Sashe 153
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba sai Ammar ne yace mai bamu kudi din nan mana handsome din nan. Dan gwagon ku hari umma ta fada a daidai lokacin da aka turo kofan falon namu bayan anyi knocking za a shigo. Duk muka juya don ganin maishi yaya Abubakar ne ya shigo da sallaman shi falon muka karba mai ya shigo. Mun gaisa dashi ya amsa tare da kallon mu ya samu wuri ya zauna umma tana tambayan shi mutanen gida . Yace suna lafiya a ranan ma ai ya baro kaduna yazo lagos din aiki sai umma ke fadin intashi in kawo mai abinci da abinsha a dauko a shago. Haka na mike zuwa dauko na dauki key din shagon don zuwa na dauko mai drinks din yana fadin a barshi umma tace haba kamar bako dai dakai modibbo. Ko baka iya cin abincin mune kada a kawo maka da sauri yace No ba haka bane mama a koshe nake dama kafin nazo nan din. Ni dai ban tsaya sauraren su ba na nufi hanyar sauka daga benen sai Ammar ya biyoni a baya muka fita tare dashi. A can yake ba labarin zuwan mustapha da baiko tsaya don ya samu akwai custermers a wurin ta sunzo daukan kaya lokacin ya aje muna abinda yazo dashi ya wuce. Koda muka fito ya tsaya ya rufe sai a lokacin na kula da motar da aka sake ajewa kofan gidan munga mota a kofan gidan bamu dauka gidan mu maishi yazo ba don akan aje motoci a haraban namu wani lokaci don muna da filin parking sosai a wurin.. Muka shigo saida naja na tsaya don ganin su, su biyun duka a lokacin daya gidan namu kamar sun hada bakin zuwa a lokacin. Wani irin matsanancin faduwan gabace ya ziyarceni lokaci daya don ganin su a tare da nayi a falon namu suna gaisawa da umma. Tunda yayi sallama ya shigo suka gaisa da junan su kowan su ya mayar da hankalin shi kan wayan shi yana dakila. A sanyayye na bude baki ina gaidashi kafi yada kan shi ya amsa muna na aje drinks din a gaban ya Abubakar kafin shima na aje mai daya a gaban shi. Na juya na shiga kitchen na dauko plate na zuba miya na kawowa kowan su plate din na aje gaban su. Na juya na saka ledan sakwara bibiyu a cikin plate nakai gaban su na aje agaban kowan su sai shi mustapha din nema ya dago kai a hankali yake fadin thanks. Na daga ba tare da yin magana ba ruwa na koma na dauko masu har na wanke hannu ina ajewa na nufi hanyar dakina naji muryan umma na fadin . Ina zaki ga abincin kunaci da kanin ki zaki tafi kuma na juyo a hankali cikin harshen yarbancin ina fadin na koshi kuma bazan iya kara ci ba yanzu. Yayyun na ki fa da sukazo zaki shiga ki barsu a zaune ta kara fada naji wani iri ina fadi a raina wayyyoni Allah na umma zata kwafsa min a nan kuma. Da ace umma tasan yadda nakeji lokacin a raina da batayi min wanan maganan ba lokaci. Yanzun dai komai ta famjama famjan inji yan iya magana bani da masaniya akan zuwan su a lokacin banda kuma dalilin shin . Don haka zaman da banaso a wurin suna zaune ban kuma da dabaran da zanyi in shige ciki a yanzu don dole inbi umurnin umma din. Haka yasa na dan dago kai na saci kallon inda suke naga mustapha shi dan duniyan har ya fara cin abincin dana aje masu din a gaban su yana ci a cikin sukuni da kwanciyan hankali ba wani damuwa a tare dashi lokacin. Sabanin yaya Abubakar dako kallon abincin ma baiyi ba yana fama da wayan shi kodan yafi mustapha din zama bafulacen kidi ne oho. Bani da zabi a lokacin illa kawai in dawo in zauna a tare dasu duk da yadda nake jin feeling some,how a gaban su din a yanzu. Kodan saboda na girmane yanzu na fara sanin kaina ko kuma dai kawai don bana son wani halaka da yan zuri,ansu baki dayane a yanzu ban sani ba. Yadda ya sake jikin shi yana ci abincin shi sosai hankali kwance suna dan hira da Ammar dake gefen shi zaune da gani kasan sun dan saba da yaron shima sosai. Amma ya Abubakar uffan baice dasu ba yana ta faman dakilan wayan hannun shi kawai karshe ma wayan shi tayi ringing ya dauki kiran yana jin maishi. Kai sai a ranan na kara sanin shi din miskiline na karshen karshe don ba zakace shi din ya taba sanin Almustapha din wani wuri ba ko suna da alaka ta jini da junan su bah. Umma na a takure take zaune cikin su lokacin kawai dai ba yadda ta iyane ta zauna amma zuciyar cike yake fam da zargin su a lokacin. Saida ya gama wayan shine yana sakawa a aljihu a daidai lokacin shi mustaha din ya mike yana cewa umma shi zai tafi jiya ya zo lagos shine yace bari yazo ya gaida mu. Godiya sosai umma take