Sashe 69
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ba zan taba barin ta a rayeba cikin duniyan nan har shegiyar yar da suka fara haifa din nan kuwa ku dauke shi mu tafi don tsayuwan mu a nan zai iya kawo muna matsala idan mutane suka fara fitowa sallah yanzu. Naji wani mai sanyin murya a cikin su yana fadin indan mun tafi dashi ina zamu kaishi yanzu a hakan ya Nuhu yace a hanzari rafi zamu jefa dan banza yaya Nuhu ya fada. Rafi hjy Addah ta fada cikin sautin kuka tare da fadin ashe shiyasa aka kasa gane gawan shi ruwa suka jefa shi ke nan. Sautin karan tashin motocin su na fara ji kafin can na fara jin muryoyin makwata mu da wasu mutane suna fadin sun tafi ai ga gawan maigadin sai alokacin na fito. Daga inda nake boye da yata a bayana mutane suna ganina sukayo kaina da tambayan meke faruwa a cikin zaucewa da rudani nake fadin shike nan sun kashe shi. Yan uwan shi sun kashe shi sun halaka min shi rayuwata ta mutu ke nan bani da sauran amfani a yanzu kuma . Haka nayi ta maimaitawa har yan sanda suka iso wurin suna bincike akan abinda ya faru a gidan ba bakin da zan basu amsa a lokacin. Wai kuma saiga yaya Nuhu na gani shine a gaba wurin bawa yan sanda labari saidai muna hada ido zai watsa min wani harara a fakaice wanda ni kadai nasan da yana min wanan kallon . Gaba daya naji ban son ganin kowa nasa har ku din nan don har lokacin da ka iso yaya ban fadi komai ba ga kowa don na koma kamar kurma mai tabin hankali a lokacin. Shine ana sallah magariba na sullace jiki na bar gidan da ba wanda ya ganni daga ni har yar tawa muka bar garin nan ke nan. Sai umma din ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya da sauri yaya Abubakar yace amma wanan mutumin anyi mara imani a duniya shine ya kakace komai da suka bari ayanzu. Daddy lalai ya zama dole a tuhume shi kan wanan zancen zan tafi inyi aresting nasa kan tuhuman shi da kashe dan uwan shi tare da batar da gawan shi tunda ga shedu mun samu a yanzu. Dakatar da Abubakar din mahaifiyar shi tayi tana fadin na fada maka ka fitar da bakin ka a cikin zancen nan don wanan zancen iyayyen ku ne ba naka ba. Daddy ya katse ta da fadin Addah ba zaki godewa yaron nan ba bisa ga namijin kokari da yayi na dawo muna dasu gida yanzu ? Ya dago kai yana kallon ta a cikin mamaki ta dukar da kai kasa tana fadin ba hakana bane yaya kasan fa halin wa yan nan mutane da sheri kai kanka kasan komai. Idan na sani shine me yara sun dawo yanzu sai su basu hakkin mahaifin su da suka taushe ba shike nan ba kowa ya kama gaban shi. Yara dai har uwar na fada maku a gidan nan zasu zauna don haka ko bayan raina ban yarda a kaisu wani gidan ba su zauna duk da nasan yin hakan zai kawo matsala a wurin, , , , , Dama ai tun jiya ina zargin hakan nasan yaran nan yayan kane da wanan matar da nake gani mahaifiyar yaran hjy karima ta fada daga kofa tana shigowa falon ranta a bace hankali a tashe. Amma wallahi anji kunya girma kuma ya baci ka haifa a bariki an biyo ka dasu nan yanzu don ga asiri ya tono a yanzu. Shine akazo nan a kulla yadda za ayi dasu ba tare da kowa ya sani ba to Allah yafi ku don naji komai a yajzu. Har kana fadin wai a gidan nan zasu zauna don diyan kane su halal malal ba wanda ya isa ya hanasu zama a gidan nan kuma ko bayan ranka watau shi ya rike makasu amana ke nan ko. To ai dadin abin basu dai da gadin ka tunda duniya basu sheda daurin auren ka da uwarsu ba ai kowa kuma a cikin dangi bai san dasu ba dama. Murmushin manya