Sashe 269
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
baci zuwa wanan lokacin sun saduda da cewa lamarin a yanzu yafi karfin su. Wanan dawowan ya kara tayar da hankalin kowa a family din mu kowa da irin abinda yake fada yanzu kan zancen wasu suce aima har an sa ranan kashesu. Wasu kuma suna fadin cewa a a ai yanzune ma za,a fara sharia dasu don wani cargo na kayan zinare da suka dulmuye a tsakanin su na dan uwan nasu da suka kashe. Hakana dai wanan zancen yayi ta yawo a tsakanin ba wanda ke fadan daidai da abinda ya faru dasu don ko wanda suka tafi don ganin su Abujan ba zasuce ga halin da suke ciki ba. A bangarena kuma dai duk da naso na kyale zancen na kasa hakan ranan da faiza ta kira wayana tana kuka take fada min wai ashe su daddy ance rateyesu za ayi ? Naji wani iri a lokacin amma tausayinta yasa na daure nake fadin ba gaskiya bane hakan don ko mu ba a nememu ba har yanzu kan zancen don ko nasan ba za ai wani sharia da bamu wajen ba a lokacin. Koma meye nasan ba zasu rufe sati biyu a can tsare ba don haka ku kwantar da hankalin ku ku daina jin jitajita hakana. Abinda ya daure min kai shine yanzu sam bana jin alaman mutane kaina a tare dani kamar da can da nake yawan jin su ko suke taso min haka kawai kamar ila har na gama komai da zanyi zan kwanta. Sai nayi wani tunane kawai na mike na nufi wardrobe din kayana na dauko wani jakkana na koma saman gado dashi na shiga laluben abinda nake nema a lokacin. Har nayi sa, a na lalubo abinda nake nema na bude kwalban na dan shaka kadan kafin na rufe na mayar ai ban kaiga dawowa bakin gadona ba tun lokacin na fita cikin hayacina. A wanan daren jumma,an dai abubuwan kaina saida suka taka min saida kyat umma ta samu suka dan lafa min ba tare da wani hayaniya ba kuma. Washegari ma sai ummace ta kai min dan ruwan tea nasha da kyat na koma na kwanta ba,a dauki lokaci ba wayana ya dauki kara ummace ta dauka tana sallama. Wanan mutumin mukhatar usman ne a layin yana jin muryan umma ya shedata suka gaisa yake tambayan ta lafiya mu tace Alhamdullahi sai dai Sahiba din ce take fama da laluran ta na jinnu da kan dameta wani lokaci. Ya danyi shiru na dan lokaci kafin yace dama tana da wanan laluran ne ashe umma tace dashi tana dashi don yanzu sun kai shekara kusan goma data fara irin haka. Dama nima a nan nayi wani irin mafalkine da ita shine yasa na kiraku yanzu inji idan kuna lafiya don mafalkin ya ban tsoro sosai da sauki umma ta fada. Bayan dan shirun da yayi can kuma ya sake tambayan ko dai duk a kan case din nan ne don abinda mafalkin ya nuna min ke nan saboda mutanen nan shu,uman mutane ne sosai wallahi. Umma tace anya zasu iya cin galaba akanta kuwa sai dai abinda ya fito daga Allah amma nina san ba dai suyi mata wani abinda zai iya kamata ba dai da sunan sihiri. Amma hjy sai nake ganin kamar ba a banza take wasu abubuwa ba a yanzu Allah ya nufa umma tace don hjy da ya kirata da shi a lokacin. Da zasu iya wani abu da ita da ba a kai wanan lokacin ba kawai dai tana da nata dalilin ne a yanzu na ganin bai kamata duka a hukuntasu a kan laifin da bai shafi wasun su ba dai. Ok na fahinta yanzu a dan bani lokaci na kara dan bincke wanda ba a kama da wani laifi ba sosai a cikin su zan sakoshi insha Allahu nagode da kuma na sameki mukai maganan fahinta dake. Ba komai umma ta fada sai dai kunyi hakkuri da wanan yanayin na Sahiba don haka abubuwan suka mayar da ita yanzu sam bata da tsoro ko fargaban komai idan ta tashi magana. Murmushi ya sakeyi yana fadin ya fahinta kafin ya kashe wayan cike da fargaba da tunanen wani zance da suka tsaya mashi a rai cikin dan maganan da sukayi da umma din na dan lokaci.