← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 240 OF 337

Sashe 240

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

muna wayan ka ba tunda ba sharian ka mukeyi yanzu ba ai zaka iya tafiya ka zauna yace ya gode ya juya zai tafi sai mai karemu yace dakata ko zan iya samun record din inji don zai min amfani nan gaba kadan idan abinda nake nema yazo daidai. Ya shiga laluban wayan shi yace gashi ka dan kuna muna nan kuma gardama ya kaure a tsakanin su lokaci guda har wasu daga can yan bayan fage na fadin ai aji irin furcin shi shiyafi. Aka kawo wani na,uran kara sauti aka hada muryan shi tarara yanawa hamza din kashedi kafin barister din ya shiga tafa hanayen shi yana godiya ya mikawa baffa wayan shi. Alkali ya bada lokacin hutu ya mike nan kowa ya samu daman mayar da zance ga nakusa dashi shima mai karesu din ya mike suka dan fita daga gefe a tare dasu. A can kuma dakin hutu alkaline a zaune ya kwabe hular kanshi suna maganan siri da babban yaron shi kan wanan case din yaron yana fadawa alkali abinda ya gano a cikin case din. Duk yadda akayi yarinyar tanada wani mai fada aji a kasan nan a yadda na fahinta gara kawai muyi abinda zai kara muna daraja da daukaka a indon mutane zaifi in yaso shi sai a mayar mashi da kudin shi. Wayan alkalin ne yayi kara ya dauka yaji mai magana na fadin shin kasan sharian da kakeyi kuwa a yanzu ya fara yawo a kafafen labarai na kasan nan don haka ka gagauta yin abinda ya dace kada kasa son kai a cikin zancen nan. Wani abokin aikin shine na wani jaha ya kirashi yana gargadin shi yace wai na tambaye ka man ita wanan yarinyar a karkashin wa take aiki a yanzu ? Yace da gani dai yarinyar tana da daurin gindi sosai a wurin wani kusa a yanzu dai na kasa gano gaskiyan zancen ina dai kan binciken hakan. Koda Alkali ya dawo lauyan su baffane yayi magana shima yana son ya samo hujjah don zargin da akewa wanda yake karewa din. Aka daga karan sai karshen daya ga sabon wata mai zuwa za a kara zama lokacin sun gama fahintar inda zancen yake kafin nan su yanke hukunci. Saida aka fito ne muka samu gaisawa da wa yanda sukazo wurin mu daga cikin yan uwa muka gaisa dasu suke muna fatan alheri akan Allah ya tona asirin maishi ko waye . Mukayi sallama dasu a rana muka juyo zuwa lagos saidai ba kamar ranan ba don yanzu mun fara samun hujja mai karfi daga yan uwa. Da daga farko suke tsoro da shayin bada sheda don kada a halakasu da tsafi ko wani abu nadaga cikin sherin Alh nuhun da suka shede shi dashi din. Ni sai bayan mun dawone ma na tuna da envelop din da Felix ya kawo min washe gari ina kwance na mika hannu na dauka. Katin fatan alheri ne maikyau dashi sai kalaman fatan samun nasara da akewa mutum a cikin katin da kallo shi kawai zaisa ka gane yana da tsada sosai. Dan murmushi na sake a fuskana a karo na farko tun dawowan mu lagos din mikewa nayi na dauko wani takarda ina dubawa ni dai Allah ya gani a yanzu kaf yan uwan mu inka debe mutu hudu zuwa biyar har dana sanin fitowa a cikin su nakeyi. Mutum biyar din kuwa sune ya Abubakar wanda Allah ya jefoshi a cikin rayuwan mu da alheri domin ya tallafa muna sai baffa hamza sai kuma gwaggo hari da danta sai baffa Abdulahi da shima yake nuna muna kulawa sosai a zaman kotun. A can