Sashe 40
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yar uwa ina bukatan adduan ku da bakunan ku masu albarka Allah ya yaye min duk abinda ke damuna dani daku duka baki dataya don Allah kice amin yar uwa Allah ya amsa muna tare dake. Ko kafin ya isa har anyu jere a sabin gida sa daya gina kuma daddy ya taimaka mai da wasu abubuwa. Wanda hakan ya kara jawo mai bakin jini a wurin hjy karima tun tana fadan hakan a lokacin a zuciyar ta dakuma aminta har dai yakai ta fito fili ta tukari Alh da zancen tana fadin moddibo fa bashi kadai bane akwai yan uwanshi suma suna da hakki a cikin dukiyan shi. Murmushi ya dan yi yana zaune kamar badashi take magana ba sai da yaji tayi shiru ya dago kai da hasals yana fadin kin gama abinda ya kawo ki ? Tace aini ba fada nazo yi ba gaskiya na fada don bashi kadai bane akwai wasu yace oh niki dabaran ke nan ke to ina wasu din suke ki nuna min su a yanzu ? Ta dago itama a cikin mamaki tana kallon shi don jin abinda ya fada yana huci yace nace ki fada min ina wasun suke a yanzu din don ni shina fara gani a yanzu. Itama a cikin fushi ta fara fadin wa yan nan matan daka raina don suma mutane ne ai kuma dasu nake alfahari. Amma kuma dake dasu dani gaba dayan ku kuke tunkaho a garin nan ko sai tayi shiru karima kina da matsala wallahi. Moddibo da kike gani wata rana ko ina raye ko ban raye shine gatan ku daga ke har diyan naki da a yanzu kikewa wanan fadan. Kuma kada ki manta ba rashi ko wani abu yasa nakewa yaron nan haka saudan shima yana da hakki hakan a kaina kamar yadda kikewa diyan ki fada a yanzu. Kin ban mamaki karima halaiyan ki na banza a yanzu suke kara fita fili ko can ace wani yana cin albarkancin wani da badon darajan mahaifin ki ba dana nuna maki ko wa nake nima kingani. Ai dama haka fadan gaskiya yake saukin abin dai yadda kowa ya iya shige da fice nima zan iya hakan ta juya ta fita tabar dakin cikin kunya ya bita da kallo. Zuciyan Alh kan cike yake da zafin wanan maganan da matar tasa ta sameshi dashi wai yana kashe zarahi akan mutum daya kamar shi kadai ya haifa. A karshe mikewa yayi yana kai kawo a dakin shi daya har hjy ta shigo ta sameshi hakan kallo tsoro tayi mai don ta fahinci akwai wani abu mai zafi dake damun mijin nata a lokacin. A haka hjy ta sameshi a dakin binshi ta fara yi da kallo don ta fanci akwai abinda ya faru da maigidan nasu na bacin rai a lokacin. Alh lafiya dai ta fada tana kallon inda mijin nata yake tsaye ya dan juyo ya kalleta tare da kawar da kai ba tare data iya furta komai a gareta ba. Ido ta kura mai na dan lokaci kafin ta nisa tana fadin Allah ya sauwa har lokacin bai iya bude bakin shi ya bata amsan abinda take so ba. Lokacin da hjy tashigo dakin shi bayan kwana biyu da hakan da turamen zani a hannun ta guda biyar tana fadin ga abin arziki Alh ta zube turamen a gaban shi saman table din dake gaban shi a falon shi din tace. Gashi hjy karima ta bada a zuba a cikin akwatin modibbo da za akai gobe Alh ya dago kai a hankali ya dan kalli hjy ya girgiza kai tare da bin kayan da kallo yace ita karima din tabada wa yan nan kayan ? Tace yanzu ina daki Ladi ta shigo min dasu sai kawai ya sake murmushi a fuskan shi yana girgiza kai yace angode ai. Tun wanan lokacin hjy Addah ta fahinci akwai wani abu daya faru mijin nasu yace hakan kan kayan don ta dauka hakan zaisa yai farinciki a fili. Sai taga sabanin hakan gareshi shiru hjy ta danyi na dan lokaci kafin ta mike tana daukan kayan data zube din a gaban shi. Haka ta fita gwiwa a sanyaye ta kasa furta komai saidai zuciyata yana cike tab da zargi kan haka. Bukin ya taso din hjy karima din ita ta jagoranci komai da akayi a ranan ta boye komai dake cikin zuciyan ta an tafi da ita a cikin sha,anin akan shawaran da kawayenta suka bata na ta daure a tafi hakanan da ita kada ta bari a gane akwai wani abu a kasan zuciyar ta. Ganin har za,a fara sha,anin buki Abubakar bai shigo ba baiyi waya da kowa ba kuma sai hankalin iyayyen shi ya tashi sosai. Daddy ya soma neman layin Abubakar din wayan ba ringing ba a daga va sai hakan ya kara tayar da hankalin daddy din sosai. Ya kara kira karo na biyu akaci sa,a ya dauka daman ya kewayane a lokacin. A cikin girmamawa ya fara gaida daddy din da daddy ina wuni, ya amsa da lafiya kalau shin ba zaka samu zuwa bane har za a fara buki. A