Sashe 37
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mun isa gida hankalin umma a tashe ranan don na gane hakan ne ta yadda take amsawa mutanen dake cewa damu u are wellcome, ko u na don comeback ? Mun shiga gidan dayake muna farkon a gidan sauran na daga ciki don ni sau daya na taba shiga cikin gidan naga ashe gidane babba dake dauke da mutane kala kala kuma wai duk irin ginan bamboo tree daine ko a cikin gidan. Wasu zakaga nasu har AC akwai a ciki wasu ginan kuma katako da katako aka hada aka mayar dashi daki mai kyau a ciki. A haka muke zaune cikin sa saidai mu namu ya nuna tsohon yine don ya dade ya soma dan fadawa amma bai lalace ba. Nikan muna shiga wuri na samu na kwanta don wani iri nake jin jikina ba karfi yayin da umma tana aje gyalen ta ta dauki buta ta nufi ban daki a lokacin. Har ta idar da sallah ban ko iya motsawa ba a lokacin ina kwance inda nake kuma ba barci nake yi ba sai can na iya mikewa naje nayi alwala na dawo. Ina sallah Ladi ta shigo tana muna sannu da zuwa da alama daga unguwa take a lokacin don shigan danaga tayi ya nuna hakan. Bayan sun gaisa tayi min ya jikin an samu ganin likitan tace mun ganshi yace makariya ne ke damun ta ya bata magani har ni ya duba yace mu koma karshen wata dai akan nawa jikin a kara awo. To Allah ya sauwaka ladi ta fada har ta juya take fadin wai gajiyane hakan yasaki laushi naga yanayin ki ya dan canza kuma ? Ke dai uwar dakina bari kawai abine da daure kai wallahi wai neman mu akazo yi a wanan can gidan da muka taso. Ke ki bari don Allah Ladi ta fada tana dawowa cikin dakin namu umma tace bari ke dai yadda jaga iya Bisi na rawan jiki da ganin nasan akwai wata a kasa. Don har cewa tayi wai meshi babban mutum ne yace kuma shine mahaifin yaran nan shiyasa data tambayeni inda muke Allah ya rufa min asiri ban fada mata gaskiyan inda muke yanzu ba da zama. Na dago daga inda nake kwance dunkule tun bayan idar da sallah na na dan kalli umma din don jin abinda ta fada. Ladi tace anya ba wani ne ke bibiyan rayuwan ku ba dama, umma tace nima abinda ya daure min kai ke nan yanzu. In har hakane kuwa ya zama dole un bar kasan nan mu kara gaba wajajen shagamu ko zuwa kamaro ko ghana mu samu wuri a can mu zauna. Umma na fada cikin mamaki don ban san lokacin dana saka baki a zancen su ba akan mahaifin mu yazo neman mu zamu kara gaba ko me ? Ni gaskiya na gaji hakana umma na gaji inma kashe mu zaiyi ya kashe mu matukar dai zanga mahaifina a duniyan nan. Ke ar ke me kika sani Ladi ta fada a hasale an fada maki neman arziki suke maku a yanzu dole neman rayuwan ku suke maku su halaka ku ai. Halakawa kuma da mukai masi me zasu halaka mu kuma ni dai koma meye su halaka mu din ma mu huta zaifi. Duka umma tayi niyar kaimun daga inda nake kwance Ladi ta tare tana fadin kada kiga laifinta yarinyace ita bata san komai ba don haka kyale ta ai jiki magayi. Har suka karaci fadan su suka kare ladi tabar dakin ban kara dago kaina na kalli inda suke ba nan ta bar umma da tunanen a zuciyar ta nawaye mai neman ta kuma ita da diyan ta. Shin wa yanda ta bari arewa ne suka biyo ta ko kuma nan ne kuma ta samu wasu masu bibiyan lamarin su kuma ? Ya isa kaduna a cikin tashin hankali misalin magariba don haka kai tsaye dakin shi ya nufa ya bude ya shiga. Wanka yayi ya dauro alwala ya fito zuwa masalaci a nan ya hadu da mahaifin shi suka gaisa yasan yazo garin suka shiga sallah a tare. Sai bayan isha,i suka shigo gidan tare lokacin ne kuma kowa yasan da zuwan shi garin ranan suka shiga taron shi a cikin murna banda hjy karima da gaisuwan kazo lafiya kawai ya hadasu ta wuce. Abinci aka gabatar masu ya dace da hjy mahaifiyar sune da girki tayi masa irin abuncin da yake so tuwon alkama da miyan danyan kubewa da kassan rago yaji daddawa da kayan yaji ya sake don anaci a cikin taro yaci sosai. Hjy Addah kallo daya tayi wa dan nata tausayin shi ya sauka mata sosai a cikin zuciya don yanayin sa kawai da ta kalla tasan yana cikin damuwa. Har suka bar wurin tana satan kallon yadda dan nata ke ciki hakan sai ya saukar mata da damu kan abinda ke damun shi din balle zuwan da sadiqa tayi gidan da sunan wai tazo ta gaidasu kuma su santa a gidan ya kara saka hankalin hjy tashi. Iyayyen su na barin wurin Nabila da gulma yace ta matso kusa da yayan nata tana fadin ai