← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 337

Sashe 171

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har yakai gida yana mamakin hakan a cikin zuciyar shi bayan ya parker motar ne yaja tsuki yana fadin shirmen banza ya fito ya shiga gida. Falo ya samu Nazifa yau ba laifi tayi dan kwaliya da alama dai ta fitane ko tayi wasu baki mm a musanman a gida ya nasa a zuciyar shi. Gaidashi tayi yayi da yaran suka shiga murnan ganin shi daga nisa ya dan daga masu hannu ya shige dakin shi ya barsu a wurin uwarce ta bushi da kallon mamaki mutum haka da riko har ga diyan shi abinda ya faru ne ya fado mata a rai lokaci daya. Izuwa yanzu daya horasu din idan tayi tunane akan abinda ya jawo masu matsalan takan tuna da hudubar uwarta datace mata. Wai Nazifa kinsan darajan mahaifiya kuwa kinsan yadda wa yanda suka dauki iyayyen su da muhinmanci sukeji yayin daka taba masu ahali. Mutum ko dan banza ne akayiwa nasa wullakanci ya sani balle wanan da shawarashi da komai nasa yana a iyayyen shi. Kinyi kokarin nisanta diyanncikin shi da jinin shi shi kuma ya nuna maki ya barki da yaran ki kuje kuyi tayi dasu akwai abinda yafi wanan zafi a wurin mace ace yau uban yaya ya yafe maka yayanka aiko da wasa ya furta maki hakan idan kina da wayau dole ki damu. Tunda nayi sallah ina dakina ina nazarin wanan files din haka ya hanani fitowa don aikin da nakeyi a falo din sai sallah kawai yake tayar dani lokacin. Ummace ta leko dakin tana fadin yau wani irin aiki kikeyi hakane ya dauke maki hankali kai na dago bayan na zana arrow kamar yadda nake saka sheda a wuri idan naga tambaya. Ina murmushi nace umma da alama aikin mu yazo da sauki don wa yan nan files din da kike gani a gabana ya kumshi duk wani bayanin da muke nema. Saidai nayi mamakin ganun haka saboda wasu fliles din da suka boye suna zaton wa yan nan ne a wurin sauri ikon Allah gagara musali ta fada . Kafin ta nisa tace baida alhakin sune shiya sosu da alheri sun nuna masa halin yan Adam yanzu gashi abinda basu zata ba yana shirin faruwa dasu kuma. Bawa akwaishi da matuwa sosai akan dukiya sai ya shagala ya manta da komai balle dukiyan daba nakaba yau ina laifin wanda ya jawoka cin arziki a karkashin shi ? Nisawa nayi ina dagowa tare da aje takardin a gefen wurin sallah na nasan don ban fito naci abinci bane yakai har umma ta biyoni dakina dan tun zuwan mu bata leka dakin da nake zaune a cikin sa ba sai ranan. Tare muka fito zuwa falon nako samu an jera abinci saman dan karamin dining table din dake aje a gefen falon Amar yana kwance yana kwashe rubutu a littafi shi yana jin motsin mu yake gaidani na amsa na zauna umma ta zauna a gefena. Muka fara cin abinci cibi uku nayi na wani irin zabura na mike tsaye da sauri kamar an tsikareni lafiya umma ta tambaya banyi magana ba nasa kai na fita daga falon kai tsaye na nufi hanyar get din shigowa haraban gidajen namu. Ganin haka hankalin umma ya tashi sosai Abudulhamid ta kira hankali tashe tana fada mashi ya fito daga shi sai dan gajeren wandon daya saka a jikin shi na zaman gida. Ina kaiwa kofan na tsaya na dan lokaci kafin na duka na dauki duwatsu kwara uku nayi addu,a na jefa a ta wajen get din duk kusurwan wurin hudu nayi haka na juyo na dawo part din mu duk su umma da Adnan da Abdul suna bina a baya. Daidai tsakiyan gidajen naja na tsaya na dade a wurin ina dan waige waige kafin nayi tako biyu na tsugunna a wurin na dade kamar ina ginan wani abu kafin na mayar da kasan na rufe. Tare muka koma ciki dasu a lokacin ina shiga falon na fada kan kujera basu ankara ba sai ji sukayi ina barci cikin abinda baifi mintuna biyar ba da shigowan mu. Abdul ne ya kallesu yana fadin nasan ba ita bace dama akwai matsalan da suka hango sukai wanan abin haka duk yadda akayi. Ke nan dai tana da sprit a kanta masu karfi Adnan ya tambaya kwarai kuwa ya bashi amsa sun dade a wajen gidan mu suna magana kafin suyi sallama da umma su shige gidajen su don dai suna mazane amma sun dan firgita don basu san meya kawo hakan ba. Washe gari jumma,a ban iya fita da wuri ba don sun dauka ma bazan fito ba a ranan sun fada da aka tambayeni cewa banjin dadin jikinane. Abin yai masu dadi sosai da sauri Inusa ya nufi office din manager ya samu malam bala a ciki ana faman kulawa yake fada masu abinda yaji a bakin abokan tafiyana. Suke fadin mu din dama na wasane an fada mata mu yan iskane da zatayi wa kutse kudi daine munci ba yadda za ayi damu