Sashe 115
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ta bai kwanta da hakan ba sai zargi yakuma shiga zuciyar ta duba ga yadda lokaci ya koma yanzu . Tun dai data tambayeni nace ni a wurin aiki kawai nake ganin shi bamu taba wani hurda dashi ba kona gaisuwa hakan yasa hankalin ta ya tashi kuma sosai da tafiya da motan da yayi din ni har ina mamakin hakan ga umma don ban zata itama ta sa motan a rai ba sai wanan lokacin ga nawa tunanen. Ganin ta damu har tana tambayana shi inda nasan shi nace umma idan ma har gudu yayi da motan ai kanshi yaiwa do dai duk inda yakaita sai ya dawo da ita nan da kanshi. Ina fadin haka na mayar da hankalina wurin kallon tv da nakeyi na fita zancen su itama umma din jin abindana fada yasa tayi shiru na dan lokaci karshe na mike zuwa dakina na kwanta na barsu a falon. Washe gari dana tashi naji saukin jikina sosai bayan na idar da sallah haka na fito na danyi aiyukan da nakeyi a gidan kafin muka shirya zuwa makaran ta. Bayan fitan muma umma bata zauna ba a gida don da zaran mun fita itama bata son ta zauna a cikin gida saita dawo shagon sayar da kayan sanyin mu ta zauna a nan. Saidai ranan haka ta zauna a cikkn damuwa dan ta saka ido har ta gaji ko zata ga Abdulhamid saidai har yamma da muka dawo babushi babu alaman shi. Hankalin umma ya kara tashi umma ta matsa sai naje ma,aikata na duba ko yazo inji dalilin rashin zuwan shi ban iya musa mata haka na shirya nabi hanya saidai banje can din ba. Na dawo na fada mata cewa bai shigo ba yau amma ta bari idan Allah ya kaimu gobe na sake dubashi. Umma tace ina ai mu tashi kawai muje can idan ba,a gane ba sai muyi karan shi kawai a station a nemeshi zafi. Ina jin haka nace tayi hakkuri har washe gari zan dawo school da wuri sai asan abinyi a kanshi haka dai ta hakkura ba dan taso ba. Washe gari ban dawo gida ba sai karfe hudu shima Amar sai uku da rabi ya iso gida mun samu umma a waje nan na zauna shagon wurinta muka gaisa. Na cire dan hijab din dake wuyana sai na zauna sai yar dogowan riga yellow daya tsaya min iya wuyan kafa muna hira ina bata labarin accident din daya faru a hanya. Umma ta matsu in gama bata labari ayi zancen daya dameta mota ya tsaya a kofan shagon ta da farko mun dauka masu tsayawa su sai kayan sanyi ne a wurin mu. Saida mai motan ya bude ya fitone mukaga ashe Abdulhamid din ne ina jin umma na sauke ajiyan zuciya har abin ya ban dan dariya. Yazon sun gaisa yake fadin umma tayi hakkurin rashin ganin shi a jiya wallahi matsala aka samu da Land lord nasu ya basu notis su tashi mai gida zai yi gyara na kuma bai basu notis din da wuri ba sai last week. Nan dai aka tausaya mashi tare dan magana kan hakan yace yazone a tafi gun mai maganin kada dare yayi in kuma sai zuwa gobe ne hakan baida matsala zasu iya bari aje gobe din. Umma tace ai ya dakata har hankalin shi ya kwanta zaifi tace ai ya bari harhankalin shi ya kwanta ya samu inda ya aje iyalin shi zaifi. Da hausa nake fadin umma mezai hana ya duba bangaren nan idan zai masa sai yazo ya gyara su shiga har ya samu inda suke so. Umma tace itama dai hakan ta gani idan wurin zai masa don zaman wurin haka ba kowa yana bata tsoro wani lokaci dakuna ukune da falo kitchen kamar yadda namu yake a sama. Dakin bakine sai aka debi garejin mota daga gefen shi shi baikai