← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 205 OF 337

Sashe 205

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan mun firfito daga motan na tsaya nayi masu godiya sosai tare da basu abin rabo ba tare da sun san abinda ke faru ba don Abdul ya fake ga fadin ba,a son asan inda nake zaune yasa zamu nuna hakan a wurin. Kowa ya nufi bangaren shi kafin na juya muka shiga ciki nida Amar muka rufo gida su umma suna falo yaran duk sunyi barci saman jikin ta muka samu wuri muka zauna har lokacin sai sannu da zuwa take muna. Ammar ne ya fara bata labari yana tambayan ta da umman mu duk taron nan ana nufin su din yan uwan mune wai ? Haba dai na fada daga inda nake zaune ina cire sarkan wuyana don na riga na cire dan kunne ko alokacin . Nace duk wanda kaga na gayar sune yan uwan mu na jini saura kuma abokan arzikine da suka zo tayasu murna kafin na juyo ina fadin amma umma nayi mamaki da daddy ya aura wa karamar yarinya kamar baby wanan mashayin haka ? Jam ta fada mashayi kuma nace kwarai umma don har ta hudashi ma zaki gane hakan a jikin shi kinsan ni bana shiri da maishan wanan abin sam don haka naganeshi da sauri. Allah ya kyauta ta fada a karshe muka amsa da amin sai tace yanzu dai saura mu saurari abinda zai biyo baya ke nan don nasan dole su nememu yanzu kan ruwa a jallo. Zasu nema sosai ma amma ba yanzun ba sai an daura aure gobe wanan zance zaiyi boosting ga kowa don zasu hadu a wurin ne za a fara wanan maganan daya shafemu din don kowa yanzu haka yana cikin wasiwasin ne a zuciyar shi kan mu. Waya ta na mika hannu na dauko daga cikin jakata na kunna sako suka fara shigo min da sauri na dauko na duba ina karanta sakon da nagani daga oga sha,aban ce yasa na bude sakon da sauri ina karantawa. Katin gaiyatane na bukin kammala karatun kanwarshi tilo daya da yake da ita wand za ayi a Oxford. Wanan kan ai sai manya zuwan shi na fada a fili meke nan fa umma ta tambayeni tana kallona jin abinda nake fadi a loka nan nake fada mata abinda sakon ya kumsa. Shiru tayi kafin tace dani au a can ke nan zasuyi taron nayi mata bayani dalla dalla yadda zata fahinta a daidai lokacin ne kuma wayana ya dauki kara lokaci guda. Na duba ya Abubakar ne a layin yana gab da katsewa nadaga da sallama ya amsa yana jefo min tambaya kuna inane nace gida sai naji ya sake wani nauyayyan ajiyan zuciya. Kafin yace OKey kawai ya amsa dashi yayi shiru sai kuma naji yace ki kula don kin tayar da hankalin manya sosai a wurin nan yanzu haka nemaku suke ruwa a jallo. Karo na farko da zaice yaji farin cikina har nayi dariya a fili haka yadda yaji a lokacin tun bayan dawowan shi garemu kafin nace sai su matsa idan suna son ganoni a yanzu ai da safe zan shigo gidan ki gaida umma. Don sam baiyi zancen yaran shi koda yake yadda yake magana yanayin ya nuna cewa shima dai hankalin shi a tashe yake a lokacin. Daddy tun safe ya fita daga gidan gidan amin sa ya nufa kai tsaye wanan fitan shine sauki a gare shi ranan don bai dawo ba sai gab da daurin aure Abubakar da suke waya dashine ya gudanar da komai har aka gama tsara komai yadda suke so. Hankali kan ba a kwance ba don duk taron yan uwa da zaka gani a gidan bukin suyi gungu gungu kowa da abinda yake fada inda a nan hjy karima take tsuntar wani zance ga jama, a. Hakan sai ya lankwasar da ita ga gagarumin shirin da tayi don taba mommy da diyan ta takaici a ranan don itama hankalinta bai kwanta ba ai a wurin. Saidai duk da hakan yan uwa da abokanta sunyi dan kide kide da raye raye wanda sukasa niyar yi don turawa mommy haushi da yayan ta. An daura aure an tashi lafiya baki suna watsewa ne baffan su nan biyu suka kira taron gagawa a tsakanin su yan family din. Bayan kusan duk wanda aka gaiyata sun isone sai yan kalilan ne basu wurin aka fara da addua kafin ya fara magana da fadin. Tau sallamu Alaikum jama, a duk da nasan wasun ku da dama nan sun san makasudin wanan kira na gagawa da ya hadamu nan wasu kuma basu sani ba dai. Kamar kullun kusan sai wani abu na muhinmin ya farune na musanman muke wanan haduwan irin haka a nan . Daidai lokacin Alh Nuhu ya tura hannu a cikin Aljihun shi na riga ya ciro kwankwan shaken shi ya balle ya diba ya tura a duka hancin shi biyu yana turmuzawa da kyau don ya dauki caji. Jiya zance ko shekaran jiya baiyanan wata yarinya da wasu a nan cikin ku suka kawo muna labari tazo da