← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 224 OF 337

Sashe 224

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

tabbatar da ba zata taba shiga lagos a cikin wanan shigan ba ko dan yayanta ya tafine baya kusa dasu. Saidai kuma naga ita ko ta damu da haka duk da kallon da yawan mutane suke mata a wurin baisa ta ji wani darr ba a lokacin muka hade ta dan rugumoni tana fadin a, a Sahiba ashe kina nan baku tafi tare da brother dina ba na dauka tare zakuyi tafiyan dashi ai. No team din mu suna nan ba tare damu ya tafi ba sai naga tayi murmushi kafin ta kalloni da kyau tana fadin aiba dole saida team zaki tafi ba don ke yanzu ogan su ce. Don me ba zakibi shi ba wai, ina cutship kukeyi a yanzu ke dashi kuna son ku fahinci juna a tsakanin kafin auren ku dashi don haka ba wani abu bane idan ya wuce dake ai a yau din don kowa yasan soyayya kukeyi a tsakanin ke dashi yanzu. Jin kalamin ta yasa na dago da sauri na dan mata kallon mamaki ta gyada min kai alaman eh tare da fadin kada kibi zancen Alaja ko wasu can masu gulma. Duk da nasan mommy mu bata son alakan ku kedashi tace ke din baki dace da brother ba sam, saidai ni banga rashin dacewan da mommy ke fadi ba a kanku nan. Don gaskiya brother na ya iya zabe sosai wallahi saidai kawai abinda mommy din take fadin a kanki shine kawai yanzu matsala a wurin ku. Kina da kyauki da kyau diri da tsari duk da ake nema a jikin mace, ta nunani da hannu tace komai naki alhamdullahi gaki da ilimin ki sosai don naji yayana na fadin kina da ilimi sosai a both side a kanki. So ni banga laifin a nan ba dan ya zabeki a matsayin pience din shi da har zaisa ita Alaja tace wai bata yarda ya gabatar dake a matsayin wace zai aura ba a yanzu. Tunda harke yake son ya aura don kina bashi tausayi da kuma kaunan ki da yakeyi right ta dan daga gira tare da kara kura min idon ta sai kuma ta nisa tana fadin. At this age da kike ya kamata ki huta hakana sahiba, ke din baki cancanci wanan rayuwan wahalan ba kamar wani namiji ko yaushe kina kan aiki nasan abinda yayana ke kallo a gareki ke nan yanzu don nasan halin shi. Amma mommy bata gane me yake nufi ba har tana fadin bata yarda ya kawo mata ke a matsayin sarakuwa ba ke mai juju ce a kanki. So ni ban damu da duk abinda kike dashi ba a kai tunda yayana yana son ki a hakan da kike, meye matsalanta tunda bada ita zaki zauna ba. Don nasan yayana nasan halin shi yana da ilimi da hankali da hangen nesa gashi da tausayin na kasa dashi duk da mahaifiyar mu bata son hakan tace halin daddy din mu da haka akai poisining din shi da goro a kauyen su. Ni nasan idan ba yaga dacewan ki dashi ba daba zai taba yarda ya nuna mata haka ba don ita wanan dai yar yuhanus taso ya aura a yanzu amma ni sam batai min ba. Shi kuma ya nuna mata kece ya yanke zai aura don haka yana da right da zai zabowa kanshi abinda zuciyar shi ke so a yanzu. Amma taki ta gane hakan ita duk da shita samu da nice nan kingan ni da kawai zan fitar zancen tane in yi abinda nake so a rayuwana tunda ita tayi nata zamanin. Na kallo ta cikin mamaki don na sandare a lokacin ina jin abinda ban taba zaton jin shi ba daga bakin ta itako ta dauka zancen nata yai min dadin saurarene a lokacin. Taci gaba da fadin wai kin san me yasa mommy keson ko yaushe ta dinga zabawa brotherna mata ya aura ? Kai na girgiza mata kamar zombi tace ba komai bane fa don ta dinga juya matar yadda take sone kawai ne daga ita har brother dina. Kin san Mum nada wani hali da baida kyau ita burin ta a ko ita taga ta mallaki kowa da komai yadda takeso shine kawai dalilin ta nayi mai zaben matar da zai aura ko yaushe kada ta auro mai wace zatafi karfin ta. Ke din nan tace akwai juju a kanki ba zata taba yarda yayana ya auri mace irin ki ba a cewanta don zaki dinga fada mai halin da kowa yake ciki da abinda zai faru ga rayuwan kowa don tun lokacin a lagos ta tsorace da lamarin ki. Nan kan dan munafukin murmushi na sake a fuskana tace ai kin san matar shi ta farko itace ta nema mashi ita yar abokin daddy muce ita. Haka ta dinga juya ta har mutuwar ta bata isa ta sake da mijin ta ba mommy bata bari sam yanzu ko da wuya ta kara samun irin ta kuma. Haka bayan mutuwanta ta aura mashi wata a America saidai ita kan wanan mommy bata san ta fita wayau ba sosai don haka auren bai kai ko ina ba suka rabu a cikin wata shidda dayin auren nasu. Don haka ba kowane yasan da zancen wanan auren nasa ba don ko Nigeria bamu tafi da ita an ganta ba don hakama wasu basu sanda auren ba . You know what ta tambaye na girgiza kai tace ke mai sa,ace gaskiya kinsan abinda yasa nace hakan na dan kalleta sai tayi murmushi. Tare da fadin idan na fada maki brother dina bai taba soyayya ba zaki yarda da hakan wallahi shiyasa nake son shi dake don abinda zuciyar shi ke sone ke. Murmushi na sake kafin nace nima ina son ki saidai ina son ki sani tsakanina da yayan ki babu wani soyayya ko wani zance makamancin hakan gaskiya. Aikine kawai ya hadamu tare bayan haka ba wanan abin da kile zato a tsakanin mu na zancem aure ko wani abu can. Idan Alaja taso ta kwantar da hankalin ta ni aikine ya hadani da danta ba wani zancen soyayya ba can kawai dai ni taimakon juna mukeyi dani dashi. Sai zancen juju da take fada saukin abin ba zuwa nayi na saya ba wanan kyautane daga Allah daya nufeni da hakan don haka ko ita bata wuce wanan matsalan ba a wurin Allah. No kada ki damu ko ki dauki hakan da zafi sonda nake makine yasa har na fada maki sirin mu gaskiya . Kada ki damu Ganiyat wanan ba wai na dauki abinda zafi bane kawai dai ina son Alaja ta gane cewa ni danta baya gabana don haka ta hada shi da d uk wace take so . Ina fadin hakan na juya zuwa dakin da aka saukemu a cikin sa da ace a Nigeria nake ko kusa da gida ranN babu abinda zai sa kara kwana .
Chapter 224 · 0% Book details