dan maraice yadda yaji muryan daddy din a cikin fushi yace dashi aimun hakkuri daddy ina tafe akwai abinda ya tsayar danine a nan ne daddy zan shigo kwanan nan insha Allahu Daddy yace dashi a hasale zancen aure kafa akeyi nan da kwana biyu mai zuwa in Allah ya kaimu don haka idan kaga dama ka shigo idaman ba zaka shigo ba ruwan ka. Yace daddy ayi min hakkuri ina sane zan shigo insha Allahu kada ma ka shigo aure daine ba fashi a cikin zuwa jibin ya kashe wayan Abubakar din ya tsorata da fushin mahaifin nasa don baya fushi irin haka dasu har ya kashe mai waya idan suna sai gashi yau din ya kashe. Don haka ya yanke shawaran kiran abokan shi a lokacin ya fara sanar dasu halin da yake ciki don mutum daya ya kira yace afadawa sauran don shi ba tarun abokai yake dasu ba. Sai daren da aka fara sha,anin buki ne yazo da abokan shi da basufi uku ba suka diro garin a cikin dare a lokacin har hankalin hjy Addah ya fara tashi tana gudun dan ya aikata wani abin da zai bar masu abin fade ga mutane. WwYayin da hjy karima aakuma duk take sane da komai dake wakana wanda take ganin duk alhakintane dana diyanta Allah zai fitar masu a nan. Gida har ya fara cika da wasu yan uwan su da sukazo daga wasu auraren na daban a bagaren daddy ma shine tare da yan uwan shi dasuka tsure shi da korafi wai yaki hadin da suka so ayi a tsakanin yayan hjy Altine da Abubakar din. Ya biyewa hjy Addah ta hada da diyar dan uwanta taki nasu din yanzu ga yarinya ta shiga wani hali don ta kwallafa rai ga hadin su da Abubakar din a rayuwan ta. Daddy din yana zaune yana jin su kafin yayi murmushi ya kalli kannen nasa mata yana fadin kai kudai mata kuna da matsala. Yau kuma har muna da bambanci ashe a tsakanin mu da gidan babfa namadi ashe a wurin ku ? Yau ashe har kuna da bakin da zaku fadi hakan kuda bakin ku har kun manta da irin halalarci wanan tsohon a gare ku har zaku fadi hakan don kasa ya rufewa tsofin mu ido. Kallon juna sukayi kafin hajiya Asiya tace mu ba hakan muke nufi ba yaya kawai dai don ganin yadda in anyi da ita hamida zumuncin zai kara karfi a tsakanin mu ne kuma yanzu. Can din bazai kara ba ke nan ya fada cikin daure fuska kafin ya gyara zama yana dan dagowa saman kujeran tare da fadin. Ina sin ku saurareni da kyau kuji kada ku manta ba haka tsufin mu suka koyar damu ba kan zumunci. Har ma udan laifi shi Nuhu yayi aiba yar shi bane tayi laifin don kuma yar kuce yar Nuhu idan kun dauki hakan. Yaya yanzu dai ai zancen ya kare dama mun fada mane kasan abinda Addah tayi muna bata kyauta ba tunda tasan akwai soyayya a tsakanin yaran nan tun farko amma ta nuna muna sin kai ga hakan. To kuji nan wanan zancen shirmen ina son duk a barshi a nan kada inii wanan zancen ya fito idan da Allah ya nufi hamida ce matar modibbo. Babu fashi ita dince zata kasance matar ba wanan din ba don haka na kashe wanan zancen tun a wurin nan ya fada yana komawa saman kujeran. Dole ba fuska a wurin su suka bar falon yayan nasu rai bace don a yadda suka shirya sun so suba hjy Addah mamaki a wanan karon. Haka dai akai sha,anin bukin hjy Addah na tsaka mai wuya ita bata tsira ba a gurin yan uwanta dake ganin laifin ta kanta daurewa modibbo gidi yake kokarin kunyata su. A bangaren mijin ta kuma sun hade mata kai gaba dayan su taga canji a wurun su kan sha,anin bukin . Duk kan da namiji daya tilo da Allah ya bata ake mata wanan abun da take gani yanzu gun dangin nata. Anyi buki an watse lafiya kowani bangare sun nuna ba komai saidai na ciki na ciki a zuciyar kowan su a lokacin. Alhamdullahi taro ya watse lafiya an kai amarya dakin ta uwarta tanuna yar yar dangi ce ita don uwar tayi mata goma shatara bayan wanda mahaifinta yayi mata kuma. Kasancewan itace ya ta farko a wurin ta yasa ta nuna nata bajintan a dakin yar kowa nata sa albarka masu zagi kuma suna bi da zagi da gulma. Agege lagos yau can abin ya daukeni yakai na sari doya ina bin layi shiga biyu nayi sa,a kamar na kifar ganin rana yayi sanyi yasa na dauki kati da kudina ina bin masu motan dashi don nasan zan sayar ko da zuwa gobene idan na kara fitowa. Motace na hango lafiyayya a gabana sai walkiya takeyi na nufi wurin motan da sauri ina fadin buy credit buy rechage card . Aka zuge glass din motan a hankali maishi bai min magana ba sai ga wani dan mashin a baya yace rechage card na sheka