barazana a gare mu cewa ita din da kanin ta yaya ne ga dan mu kuma dan uwanku marigayi sambo daya rasu a shekarun baya daya shude. Nan aka fara dan hayani a falon tsohon lokaci guda kowa da abinda yake fadi a lokacin don wanan bakon lamarin da akazo dashi din. Ko tana da hujjan fadan hakan ko baiyanar da kanta da take kokarin yi yanzu a gaban mu idan tana da hujjan hakan sai tazo muna dashi don mu gamsu da bayanin ta Alh Nuhu ya fada a kausashe. Yana bin kowa dake falon da kallo idanun sa sun kada sunyi ja sosai a lokacin kowa yai shiru a falon yana sauraren shi don bai magana wani nayi ko don dole a kyaleshi ya gama. Yaci gaba da fadin wanan zancen banza da wofine ai ta bijiro muna yanzu wai ita din yace ga dan uwan mu a sanin nan kowa yasan Sambo ai ya dayace gareshi sai matar daya bari daya. Ita kuma akarshe tabi dare ta gudu a ranan da abin ya faru yasa muka fara zargin ko itace ta kashe shima ta gudu kuma. A iya bincke mu gano inda take har malamai bakwai mun gani kan hakan wurare daban daban suna sheda muna duhu suke gani ma,ana dai bata duniyan nan daga ita har yarta kuwa. Don me yanzu wata yarinyar banza can yar duniya ga yadda akace ai wanan din kamar kabilace ma ita to a waje ya haife ta ko me bamu sani ba ? Wanan kuma ka fadi ba daidai ba yaya don ba zamuyi saurin sheganta yar nan a yanzu sai idan mun tabbatar da hakan baffa Hamza ya fada wani mai ra,ayin rikau ne shi ba ruwan shi da kowa a cikin su. Wani kallon shi Alh Nuhun yayi kafin yace duba Hamza kada kayi kokarin kawo muna zancen da baida hujja a nan ko kadan abinda muka sani shine Sambo dai ya rasu haka kuma iyalin shi duk munsan basu raye a yanzu. Wanan ba gaskiya bane kan don har in kana tunanen hakan ka daina komai mai iya yuyuwane a yanzu idan yarinyar nan tazo da hujja mai karfi ya tabbata ita din da kanin ta din yayan marigayi din ne ke nan. Ta kawo hujjan mana ko ta baiyana nan agaban mu idan ta isa ita din tsagerace muna sauraron ta ya sake fada rai bace kowa dai nan yasan mairoce matar sambo yau ina mairo din take. Zata ko zo har mairo din baffa Abdullahi da tun dazun yake son yin magana yana shakkan abinda zai fada din a wurin sai yanzu Allah ya bashi ikon fadin hakan kowa ya kallo shi. Kwarai zata zo har mairo din da kuke fadi a yanzu mairo bata mutu ba tana raye don ance kwanakin baya suna cikin harin nan ita da yaran kusan shekaran biyu a nan kaduna gidan dcp zaune. Meka fada yace kwarai yau da safen nan Addah ke fada min komai don tayi shirune da bakinta bisa bin umurnin shirin mijinta da yace kada ta nuna kosu din waye a gare su taja bakin ta tayi shiru bata fada ba. Ta fada muna duk yadda a yanzu kuke tsamanin wasan ya wuce nan sin ashe mairo ta tafi da ciki a jikin ta wanan cikin shine wanan yaron da kuke tantama akan shi. Ita Addah ta fada maka hakan yace kwarai da gaske kuwa bani kadai ba dani da Hamza da sani da Hari da Asiya yau da safen nan a falon ta. Lalai kuwa zamu zauna da Addah kai zancen nan fa yafi shafuwan mu a nan nake gani baku kadai ne zaku nuna damuwan ku a kai ba kawai. Amma dai muna da hakkin cikin wanan zancen kuma kamar yadda kowan mu nan idan ya mutu ya bar baya kowa zaiyi hakki a kai don kula da abinda dan uwa ya bari hamza din da yake karami cikin su ya fada. Kwarai kuwa baffa Buhari ya fada wanan maganan haka shike hamza don haka yanzu ya kamata ace mun samo ita mairo da yaran nata don samun gamsashen sheda a wurin ita mairon. Abinda nagani ke nan baffa Abdullahi ya fada don zancen manya sunyi shiru sun bar matasan kannen su suna magana a lokacin. Samun su yanzu shine shawara na gaba baffa hamza ya fada sai Abdullahi yace baida wani wahala don wanan yaron moddibo da dan wajen hari sun san da ida suke zaune a can ikko. Ikko fa Alh Nuhu ya fada a cikin mamaki yace kwarai a ikko suke zaune ashe duk wanan dadewan haka tana ikko zaune ashe. Amma indai hakane Ali dcp ya munafunce mu ai ba haka mukayi dashi ba ya fada a cikin subutan baki baffa hamza ne ya dawo mai da tunanen shi yace yaya kukayi dashi muji ? Wani banzan kallo ya jefawa kanin nasa yace baka isa ba kuma in fada maka don kai hamza da nake gani nake hango zallan bakin ciki a idon ka baka isa ka titsiyene nan in fada maka ba yanzu. Dan dariya hamza din da suke daki daya da hjy Addah ya kwashe dashi don shi lectura ne a A b u
Chapter 205 · 0% Book details