mai tana saka mai albarka kan irin yadda suke kullamu suna zumuncin lekomu lokaci lokaci. Duk abin nan da sukeyi ko ya dago kai yaiwa dan uwan nashi magana asalima ko sashen da yake ya Abubakar bai kalla ba lokacin, duk da yana jin shi yana sallaman da umma din ko dagowa baiyi ba har ya fita. Nikan hakan sai ya ban mamaki sosai da tsaro tunda nasan yadda iyayyen su suke da zumuncin su ganin haka saina kara shan jini da zurian tasu ga baki daya. Yana zaune a inda ya barshi sun fita da Amar sai ga Amar din ya dawo yana fadin ya wuce sister wai mu shirya gobe zai zo ya kaimu beach. Umma ya akayi wanan ke zuwa maku gida haka har kuka yarda dashi baku san koshi waye bane halan har ku sake dashi haka ? A, a modibbo baka gaje dan uwan naka bane halan don nima mamaki nakeyi tun shigowan shi yadda kuka nunawa junan ku baku san juna ba. Saida ya dan murmusa ya dago kai yana fadin nasan shi mana mustapha dan gwaggo hari sister din daddy ko ? Wanan ba mutumin arziki bane kada wata rana ya jefaku a fitina azo ana maku buncike a gida kan laifin da baku aikata ba. Umma tayi wani iri da sauri ta kalli moddibo din a cikin mamaki tana fadin cikin sanyin murya Shidin ai yana zuwa nan ne saboda alakan iyayyen ku modibbo duk da ba sanin dawwan mu gidan nan mukai mashi ba da farko . Amma yanzu din da ya ganmu tare da mahaifinka zuwan mu kaduna shine karfin zuwan shi lokaci lokaci can ba a rasa ba yakan dan leko mu a gaisa. Kada ku yarda dashi Umma don Almustapha ba mutumin kirki bane dan smogal din haramtattun kayan da gwaunati ta hana a shigo dasu cikin kasan nan ne. Da sauri muka dago da wani irin kallon juna nan da umma lokaci guda yau ko ba komai munsan dalilin da yasa ake neman shi wanan can lokacin daya fake a gidan da muke haya. Yanzun don mutum na smagal ya zama abin kyama ga kowa ke nan umma ta tambaya cikin mamaki tana kallon modibbo din dake bayani Yace kwarai kuwa umma don yana cikin jerin mutanen da gwaunati ke hari sosai idan dubun shi ya cika zai rainawa kanshi ranan sosai saidai yana ganin shi mai wayau ne ba za a iya gane shi ba yake gani. Don haka ku nisanci hurda dashi don ni sam ban yarda dashi ba ko kadan da zuwa nan din da yake maku don sam bansan yaddama ya gane wai kuna nan ba har ya biyoku ya fada yana min wani irin kallon tuhuma. Banda alakan komai dashi banda na gaisu a tsakanin ga umma nan ka tambaye ta kaji asalima shida kanshi yayi warning din kan nuna na taba sanin shi a baya idan zaka tuna ranan dinner diyar gwaggo Asiya da mukaje tun wanan lokacin na rike wanan kalaman daya furta min gaisuwan ma sai da umma ta matsa min nake gaida shi idan mun hadu. Yace kun gani ba idan ya yarda da kanshi ai ba ai ba zai fadi hakan ba gareki muna fukin kasa don suna yaudara saboda suyi kudi sufi kowa suke wanan harkan mai hatsari a garesu nina san mustapha don kusan tare muka taso a zurian mu dashi nasan halinsa sarai da kasada. Ka yarda dashi don shi din ba wanda kuke zargi bane na tsunci kaina da fadi haka lokaci guda ina kallon yaya modibbo din da shima ni yake kallo da mamaki. Yayi min wani irin kallo nace kwarai kuwa yaya babu ruwana dashi bayan gaisuwa tun baisan mu suwaye a gareshi ba kuma har yanzu din ma bai sani ba don nasan kan abinda yake zuwa gidan nan ke nan a yanzu ya binciko alakan mu da daddy ku kuma ko hakan bawai ya dameshi sai ya sani bane. Yana dai zuwa nan ne kawai don nasu yazo daya da amar ya mustapha shi kanshi kuma ai baisan yaudaran shi sukeyi ba suna surka sana,arsu da miyagun abubuwa a cikin kayan su da sukai odan zasu shigo dashi kasan nan. Don haka suke amfani dashi don ya iya harkan suka lababa shi suna amfani dashi wuri saka kaya ya shigo masu dashi a cikin rashin sani. Sai dai amma yanzu din ai yasan komai don shi kanshi kyamar abokan harkallan nasa yakeyi sosai a yanzu suma din suna farautan shine kamar yadda suka san yana nasu. Kallona ya tsaya yana yi a cikin mamaki na mike nace kwarai idan baka yarda ba ka bincika kaji zaka gane gaskiya insha Allah duk dani banda wani business dashi kamar yadda kake zato. Abin harin ka yana cikin gidan yanzu haka hanya dayane duk asirin da ta dauko maka yana a cikin dakinta a kasan wardrobe din kayan ta cikin farin leda da zaka samu dama ka dauke zaku zauna lafiya duk da shirmen na mahaifiyar tane ba nata bane daga haka na wuce na barshi zaune da mamaki yana bina