daddy din yayi ya kalleta yana murmusawa yace kwarai kuwa yara yayana ne uwar kuma kanwata ce ita sai me kuma ? Zaka dai fada tace tana huci tana kari don ranta ya ga ma baci da abinda zuciyar ta ya raya mata a lokacin game damu din. Haba hjy karima ina kuma wanan zancen ya fito haka a bakin ki hjy Addah ta fada a cikin mamaki sai hjy kariman ta juyo a hasale tana fadin kaji munafukar mace a nan. Idan ba yayan sa bane na waye har yake fadi yanzu a rika mashi su a cikin amana koda bayan ransa ne ? Don kin mayar da kanki wata bagidajiya can har zaki yarda a yi wanan aika aukan dake ke gaki mai son miji kina son a kiraki da salihan mace ko mai rufawa miji asiri saboda son yabo da kikeyi a wurin shi. Kaiya boyar Allah wanan mumunan zancen bai kamata kiyiwa bawan Allah nan shi ba don shi din yayanane na jini kamar yadda hjy take yar uwa a gareni itama. Yaya kuma su ba shegu bane diyan dan uwansu ne da baya raye a yanzu don Allah ki fahinci abin da idon basira kafin ki furta kalamanki. Abubakar daya gama cika a wurin ya mike yana fadin daddy sai kafito ni zan dan fita anjima zan dawo mu karasa zancen. Daga haka yasa kai ya fice a dakin cikin takaici wai a gaban shi yau hjy karima ke dakawa uwarshi tsawa haka don rainin wayau. Dama ba yau ba ya gama fahintar halinta matar yar bala,in rainin wayau ne sosai idan ta samu wuri haka kuma yaga karfin halin daddy da har tayi mai wanan mumunan shedan a yanzu bai dauki wani mataki a gareta ba. Yau dashine gobe ba zata kara gigin raina mai wayau haka ba a gaban mutane ya kara jan tsuki yabawa motan shi wuta ya tafi. Daga inda nake tsaye bayan labule na sulale a kasa ina hawaye tare da kare bakina da hannu kada suji sautin muryana a lokacin. Can naji muryan daddy yana fadin modibbo kada kace zakayi wani yunkuri a yanzu kan wanan zancen ka bari sai mun zauna mun gama tataunawa sai mu san inda zamu bullo masu ga zancen. Yace naji daddy ya figi mota zuwa gidan shi kai tsaye a falo ya kicibis dasu Nazifa a zaune da yan uwanta suna gaidashi da dawowa yayi kamar bai jisu ba ya shige dakin abinshi ya kyalesu yana maijin haushin mahaifin su duk ya shafesu a lokacin. Sintiri ya fara yi a cikin dakin yana nazarin labarin da umma tabasu a yanzu a kan mu yaje ya dawo ya kasa zama a dakin karshe ya nisa yana fadin. Wai imagin ace dan uwan haihuwan kane yai maka haka inaga wani sabba can bare na waje aida zai aikata wanda yafi haka ke nan gareshi duk saboda abin duniya sukaiwa dan uwan su haka. Shine mommy ta san da hakan har ta yarda ta aura mashi jinin wanan mutum da yayan da zata haifa dashi suna iya kasheshi ke nan ashe ? Hannun shi ya dunkule a wuri daya yana naushi kafin yace a fili na tsani wa yan nan mutane har cikin raina ga baki daya. Wait yace da sauri ya daga kanshi yana fadin what harda su kawu iliya ke nan duk wanan arzikin dama ba nasu bane suke ci ke nan ashe hakkin wasune suka gina kansu dashi ashe. To waye mai sanyi muryan data fada ya danyi nazari can ya girgiza kai yana fadin haka ba zai yuyu ba ace wai harda baffa Audu cikin case din nan. Ya fara girgiza kai yana fadin No No no no dukan su ke nan sun hudun duk baffanin mune sukai wanan aika aikan ko me Allah dai yasa bada daddy a cikin su ba ya fada da karfi gaban shi nata faduwa don yasan kusan kansu dayane ga komai da sukeyi Fadawa yayi saman gadon ya dafe goshin shi da hannun shi daya yana fadin daddy ya damu da zancen yaran nan sosai me hakan ke nufi ke nan a yanzu.