fakat yana wani bude hannayen shi biyu yake magana a cikin isa da izza. Zubur na mike ganin lokacin a gurguje na fada ban daki nayi wanka na dauro alwala na fito na tayar da sallah. Shiryawa nayi cikin bakar abaya nagyara tsab zaka dauka balarabiyace ni din na fito na dauki files dina da laptop na shiga motan sai ganina kawai sukayi na shigo wanda yakai gulman banda lafiya ranan shiya kawo masu tsegumin zuwana kuma. Kallon juna sukayi da mamaki kafin suce ga yar iska shu,uma kada fa yarinyar nan taso juyamuna hankali fa. Ban zauna ba sai yawatawan da muka kama dasu Adnan bayan inda ya rifto muna jiya na nufa tare dasu ba abinda ya faru da saman rufin din wurin to amma ya akayi cikin ya rusa Adnan ya tambaya. Wurin na dan kurawa ido na dan lokaci na sauke ajiyan zuciya muka koma ciki bayani na fara yi masu kan abinda nayi nazari kowa ya duba abin yadda ya dace sauran zancen zami barshi sai monday mu karasa nace dasu. Da biyu nayi hakan don nasan zasuji wanan zaman namu na ranan don haka nake son hanin kullin da zasuyi muna kuma nan gaba. Motana na nufa don tafiya gida saidai tun kan na kaso inda take in shiga naji gabana yayi wani irin faduwa sosai addua nayi na sa kai na shiga don zuciyana ta ban na shiga kawai . Hakana tuka zuwa gida ba abinda ya sameni saidai ina fita ban jima ba ake fadin akawo agaji motar na fitar da hayaki a cikin ta. Aka dai samu aka tsayar da taimakon mazan site din namu abin yabawa kowa mamaki Amar yabi Abdul da Adnan tare da iyalin shi zuwa sallah jumma, a sai ya rage dagani sai umma a gidan ban yarda na kwanta ba don kada sallah ya wuceni. An sako jumma,a ke nan ya fito ya shiga mota ya dauki waya kira layin umma muna zaune kiran ya shi ya shigo a wayan umma nike kusa don umma na sallah na dauka don ganin shine mai kira. Haka kawai naji yanzu ya kamata na daina nuna mai komai tunda yace ba laifin shi bane hakan don shima baiso haka din ba da aka kyalemu din. Sallamu Alaikum na fada ya amsa min tare da fasin so you are at home Sahiba nace eh yaya good afternoon ya amsa da afternoon. Ya kuke ya mama nace lafiya tana sallah ne yace ok kuna dai lafiya ko kwana biyu ban zo na duba kuba aiki yayi min yawa a nan ina kaduna. Ayyah yasu Faiza dasu Amira na tambaye shi yace lafiya suke suna tambayan ki sosai da alama shima yaji dadin yadda na sake ranan muna magana dashi din. Idan mama ta idar zan kira ki gaida Ammar ya fada yana kokarin kashe wayan dake hannun shi din ina fadin umma ta idar amma ya kashe wayan baiji ba. Umma na idar da sallah take fadin Abubakar ne ko na gyada kai tace ya kirani jiya yana fadin akwai tambayan da yakeson yayi min bansan ko na menene ba dai don bai fada ba tukun. Mwku yake son tambayan ki kuma na fada shigowan Amar yasa muka bar wanan zancen da mukeyi din yana bamu labarin wai yaga hanyar da muke zuwa school da muna gidan daddy zaune. Ni dai kallon shi nayi umma ko cewa tayi dashi haba Amar koni bazance ga hanyar da zamubi zuwa gidan daddy daga nan ba don gaba daya garin nan ya juye min ban san a wani barin muke ba. Dariya abin ya ban nace bamu da wani nisa sosai dasu a nan don muna New GRA ne nan kinga ba nisa sosai dasu ba daga nan. Wayan tane ya sake daukan kara ya kira ko ta fada ina mika mata wayan dake hannun nawa ta karba bayan tayi receive. Sun gaisa yake fadin ko kin san filaye nawa Uncle ya bari a duniya kafin ya rasu mama don naga kamar ba wanan case din a cikin case din shi yadda wani makwabcin shi yaba da shedu shekarun da suka wuce. Shiru umma ta danyi kafin tace ba zance na sani ba gaskiya amma dan littafin da yake rubuta komai na samu daman daukan shi yana wurina kafin na bargida . Wata kila zaka iya ganin komai a cikin sa da kake so yanzu ban baku bane a baya don ganin zancem bai tashi ba lokaci. Da kyau mama haka yayi yana nan a hannin ki yanzu haka ko tace yana wurina yanzu haka bana yarda nayi nida dashi ko kadan ai. Zan shigo lagos wani sati zanzo har gida na karba in duba don Allah a ajeshi da kyau don nasan akwai bayanan da zan iya samu a cikin sa. Basu gama wayan ba layi ya katse lokaci guda kallon umma din nayi ina fadin bana son su san cewa muna garin nan umma. Dama saida nayi wanan tunanen hakan zaizo bai samemu a nan din ba kawai a kyaleshi mana idan har ya samu zuwa din bai samemu ba zaiyi zaton mun tafi wani wurine don ba zai taba zaton muna garin nan ba ai saboda Abdul dai yayiwa kanin
Chapter 171 · 0% Book details