namu dake da daki hudu ba a sama. Umma tace dashi nace ba da wanan wurin zai maka ka duba ka gani sai ku dawo nan da iyalin naka har ka samu wanda kake so din idan kuma yayi ma shike nan ku zauna a ciki. Da sauri yake tambaya ina wurin umma ta nuna mashi ya juya tace bari ta dauko key a bude ya gani ya ma rasa me zai fada a lokacin. Ni ta tura na shiga na dauko mata key din ya bude ya shiga ya bude ko ina ya gani sai gashi ya fito yana wasan baki tare da fadin wuri yayi kyau sosai wallahi a nawa zasu dauka haya ke nan. Da sauri umma ta tare shi da fadin ba wanan ya kiyasata ya gani ai yasan yadda ya kamata sai ya fadi yayi shiru na dan lokaci kafin ya dago yana murmushi yace dadai za a fada mai zaifi don kada ya shiga hakkin mu da yawa ba zai so hakan ba. Shiru nayi ina sauraren su umma tace ai itace ya kiyasata yace to a raga mai ya bada dari biyu da hamshin a shekara idan bai tauye mu ba. Umma tace dashi kabada dari da hamsi a shekaran Allah ya kara rufa muna asiri ya shiga mata godiya ba adadi. A zuciyana nace ashe da tun tuni mun bada hayan wurin da mun dan samu mun rage ta wanan hanyar amma wurin yana kulle ba wanda aka bawa shi haya. Yayiwa umma godiya sosai tare da addu,a kamar wanda zaiyi kuka a lokacin don bai taba zato ko tsamani zai samu ko kwatankwacin hakan ba a wanan halin sai gashi Allah ya kawo mai daga sama a cikin sauki. Shiyasa kyautatawa yake da dadi koga wanda baka taba sani ba saboda baiga dai abinda yai muna ba har aka amince masa hakan. Washe gari tun kan in fita zuwa school sai gasu da iyalin shi sun shigo gyaran wajen nan na fita na barsu suna gyara. Ba abinda ya kara min dadi sai ganin su da yara maza nasan cewa Amar zai samu abokan wasa ke nan a yanzu yan uwan shi maza. Ai kafin mu dawo daga school har sun kwaso komai nasu sun tare a ciki sai gidan ya dan canza min kamar ba gidan mu ba ga haske ansaka a ko ina ya kara haske wajen. A gaskiya mutum dadi gareshi ko yayane don gashi mun fara ganin hakan tun yanzu nashiga gida umma ke fadin yau baki sun hanani bude shago sun tare aciki yau din nan. Nace umma naga an gyara wuri yayi kyau sosai wallahi Allah ya bamu hakkurin zama dasu tunda musulmai ne yan uwan mu su tace amin nima adduan dana gama ke nan a zuciyana. Wanan shine mafarin shigowan Abdulhamid a cikin rayuwan da ya shiga cikin labarin da zan baki nan gaba. Satin mu daya tare dasu gaskiya ba wani matsala a tsakanin mu duk da ba zama nakeyi ba sai da yamma idan na dawo yamman ma ina shago amma na kula da yadda takewa umma biyayya sosai sun dauketa kamar wata yarsu ko yar uwa duk da matan takan dan so zama muyi hira saidai ban saba da sakewa mutane haka ba. Ranan na takwas a gidan mu yazo da dare ya samu umma yana fada mata cewa mu fito muje don yayi magana da Alfa din yace yazo damu yau karfe takwasa. Ba yadda na iya haka umma tasani a gaba muka shiga motan shi zuwa wurin a hanya ne yake ba umma labarin cewa. Tun zuwan shi lagos yasan malamin sun zauna a unguwa daya dashi lokacin don shi dan lokoja ne ya shigo lagos wurun dan uwan shine daga baya kuma dan uwan nasa ya barshi ya koma cottono da zama. Har dai muka kai yana bamu labaein shi a takaice har matar nasa da suke yan gari guda da ita daya aura yaren su daya dashi sai dai ita iyayyen ta na nan cikin lagos zaune .