin da nayi sallah dake gefena na rufa a saman dan rigan dake jikina dogo ya matse min jiki har zaka iya ganin suran jikina a fili. Wani dan guntun murmushi ya sake wanda har ina iya jiyoshi a lokacin Sahiba meke damun ki haka kinbi kin sukurkuce kamar ba Sahiban mommy ba dana sani mai kwazo. Ko duk a kan cikan alkawarin ubangiji akan mu yasa kike kokarin nuna butunlcewan ki a hakan ? Wani kallo na jefamai mekama da tsana do your wish kayi amfani da daman da kake zaton kana dashi a yanzu a kaina. Kada kayi tsamanin a yanzu kayi nasara ke nan ko ka dauka wanan damane da zakayi amfani dashi a kan mu kan wani manufa naka don ka cin ma nasaran abinda kake nufi. Hannaye ya ware kafin yace Allah ne kadai shedana banda wani manufa ko daya akan family din mutumin da yayi silan zamana wani abu rayuwa na. Bani da komai a kanku sai alheri fatana mu rayuwa tare mu kara kafa kan mu a karkashin innuwa daya daku haka kawai zan maku nasan na taimakawa kaina daku farin ciki yakai ga mahaifin ku. Stop dat jork kana tsamanin ban san abinda kake kokarin yi bane a kan mu din sai yayi murmushi yana gyara tsayin shi yace idan ma har kin yaudari kanki a hankan zato zunubine . Allah yaga manufata a kan ku yanzu kuma kada zuciyarki ya yaudari wani ko zato akan shi Allah ya gani ban nuna kudi ko karfin iko akan kowa ba naki illa zallah gaskiya danazo masu dashi kuma suka gamsu da hakan gareni. Don haka ina rokon ki da ki cire komai a zuciyar ki yanzu ki natsu ki fahinci waye mukhatar a wajen ki da mahaifin ki . Ranan da naga natsuwa zan sanar dake koni waye nan gaba na barki lafiya dama nazo naga fuskan kyakkyawan amaryatane nakuma yi maki sannu da jiki duk da nasan ba abinda ke damun ki sai fargaban gamayya dani a yanzu. Karkiji komai ni nidin mutum ne mai saukin kai da sanin ya kamata ga duk wanda ke karkashin innuwa na a zaune har sai idan maishi ya fito da nasa manufan a kaina muke raba hanya dashi . Saidai ki sani ni da sahiba auren mu na mutu ka rabane insha Allahu da sannu zaki fahinci koni waye nan gaba. Ki kula da kanki don Allah kada wani abu yazo nan gaba yafaru dake please take care yaran ki sunce a gaida ke idan na ganki. Yara na dago kai ina sake kallon shi da mamaki yaranshi fa ke nan yana da mata kila ma mata don hausawa irin wanan a yanzu ba zancen mata guda a gareshi sai mata dai da yara kan. Ohni sahiba naga ta kaina a duniyan nan ni yaya zanyi da rayuwana ke nan da wanan kaddaran dayazo min a hakan ?
Chapter 291 · 0% Book details