← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 324 OF 337

Sashe 324

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

dasu sister lokaci lokaci wanan bai dameni ba tunda dama ba a gida daya muke zaune tare dasu ba. Hankalina kwance nake rayuwana a gidan muna waya dashi lokaci lokaci yana kirana har mu danyi hira dashi ko ya rambayeni idan ba wani damuwa a tare damu nan maidugurin. Har yakai wata daya da sati biyu lokacin yazo maiduguri koshi daga South Africa ya wuto zuwa Nigeria muna nan da yamma bayan magariba muka gashi ya shigo unexpected. Ina dakina lokacin na idar da sallah ke nan ina shafa mai don nayi wanka lokacin dana shiga yin alwala dama na fito na tsaya yin sallah. Ganin mutum kawai nayi a bayana tsaye yana rataye da suit din shi a kafadan shi sai farar riganshi yar ciki da hannunshi ke sama yana kokarin balle bottom din rigan daga sama a lokacin. Dan juyowa nayi gareshi ina kokarin kama dan tawul din da nake da daura gaba dashi lokacin ina fadin you're wellcome ansan man dake hannuna yayi a hankali ya mayar saman mirrow din. Zagayowa yayi zuwa gabana inda nake zaune kallon juna mukayi na dan lokaci na sada kaina kasa cikin nauyi da kunyarshi. Kokarin mikewa nayi sai naji ya rikeni lokaci guda na dan kara kalloshi zaiyi magana na rigashi ina fadin let me dress my self first. Sautin murmushin shi naji yana fadin ko kin manta cewa ni mijinki ne a yanzu haka nake son kallonki ya fada yana kokarin son mu hada ido dani dashi amma sai naki hakan. Sai yakai hannu kamar zai kama ma daurin tawul din na jikin nawa da sauri na mike zubur sai ya rikoni gaba daya zuwa jikinshi lokaci guda yana sauke wani irin ajiyan zuciya tare da fadin baby i miss you. Jikinane ya fara rawa lokaci guda ina kokarin janye jikina daga gareshi don a zatona irin wancan yanayin zai dawo min na ciwon mara da zuban jini shi nake gudun kada ya faru a yanzu din kuma dani. Saidai har muka gama tsayuwa mu a wurin ya sakeni banji wancan bakon yanayin nawa ba da nakeji idan mun dan hada jiki dashi saidai hawayen daya dinga fita min daga idanuwana kawai a lokacin. Wanda bansan dalilin zuwanshi ba a lokacin amma har yafita daga dakin hawaye bai daina zuba mi ba nasan bai kula da hakan bane a lokacin. Da kyar na samu na saka riga a jikina na koma nayi rub da ciki kwance gashi ina son tashi naje koda falone amma na kasa yin hakan a lokacin. Haka ya dawo ya sameni a cikin wani yanayi na daban da bai fahinta ba zaune yakai a kusa dani yana fadin na dauka akwai abinda zan samu indanci a yanzu. Jin nayi shiru banko motsa ba a lokacin a yadda nake kwance yasa ya dan dubani da kyau saiya fahinci ai barci ma nakeyi a lokacin. Dan bin dakin yayi da kallo bayan ya dago ko ina na dakin tsab yake kamar ba a amfani da dakin koba mutum a cikinshi dake rayuwa. Ajiya zuciya ya sauke kafin ya mike ya fita ya hado tea da kanshi ya dawo dakin ya sameni yarda yabarni a kwance har lokacin yasha tea dinshi ya fita ya dan jima ya dawo ya rufo kofa tare da bissimillah a bakinshi. Kafin ya jiyo ya dan tsaya tare da karato adduan tsari masu nauyi da tsayi yana tofawa a ko wani kusurwa na dakin nawa a hankali. Duk kunnuwanshi sunji mashi kamar anja tsuki da dankarfi ko a hasale baisa ya dauki wanan wani abu ba a zuciyar shi. Bissimillah ya kara tare da dan rage wutan dakin yana kaiwa zaune daga gefena tsukin ya kara ji anja da da karfin sauti tare da jin motsi kamar an taba handle din kofan dakin daya rufe din da da karfi da sauri ya dan kallo wurin saidai babu komai daya gani a wurin illa duhu a lokacin. Wayan shi ya dauko a aljihunshi ya bude page alkur,ani mai tsarki ya fara karantawa a hankali yayi nisa sosai a cikin karatun shi sai ji yayi nayi wani irin mika da nishi lokaci guda tare da juyawa a yadda nake kwance da farko.
Chapter 324 · 0% Book details