kaduna kuma yau gidan nasa makil yake da yaran shi da wasu yan uwa da abokan arziki dake ganin kazafi akai masu don kawai a bata masu suna a gari. Falon na cike da mata wata mai zakin murya a cikin matan dake falon take fadin kai wanan zamanin dame yayi kama haka ? Wai ace yar dan uwanka daya mutu ya bari itace wai zatayi karan ka ta zauna kotu dakai tana sharia don lalacewan zumuncin zamani. Yo keko dai akan kudi maye mutum ba zai iya yi a yanzu ba hjy hafsa wata karba daga gefen ta ni sai na dauka kamar hadin bakine don kawai anga suna samu bari a tsiyata mutum a huta a koma daidai. Wanan yar ai ta bushe fitilan tako don ance ma ko shigarta kawai kagani kasan ta rika ta kuna bata taran kauri don idanuwan ta a bude suke. To aini yadda naji ance tare da manyan kasa take kinga kuwa dole ta dauka zata iya can wata daga cikin yan uwa ta amsa su da fadin . Ni har taysayi take ban bata san waye Alh bane ta kawo kanta Alh ai ba, ayi mashi wanan haukan yama kyaleta dai don tana yarinya ne karama kila ? Nan dai suke ta shaci fadi dinsu har suka gaji sukai sallama suka tafi ba don sun gaji da gulma daga gefe wata yar gidan ta kalli nazifa tana fadin niko wanan shigan da za ayi har kotun zanje naga wanan yar iskan yarinyat dai a idona. Baki nazifa ta tabe tana fadin kiga haushi dai kan din ance wallahi karamar yarinyace sa,an su manir kinga kuwa ai karamace sosai wuri ta samu kawai tana iya shegen ta kawai indai Abbane ai kar yake kallon ta. Toshi mijin kiku fa da akace shi yazo da ita daga lagos din ya nuna mata gida fa tace wanan dan iskan ranan naji mahaifiyan shi na masa fada yace shi ina ruwan shi cikin wanan case din tunda bai shafeshi ba. Ai baima zuwa kotun ina gani don ko wanan zaman ma yana Abuja aka zauna bai gari ai shiyasa na kyaleshi. Da zai tafi na bugi cikin shi ina fadin gobene fa zaman su Abba kotu yace dani ina ruwan shi da zaman su shi wanan zancen ba nasa bane don haka zaije yayi mai fiddashine. Shi zancen biyan wanan kudin company din yanzu ke gaban shi suga inda kudi zai fito a biya su kudin shine a gaban shi. Kai gaskiya Abba yana da makiya wallahi ki duba fa Nazifa idan haka ba shiri bane ina Abba ya taba fadawa hannu irin wanan gashi lokaci daya . Allah ya fisu ai kome kuwa zasuyi ba zasu taba cin nasara ga Abba ni shiyasa abin baya damunama sam wallahi don a shirme nake daukan zancen. Wai ace anyi karan Abba haba kai jama,a da kuma laifin yin kissan dan uwansbi fa ? Nifa har yanzu zuciyana ya kasa tsayi wuri daya wallahi tun maganan da mama tai muna ranan nake jin kamar wani abu zai farune dasu Abba din . Don fa yarinyar nan ta shirya sosai wallahi ga ta ba tsoro ko shayin kowa haka zata tsaya tana fuskantar kowa a cikin kotun. Ni yanzu so nake kawai naga an kare wanan sharian wallahi saina fadawa baffa hamza magana daga yau alakan namu ta jini ta bare ai yaga yadda nayi mashi dazun da muka hadu dashi wani kanin su ke wanam zancen a cikin takai . Wai tace a bata dukiyan mahaifin nata kuma abi mata hakkin halaka mata uba dasu Abba sukayi idan ba tsoro ba uwar nata tazo ta tunkari su abba mana idan bataji tonon asiri ba a wajen su. Saida suka kare barikancin su sanan yanzu suzowa mutane da wani zancen bamza cN
Chapter 240 · 0% Book details