Sashe 219
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
mommy dama ai sun sani suka yarda baki nawa ya fada masu cewa baida hali amma saboda kudin da yake basu ya rufe masu ido har da cewa anty tayi ana masu bakin ciki da hassadane da nakin ciki don anga yarta tayi saurin samun miji. Indai yan gidan uncle ban hana wanan Isma,il din nan ba shine mai dama nidai ga yaran gidan nake gani jinan mommy ta fada duk suka dago suna kallon ta . Bana son jin irin wanan maganan a bakin ku da baby din da shi Sufynu din duk yan uwan kune don haka kowa matsalan shi ya shafe ku ku kama bakin ko kuyi masu addua. Shiru sukayi wanan yasa tun farko basu son mommy din taji zancen a bakin su hauwa kuma ta fada mata yanzu don haka basu so ta fada mata ba. Yaushe ne hakan ya faru mommy ta sake tambaya hauwa ta kalli Faiza tace ga wace ke fada muna yanzu mu. Faiza ta bata rai tace nima Fatimace ai ta fada min tace wai mommy ta kora su waje don baby tazo mijinta ya duketa sai take ban labari. Shiru mommy tayi bata kara magana ba bayan Allah kyauta data fada ta dauki remote din tv tana canza chenal Faiza ta mike zuwa daki. Falon cike yake da ire iren su ana hayaniya daddy yayi sallama ya shigo suka amsa banda Alh Nuhu daya kawar da kanshi gefe tun shigowan daddy din falon. Gaisawa ya fara yi da mutanen daya sama a wurin suma suna amsawa a cikin girmamawa mutuntashi don girmanshi da irin darajan shi. Har kasa ya duka a gaban shi yana bashi girman shi na matsayin shi babban yaya a garesu a family su. Hakan ya kara fasa kan Alh nuhun dole ya juyo yana amsawa babban mutum kamar daddy ya bashi girma haka a gaban kowa aishi babu kamarshi ya sani. Yaya ina can ina jin yadda abubuwa suka dinga gudana yace a cikin basarwa eh abune mai kama da an shirya shi dama saidai ai zai koma kan duk wanda ya shirya haka don baisan Nuhu ba dakyau yasa aka kulla hakan don kawai a tozartani a idon jama,a. Shi abu idan yazo a daina sa zargi a cikin shi don duk nan mun sanda haka na iya faruwa da kowa a kan harkan shi ba komaine muke samu yazo muna daidai ba yadda muka tsara. Kwarai kuwa wanan haka yake Alh Bello ya fada daga inda yake zaune yaci gaba da fadin kai kasan idan ba kaddara ba har yaushe wanan yarinyar me kama da yar tsana zata zo tayi nasara haka a kan mu lokaci daya. Kada kai mamaki Alh bello ina fada ma wanan abin kamar wani shiri ne akai muna akan hakan don kawai aga mun tozarta a idon jama, a. Ban dauka yadda kake tunane bane Alh hakan dai kamar wani al,amari ke shirin faruwa haka na dauki zancen idan kayi zurfin tunane . Me kake nufi da hakan daga fada Alh Nuhu ya tambayi Alh Bellon abokin shi yana mai tsure shi da idanuwan shi. Eh ko ka manta da kowa nan abinda kake tunane ya shafeshi sallaman wasu abokan sune ya dakatar da faaa kwan da Alh bello ya tashi yi a lokacin. Mikewa daddy yayi yana masu sallama da niyar tafiya yana furta Allah ya tsare shi zai koma idan ba damuwa zamu iya ganin juna karfe hudu a gidan gonana Alh nuhu ya fada. Ba damuwa Allah ya kaimu lokaci lafiya ya fada ba tare da damuwa da komai ba ko darrr yadda wasu keji idan ya furta hakan. Daga inda muke tsaye muna hangosu kan shi a duke Ganiyat nayi mai magana kanshi yana a duke can ya dago ya tura wayan shi cikin aljihun shi. Kai tsaye ya taka zuwa inda Alaja suke zaune da mutanen ta yai magana dasu na dan second ya juya yayiwa Jimoh alama da hannu jimoh ya taso da sauri ya sameshi. Mun hango dai jimoh na kada kai kafin ya juya zuwa wurin yan uwan tafiyan mu yai masu magana shi kuma ya nufo inda muke tsaye din kai tsaye. A nan ya same mu mu tafi yace damu kawai yai gaba muka bishi a baya zuwa wurin da aka tanadar muna motocin da muke amfani dasu kasan. Kai tsaye wurareb tarihi muka nufa ranan munsha yawo shikan sai aiyu kan shi yake a cikin computer din shi dake lake dashi Jiddadun Alaina. Mun dawo masaukin mu a gajiye sai shirin tafiya kamar yadda ya fada muna zamuyi gaba a ranan su alaja zasu biyo mu baya idan Aishat Ganiyat ta karbi kayan ta daga makaranta. Karfe goman dare na ranan muka daga zuwa Dubai muka sauka da safe ana a can ma mun samu masu taron mu kamar yadda aka shirya. Masauki maikyau ga nagarta da jin dadin rayuwa nikan tun bayan sallah dana kwanta barcina nayi sosai sai uku na rana na falka koshi don sallah dana tuna yana kaina banyi ba. Na idar na zauna ina addua tare da jan lokaci don la,asar daya gabato a lokacin saidai kafin lokacin cikina ya fara kiran ciroma . Gaskiya a wanan tafiyan mun sheda cewa Oga Sha,aaban ya nuna jin dadin shi ga aiki mu kamar yadda ya fada din don a gaskiya mun ga gari gari ya gan mu. Shin shi mai hali Allah kan ga zuciyar shi yai mashi zarafi duk da ba duka masu halin Allah yaiwa halin kwarai haka ba akwai irin su baffana Nuhu da suka riki arziki abokin tafiya lahira a garesu. Wani kuma mai kudin Allah kan bashi basira da zai gane cewa yiwa wasu shine abinda zai tsira ya samu daga cikin arzikin shi a gobe kiyama. Samun irin su kalilan masu kafin basira da tunane a wanan zamanin zakaga wani a cikin daula kamar ba gobe gare shi wanan yasa ya shagala imanin shi baya kaishi tuna halin da rayuwan wasu suke aciki. Amma saidai cikin dubu akan samu goma da zukatan su fal yake a wurin taimako taimakon da zai zama silar dagawa wani dagawan wani da shi kuma fiye da mutum dubu zasu karu a dalilin shi nan gaba duk ta dalilin mutum daya ubangiji Allah ya karawa mai arzikin taimakon tallaka arziki na duniya da kiyama Allahuma amin. Nayi wanan bayanin ganin yadda ogan mu ya tallafawa rayuwa cikin rayuwa da yayi sanadin dagawan wasu da dama a dalilin shi bawa ya tuna idan har Allah ya bashi ikon aikata hakan wani irin lada zai tara a wurin Allah wanda ya samu a sanadin tallafawa rayuwan mutum daya rayuwa itama ta ceci rayuwan dubu nan gaba ?