yaya baka zo tun jiya bane da yau kasha kallon mamaki a gidan nan sosai. Dame ya faru ya tambaya cikin son ya san ko meye saidai har lokacin idon shi na awayan shi yana karanta sakon da aka turo mai wanda ya dauke mashi hankali. Wai ashe wanan Samiran zaka aura yar gidan kawu Nuhu din nan yau ai tazo gidan nan gaida su daddy, wai amma dai tasha mai gaskiya a jikin ta kamar a gidan su aka bude kamfanin bleching fa. Au baki sani ba a gidan nasu kamfanin yake ko bata kawo maki tsaraban irin sa bane da tazo ? Ta saki yar dariya tana fadin kai yaya bafa kushe mata nake yi a hakan ba daga fadin gaskiya naga ka hasala dani mana yanzu ? Daga fadin gaskiya Allah bana son na ana shafa wanan mai din ne yace ai amsa na baki zaki tambayeni nasan ko wacece kike zance akanta asalima yanzu naji zancen a bakin ki ai. Tana dariya ta sake fadin kai kaji yaya abin ya koma yar boyone yanzu kuma ai zamu ganta har mu gaji sai dai gaskiya akwai aiki kan gare ta yadda nasan halinka da tsanani din nan. Dama ai nasani mai shegen zuban nan sai ta tare ka da zancen nan tunjiya take mita a kai hjy ta fada daga bayan su tana karasowa a inda suka barsu zaune har lokacin. Kai ya dago a lokacin yana duban hjy din har ta karaso inda suke zaune ta zauna Nabila tace Allah mommy abin ne ya ban mamaki sosai yadda tazo muna da fitsara a gida bako kunya wai ita tazo nuna kanta gareku. Sai akace kuma ki fada mai hakan ko don shegen surutu irin naki hjy ta fada tana hararan yar nata tayi dariya tana mikewa tare sa fadin mommy abinda nagani fa na fada . Kallo Abubakar hjy tayi tana fadin malam ka koshine ko s zubama ferfesu ka kara dashi dan murmushi ya kakaro a fuskan shi tare da fadin . Mommy ins zankai abincin nan danaci yanzu haka ma yana damuna don shine yasa na kasa tashi a nan tun dazun. Wani abinci kaci bayan wanan dan cakulan da kukayi daga kai har Alh bakuci komai ba ta fada tana kallon shi dole in dan zauna ya fada min kafin naje na kwanta ai . Sai da safe mayi zancen da wanan fadi ba a tambayeka din data fara ma don yarinyar dazun an turo ta gidan nan da safe ta gaiyar damu. Suhaila tace mommy ki bar cewa ta gaida ku tazo dai tayi maku fitsara a gidan nan dai ita da yan uwanta. Kai kukan yaran nan akwai iya sa ido da shishigi da gulman tsiya ina ga sai dai na maku tsiya akan zancen nan. Mommy ai abinda suka ganine suka fada da bata zo tayi ba ai hakan ba zai damesu ba son basu saba ganin irin fitsaran su ba a gaban manya. Wallahi yaya zama fa tayi sosai suna hira da daddy da mommy a falon nan har tana tambaya wai yaushe zaka zo . Murmushi yayi na mugunta tare da fadin oh ni take son gani ma ke nan ya fada yana girgiza kai da sauri hjy tace kaga kada ka biyewa yaran nan kaje ka aikata abinda bashi. Mu zumunci muke son gyara mu hada a tsakanin don zumunta yayi karfi ba abinda zai sake wargaza kanun ba a hakan ta fada cikin dan bacin rai. Mikewa yayi yana dan buga cikin shi alaman ya koshi da yawa don ya kawar da zancen don ganin ran mahaifiyar nasu ya fara baci da zancen. Har ya shiga dakin sai mamaki da al,ajabin abinda sisters din shi ke fada mai yakeyi saidai abinda ya kula hjy tana son zancen ko don abinda ta fada a gaban shi yanzu a falonsu. Da wanan tunanen barci ya dauke shi sai washe garine days zo gaida daddy ya fito mashi da zancen dif ya dauke kamar ruwa yaci shi a lokacin. Don irin albarkan da daddy din ya dinga saka mai kan amincewa da zabin da mahaifiyar shi tayi mai kuma yabi irin al,adansu na iyayye da kakani da aka shimfidasu akanshi duk zurian su kuma suke bin hakan har yanzu . Saidai duk bayanin da mahaufin ke masa hankalin shi baya jikin sai lokavin da daddy ke fasin mun yanke shawara karshen wanan watan da zamu shiga za,ai komai har daura aure tunda duka bangarorin bamu da wani shirin daya saura akan hakan matace kawai dama kake jira ka tare a gidan ka ita kuma iyayyen sunce a shirye suke ko wani lokaci dama. Kaga shike ka zama cikakken mutum a yanzu don duk wanda yakai ga aje iyali girma ya haushi ke nan a rayuwa zakaga ko mutane suna mutuntaka fiye da lokacin da baka da aure. Don haka kafin ka koma inda ka fito sai kaje kaga yarinyar da idon kaga irin zaben da mahaifiyar ka tayi ma don suma suna son gani jiya har nan gidan take tazo gaida mu ita yarinyar da yan uwanta nima kuma bazan